Bai kamata a riƙa yi wa ‘yan fim kallon karuwai ba – Hafsat Ammi

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano 

Jaruma Hafsat Hassan, wacce aka fi sani da Ammi, sabuwar jaruma ce da ta fara taka rawarta a masana’antar shirin finafinan Hausa ta Kannywwod. Duk da cewar ba ta daɗe da shigowa ba, amma dai a yanzu ta fara zama fitacciyar jaruma, musamman a waƙoƙin da suke fitowa a wannan lokacin. Don haka Wakilin Blueprint Manhaja, Mukhtar Yakubu, ya tattauna da ita, don jin yadda ta samu kanta a cikin harkar ta fim. Sai ku biyo mu ku ji yadda ta kasance:

MANHAJA: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.
HAFSAT AMMI: To, ni dai suna na Hafsat Hassan, wadda aka fi sani da Ammi, kuma ni haifaffiyar Maiduguri ce, Ina da shekaru 27. Na yi makaranta zuwa sakandare. Amma dai a Kano na yi rayuwa har na yi aure na haifi yara uku, daga baya kuma auren ya mutu, kuma yanzu ga shi na samu kaina a cikin harkar fim.

To ya aka yi kika samu kan ki a cikin harkar fim?
Ka san duk abin da ya kasance kana da rabo a ciki, to sai ka same shi, don haka sai ya zama Ina rayuwa a cikin ‘yan fim ta dalilin ‘ya’yana, to da haka har na zo na ji Ina da sha’awar harkar.

To, da wane fim kika fara, kuma a wacce shekarar?
Na fara yin fim ɗin ‘Uwar Gulma’ a cikin shekarar 2021, kuma na yi waƙoƙi kamar guda biyar, sai kuma finafinan da na yi wanda zan fito kamar sin ɗaya sin biyu, sannan akwai finafinan Barkwanci da a ke sakawa a YouTube da sauran su.

To, an ce kina yin waƙoƙi na siyasa ma ko?
Gaskiya ne. Ina yin waƙoƙin siyasa domin na yi wa mutane da dama, kuma Ina kan yi ma a yanzu.

A yanzu an fara ganin fuskar ki ba kamar a baya ba, ko ya ya za ki kwatanta rayuwar ki ta baya da kuma a yanzu?
To rayuwa ta baya dai Ina yin ta cikin sauƙi, amma a yanzu sai ya zama kowa yana son ya yi magana da ni, to sai abin ya zame mini wani sabon abu, don yanzu duk in da na je sai a rinƙa cewa ai na gan ki a fim kaza, to sai abin ya yi ta burge ni, Ina son hakan, don haka wani lokacin ma idan zan je wani waje sai na saka abin rufe fuska, saboda idan muka je musamman wajen aiki sai ka ga yara suna zuwa suna so su yi hoto da mu. To haka dai nake rayuwar a yanzu, kuma na samu abubuwa da dama, don sai ka je waje haka mutane su karɓi lambar ka suna son su yi magana da kai, ka ga wannan sauyin rayuwa ne wanda a baya babu shi don ba kowa ya san ka ba.

To, yanzu wane irin buri kike so ki cimma a harkar fim?
Gaskiya Ina son na zama fitacciyar jaruma wadda za a rinƙa yin alfahari da ita a wajen tallata abubuwan da suka shafi al’adar mu ta Hausa da Kanuri.

Hafsat

To, ko kin samu wata matsala a shigowar ki cikin harkar?
Gaskiya ban samu ba, tun da daman na faɗa maka ni ina da gata a cikin ‘yan fim, domin ko a yanzu Ina alfahari da ubangida na Sani Indomie, domin shi ya fara saka ni a fim, kuma duk wata nasara da na samu to shi ne ya tsaya mini, don haka babu wata matsala da na samu.

Daga ƙarshe wane saƙo kike da shi?
To, saƙona dai ga masoya na shi ne, kada su ga muna harkar fim su rinqa ɗaukar mu ‘yan iska, Karuwai ne, don haka a daina yi mana wannan kalaman, domin kowanne aiki da ka gani, akwai nagari akwai na banza, don haka ba mu taru mun zama ɗaya ba.

To, madalla. Mun gode.
Ni ma na gode sosai.