03
Oct
Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Masana'antar fina-finai ta Kannywood a ƙarƙashin ƙungiyar ƙwararru ta masu shirya fim ta ƙasa MOPPAN, sun tsara wani haɗin gwiwa da Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi domin magance matsalar da ta ke yaɗuwa a tsakanin matasa a ƙasar nan. Shugaban ƙungiyar ta MOPPAN Dakta Ahmad Sarari ne ya bayyana hakan ga wakilin mu bayan wata ganawa da 'yan fim ɗin su ka yi da Shugaban Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyin na ƙasa, Janar Muhammad Buba mairitaya. Dakta Ahmad Sarari ya bayyana mana cewar, "zaman da muka yi da shugaban wannan Hukumar,…
