Nishadi

Mawaƙan Annabi suna rayuwa ne a gaɓa mai haɗari, inji Mahmoud Nagudu

Mawaƙan Annabi suna rayuwa ne a gaɓa mai haɗari, inji Mahmoud Nagudu

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Mahmoud Isma’il Ibrahim, wanda aka fi sani da Mahmoud Nagudu, fitaccen mawaƙi ne a fagen yabon Manzon Allah (SAW) tun yana ƙaramin yaro, sai dai ya yi fice ne a fagen waƙoƙin fim a shekarun baya. Amma dai yanzu ya daɗe ba a jin ɗuriyarsa a fagen waƙoƙin Nanaye, sai na yabon Manzon Allah kaɗai. Kasancewarsa mai ilimi a fagen yabon, ya sa Wakilin Manhaja a Kano, Mukhtar Yakubu, ya nemi tattaunawa da shi a kan abubuwan da yabon ya ƙunsa a fage na ilimin musamman ganin yadda a ke tafiyar da tsarin kara-zube a…
Read More
Kannywood: Mafari da makoma

Kannywood: Mafari da makoma

Daga AL'MUSTAPHA ADAM MUHAMMAD Wasan kwaikwayo wani al’amari ne mai daɗɗaɗen tarihi a rayuwar ɗan Adam. Ya samo asali ne shekaru aru-aru da suka wuce a daulolin Girkawa da Rumawa tun ɗaruruwan shekarun da suka shuɗe. Tun a wancan lakacin akan yi amfani da wasan kwaikwayo ne don nishaɗantarwa da zaburar da rundunonin sojojinsu da suka yi nasara a yaƙe-yaƙen su a wancan zamani. Haka zalika akan yi wasannin kwaikwayo don faranta wa masu mulki rai su samu cikakken muwalati da nishaɗi. A irin waɗannan lokuta ne makaɗa, masu iya bada hikayoyi, maraya da mutanen fadla masu barkwanci kan sheƙe…
Read More
Fim ɗin Gari Guda zai buɗe sabon shafin kallo a sinima – Darakta Sufyanu Kabo

Fim ɗin Gari Guda zai buɗe sabon shafin kallo a sinima – Darakta Sufyanu Kabo

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano A yanzu dai duk wani shiri ya kammala na fitowar sabon fim ɗin 'Gari Guda', wanda Kamfanin 'Islamic Film Empire' suka shirya, kuma Sufyanu Lawal Kabo ya bayar da Umarni.Ganin yadda fim ɗin ya bambanta da sauran fina-finan da aka saba shirya wa a masana'antar fina-finai ta kannywwod ne ya sa muka nemi jin ta bakin Daraktan fim ɗin Sufyanu Lawal Kabo don jin irin abubuwan da fim ɗin ya ƙunsa. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance: Akwai wani sabon fim da ka yi aikin sa, kuma ka ke…
Read More
An shirya gudanar da babban taron KILAF na bana

An shirya gudanar da babban taron KILAF na bana

Daga BASHIR ISAH Kamfanin Moving Image Limited tare da haɗin gwiwar Tsangayar Nazarin Sadarwa ta Jami'ar Bayero, Kano, sun shirya gudanar da babban taronsu na shekara-shekara na tallata harsunan gida na Kano a kasuwar fina-finai ta Afirka, wato Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival ko kuma KILAF a taƙaice. Taron KILAF na 2021 zai gudana ne a ranakun Litinin 22 da Talata 23 ga watan Nuwamban da ake ciki. Wannan shi ne karo na huɗu da ake shirya taron. Sanarwar manema labarai da ta sami sa hannun mu'assasin KILAF, Abdulkareem Mohammed da shugaban tsangayar nazarin sadarwa na…
Read More
Yadda aka fara haska fim ɗin Fanan a Sinima

Yadda aka fara haska fim ɗin Fanan a Sinima

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano A yanzu haka dai an fara haska shahararren fim ɗin  'FANAN' a Cinimar Platinium da ke kan titin Zaria, kusa da Masallacin Umar Bin Khaddab da ke cikin garin Kano. An daɗe dai ana ta sanar da bayyanar fim ɗin wanda aka shirya shi tare da kammala aikin sa kusan shekaru biyu da suka gabata. Kuma an ƙiyasta fim ɗin ya laƙume miliyoyin Naira. Fim ɗin dai na tsohuwar jaruma Mansurah Isah ne, wanda aka shirya shi a ƙarkashin kamfanin 'Today's Life' tare da haɗin gwiwar wasu kamfanoni domin samun ingantuwar aikin. A lokacin da…
Read More
Yadda zaɓen ƙungiyar MOPPAN reshen Abuja ya gudana

Yadda zaɓen ƙungiyar MOPPAN reshen Abuja ya gudana

Daga IBRAHIM HAMISU a Abuja Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya Fina-finai ta Nijeriya, Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) reshen Abuja ta gudanar da zaɓen shugabanni a ranar Asabar 30 ga Oktoba, 2021, a harabar ɗakin taro na kamfanin Kufaina Films da ke Abuja. Malaman zaɓen dai sun fara tantance 'yan takara da misalin ƙarfe 10:30 na safe. An kuma kammala tantance su ne zuwa ƙarfe 11:30, inda aka tantance 'yan takara guda 10. An fara kaɗa ƙuri'a ne da misalin 11:30 na safiyar a ƙarƙashin kulawar Babban Ma'ajin ƙungiyar MOPPAN ta ƙasa, Alhaji Bala Mu'azu Kufaina. Bayan ƙirga ƙuri'un…
Read More
Yadda na ci kyautar da wani jarumi a Kannywood bai ci ba – Gidan Dabino

Yadda na ci kyautar da wani jarumi a Kannywood bai ci ba – Gidan Dabino

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A makon jiya mun yi muku gabatarwa kan wannan tattaunawa da Manhaja ta yi da fitaccen jarumi kuma marubuci, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino (MON), inda mu ka yi muku alqawarin cewa, a wannan makon za mu kawo muku cikakkiyar tattaunawar. Shi dai Gidan Dabino ba baƙo ba ne a masana'antar Kannywood, domin su ne suka yanke mata cibiya, ya fara da dirama ne tun a shekarar 1984, wato shekaru 37 da suka gabata, a zantawarsa da wakilin Manhaja a Kano Ibrahim Hamisu, za ku ji yadda Ado Ahmad Gidan Dabino ya lashe kyautar jarumin…
Read More
Me ya sa Ado Gidan Dabino ya ke mamaye kyautar jarumin jarumai?

Me ya sa Ado Gidan Dabino ya ke mamaye kyautar jarumin jarumai?

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) ba baƙo ba ne a masana'antar Kannywood da kasuwar adabi, domin su ne suka yanke wa Kannywood cibiya. Ya fara da dirama (wasan daɓe) ne tun a shekarar 1984, wato shekaru 37 da suka gabata. A zantawarsa da Wakilin Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu, za ku ji yadda Ado Ahmad Gidan Dabino ya lashe kyautar jarumin jarumai har sau uku a shekara ɗaya kuma da fim ɗaya a fim ɗin ɗaya, wato Juyin Sarauta’. Ko a watan Nuwambar da ya gabata (2020), Malam Gidan Dabino (MON) ya samu nasarar lashe…
Read More
An yaye sabbin ɗaliban fim a Kano

An yaye sabbin ɗaliban fim a Kano

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano Bayan cigaban da makarantar koyar da harshen Turanci ta Jammaje Academy ta samu daga koyar da harshen Turanci zalla zuwa wasu kwasa-kwasai na koyar da sana'o'i da dabarun yin kasuwanci, a yanzu kuma makarantar ta fannin koyar da dabarun fitowa a fim, wato 'acting', ta kai ga matakin yaye ɗaliban da suka shiga cikin kwas ɗin a zango na farko. A ranar Lahadi, 10 ga Oktoba, 2021, aka gudanar da taron yaye ɗaliban guda 40 tare da ba wa wasu daga cikinsu shaidar kammala karatun nasu da suka yi na tsawon watanni. Taron, wanda aka…
Read More