Kasashen Waje

Hajjin bana: Ɗaurin watanni 6 da tarar Riyal 50,000 ga direban da ya yi jigilar alhazai ba tare da shaidar izini ba

Hajjin bana: Ɗaurin watanni 6 da tarar Riyal 50,000 ga direban da ya yi jigilar alhazai ba tare da shaidar izini ba

Daga WAKILINMU Sashen kula da sha'anin fasfo na Ƙasar Saudiyya ya yi gargaɗin cewa, duk wanda aka kama yana jigilar mahajjata ba tare da shaidar izini ba za a yi masa hukuncin ɗaurin wata shida a gidan kaso har da ƙarin tarar Riyal 50,000. Baya ga wannan, sashen ya kuma ce za a bayyana sunayen masu laifin a kafafen yaɗa labarai na cikin gida tare da ƙwace abubuwan hawan da aka yi amfani da su wajen aikata laifin. Kazalika, hukumar ta ce duk wani mai aikin Hajjin da aka kama da laifin yin amfani da kan sarki (Stamp) na bogi…
Read More
‘Yan sanda sun kama mutum 28 bisa zargin kashe Shugaban Ƙasar Haiti, Moïse

‘Yan sanda sun kama mutum 28 bisa zargin kashe Shugaban Ƙasar Haiti, Moïse

Daga BASHIR ISAH 'Yan Sandan Ƙasar Haiti sun kama wasu mutum 28 dukkansu baƙi da aka yi zargin suna da hannu cikin badaƙalar kashe Shugaban Ƙasar, Jovenel Moïse, a farkon wannan makon. Bayanan 'yan sandan sun nuna cikin waɗanda aka tsaren wasunsu sun taɓa yin aikin soja, kuma an kama yawancinsu ne bayan ɗauki ba daɗin da aka da aka yi na musayar wuta a wani gida da ke Port-au-Prince, babban birnin ƙasar. An gabatar da waɗanda ake zargin ga manema labarai jina-jina a ran Alhamis da ta gabata tare da wasu makamai da aka samu aka ƙwace a hannunsu.…
Read More
Cutar korona: Shugaba Bio ya kafa dokar hana fita a Sierra Leone

Cutar korona: Shugaba Bio ya kafa dokar hana fita a Sierra Leone

Daga WAKILINMU A matsayin wani mataki na yaƙi da ɓullar cutar korona karo na uku a ƙasar Sierra Leone shugaban ƙasar, Julius Maada Bio, ya bayyana kafa dokar hana zirga-zirga daga ƙarfe 11 na dare zuwa 5 na asuba, wadda za ta soma aiki Litinin mai zuwa idan Allah Ya kai mu. Ɗaukar matakin ya haɗa har da rufe masallatai da mujami'u, sai gidajen abinci da aka buƙaci su riƙa tashi da ƙarfe 9 na dare, sannan taron bukukuwa kada a wuce mutum 50. Bio ya bayyana ɗaukar matakin ne a Alhamis da ta gabata, tare da cewa an yi…
Read More
Raina kotu ya janyo wa Jacob Zuma zaman gidan yari na watanni 15

Raina kotu ya janyo wa Jacob Zuma zaman gidan yari na watanni 15

Babbar kotun ƙasar Afirka ta Kudu ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma hukuncin zaman gidan yari na watanni 15, bayan samunsa da aikata laifin raina kotu, biyo bayan ƙin bayyana a gaban masu binciken zargin rashawa da aka yi masa. An shaida wa Zuma cewa ya miƙa kansa nan da kwanaki 5, kuma idan ya ƙi yin biyayya za a umurci ‘yan sanda su tisa ƙeyarsa zuwa kurkuku. Wannan hukunci abu ne da ba a saba gani ba kuma cike yake da tarihi, don kuwa ya zama abin misali ga Afirka ta Kudu da ma nahiyar Afirka baki…
Read More
Jiri ya kwashi Shugaban Ƙasar Zambiya ya yanke jiki ya faɗi a taro

Jiri ya kwashi Shugaban Ƙasar Zambiya ya yanke jiki ya faɗi a taro

Daga AISHA ASAS Shugaban Ƙasar Zambiya, Edgar Lungu, ya yanke jiki ya faɗi a wajen wani babban taro na ƙasar da aka gudanar a Lahadin da ta gabata a Lusaka, babban birnin ƙasar. Jim kaɗan bayan faruwar lamarin, sakataren gwamnatin ƙasar, Dr Simon Miti, ya bayyana wa manema labarai cewa Shugaba Lungu ya wattsake har ma ya ci gaba da harkokinsa. Dr Miti ya ce jiri ne ya kwashi shugaban yayin da yake jawabi a wajen taron bikin Ranar Tunawa da Dakarun Ƙasar karo na 46 inda ya yanke jiki ya faɗi, amma cewa ya wattsake ba tare da jimawa…
Read More
Ƙuri’a ɗaya ta kawo ƙarshen mulkin Netanyahu na shekara 12 a Isra’ila

Ƙuri’a ɗaya ta kawo ƙarshen mulkin Netanyahu na shekara 12 a Isra’ila

Daga AMINA YUSUF ALI Firayiminista Benjamin Netanyahu, kuma firayiminista mafi daɗewa a Ƙasar Isra'ila ya yi adabo da kujerarsa. Hakan ta faru ne bayan majalisa ta sutale shi tare kuma da maye gurbinsa da wani sabon Firayiministan wanda aka zaɓo shi ta hanyar haɗin gwiwa da jam'iyyun siyasar da suke a ƙasar. A halin yanzu tuni sabon Firayiminista Mista Bennet ya ɗare kujerar Netanyahu wanda ya shafe tsawon shekaru goma sha biyu a matsayin firayiminista a ƙasar. Mr. Bennet dai ɗan ɓangaren mulkin ra'ayin riƙau ne na 'yan ƙasa. Kuma ana sa ran zai shafe shekaru biyu yana riƙe da…
Read More
Mutum 11 sun halaka a harin makaranta a Rasha

Mutum 11 sun halaka a harin makaranta a Rasha

Daga UMAR M. GOMBE Rahotanni daga Ƙasar Rasha sun nuna a ƙalla mutum 11 waɗanda galibinsu yara ne, suka mutu a harin da aka kai wata makaranta da ke yammancin Kazan a ƙasar. Kamfanin dillancin labarai na RIA da ke ƙasar, ya ruwaito cewa a ƙalla yara 16 zuwa 12 da kuma wasu mayan su 4 ne aka kwantar a asibiti bayan harin a Talatar da ta gabata. A cewar kamfanin dillancin labarai na Interfax, wasu 'yan bindiga biyu ne suka buɗe wa makarantar wuta inda suka yi ta harbin kan mai uwa dawabi. Hoton bidiyon harin da aka yaɗa…
Read More
Yaƙi da Boko Haram: Buhari ya kunyata Afirka – inji ɗan jairida a Ghana

Yaƙi da Boko Haram: Buhari ya kunyata Afirka – inji ɗan jairida a Ghana

Daga FATUHU MUSTAPHA Ɗan jaridar Ƙasar Ghana, Kwesi Pratt Jr, ya ce ya ji kunya matuƙa da ya ji cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda tsohon soja ne, ya nemi ƙasar Amurka da tallafa wa Nijeriya kan batun yaƙi da matsalolin da suka addabi ƙasar. Ɗan jaridar ya ce Shugaba Buhari ya tattara ya bar ofishinsa tun da ya gaza cika alƙawarin da ya ɗaukar wa 'yan Nijeriya. Shugaba Buhari yayin wata ganawa da Ƙaramin Sakataren Amurka, Anthony Blunkrn, a Talatar da ta gabata ya ce ya kamata ya yi a maida AFRICOM zuwa Afirka don ƙarfafa ƙoƙarin da ake…
Read More