Kasashen Waje

Naɗa ɗan marigayi Deby matsayin shugaban Chadi ya bar baya da ƙura

Naɗa ɗan marigayi Deby matsayin shugaban Chadi ya bar baya da ƙura

Daga UMAR M. GOMBE 'Yan hamayya a siyasar ƙasar Chadi sun ƙi amincewa da naɗin da sojojin ƙasar suka yi wa ɗan tsohon shugaban ƙasar, marigayi Idriss Deby a matsayin sabon shugaban riƙo na ƙasar. Sojoji sun naɗa Muhammat Kaka Idriss Deby a matsayin shugaban riƙo na ƙasar ne biyo bayan rasuwar mahaifinsa a Talatar da ta gabata. Sai dai da alama naɗin bai yi wa wasu 'yan ƙasar daɗi ba inda wasu 'yan siyasa masu hamayya suka fito suka nuna rashin amincewarsu game da naɗin tare da cewa ƙasar ba ta mulkin kama-karya ba ce. Kafin wannan lokaci, General…
Read More
Shugaban Chadi, Idris Deby ya rasu

Shugaban Chadi, Idris Deby ya rasu

Daga UMAR M. GOMBE Rahotanni daga ƙasar Chadi sun tabbatar da rasuwar Shugaban Ƙasar, Idris Deby Itno, mai shekaru 68. Bayanan sojojin ƙasar sun nuna marigayin ya kwanta dama ne sakamakon raunukan da ya samu a karawar da ya jagoranci dakarunsu wajen fatattakar ‘yan tawayen FACT na ƙasar. Bayanan sosjojin sun sake nuna cewa, marigayi Deby ya rasu ne jim kaɗan bayan sanar da nasarar da ya samu a babban zaɓen ƙasar da aka gudanar a ranar 11, Afrilu, 2021. A cewar Hukumar Zaɓen Chadi, marigayin ya lashe zaɓen ne da kashi 79.32 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa. Sanarwa…
Read More
‘Yan sandan Nijeriya 144 sun isa ƙasar Somaliya domin aikin bada tsaro

‘Yan sandan Nijeriya 144 sun isa ƙasar Somaliya domin aikin bada tsaro

Daga WAKILINMU Nijeriya ta tura gudunmawar 'yan sanda su 144 ya zuwa ƙasar Somaliya domin aikin tallafa wa fannin tsaron ƙasar. Nijeriya ta tura jami'an nata ne ƙarƙashin tawagar AMISOM ta ƙungiyar tarayyar Afirka (AU). Babban jami’in tsare-tsare na tawagar AMISOM a ƙasar, Daniel Ali Gwambal, ya bayyana cewa 30 daga cikin 'yan sandan za su yi aiki na tsawon shekara guda ƙarƙashin tawagar AMISOM, inda za a tura su yankunan Beletweyne da ke jihar HirShabelle, sauran kuma za su yi aiki a sassan birnin Mogadishu babban birnin ƙasar. Jami'in ya ce sauran ‘yan sandan za su yi ayyukan tsaro…
Read More
Nijar: Yadda gobara ta ci ƙananan yara 20 a makaranta

Nijar: Yadda gobara ta ci ƙananan yara 20 a makaranta

Daga BASHIR ISAH Ƙananan yara 'yan makaranta kimanin su 20 aka ruwaito sun halaka a ƙasar Nijar sakamakon gobarar da ta auku a wata makaranta. Wannan mummunan al'amari ya faru ne a Talatar da ta gabata a gefen Niamey, babban birnin ƙasar, inda iyaye da malamai haɗa da sauran al'ummar yankin suka kasance cikin alhini mara misaltuwa. Gobarar ta ci yaran ne a cikin azuzuwan da aka gina da katakai, kamar yadda shaidu suka bayyana. Daraktar makarantar, Habiba Gaya, cikin kuka da hawaye ta faɗa wa jaridar AFP cewa haka yaran suka ƙone a cikin gobarar. Ta ce wasu daga…
Read More

Zimbabwe: Ɗalibai 106 sun kamu da cutar korona cikin sa’o’i 24

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga ƙasar Zimbabwe sun nuna ya zuwa ranar Alhamis da ta gabata, an samu ɗalibai 106 daga wasu makarantun ƙasar guda biyu da suka harbu da cutar korona a cikin yini guda. Sakamakon gwajin da aka yi ya nuna cewa ɗalibai 51 sun kamu da cutar daga makarantar Sacred Heart GirlsHigh School da ke Esigodini, sannan ɗalibai 55 daga makarantar Umzingwane High School. Kawo yanzu, ƙasar mai yawan al'ummar da ya haura milyan 15, mutum 1,525 aka tabbatar cutar korona ta yi ajalinsu. Sai dai a daidai lokacin da aka sake buɗe makarantun ƙasar, tsoron cewa…
Read More

Bazoum ya naɗa sabbin ministocin sa a Nijar

Shugaba Bazoum Daga UMAR M. GOMBE Sabon Shugaban Ƙasar Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya naɗa sabbin ministoci da za su yi aiki a gwamnatin sa, kamar yadda sanarwar da Sakataren Gwamnatin ƙasar ta bayyana a ranar Larabar da ta gabata. Sanarwar ta ƙara da cewa, an naɗa sabbin ministoci 33, kuma shida daga cikin su mata ne. Hakan na nufin adadin ministocin ya ragu idan aka kwatanta da ministoci 43 da suka yi aiki a gwamnatin tsohon shugaba Mahaman Issoufou. Naɗin ministocin ya faru ne a yayin da sabon Fira Ministan Jamhuriyar ta Nijar Ouhoumoudou Mahamadu ya sha rantsuwar kama…
Read More

Shugaba Ouattara ya ce Gbagbo da Ble za su iya dawo wa gida

Alassane Ouattara Daga UMAR M. GOMBE Shugaban Ƙasar Kwaddebuwa, Alassane Ouattara ya ce tsohon shugaban ƙasar Laurent Gbagbo da kuma jagoran matasa ’yan gani-kashe-ni da ke mara masa baya wato Charles Ble na iya komawa gida a duk lokacin da suke buƙata, bayan da kotun duniya ta ICC ta wanke su daga laifukan da ake zargin su da aikatawa. Shugaba Ouattara, wanda ke jagorantar taron majalisar ministocin ƙasar a ranar Larabar da ta gabata, ya ce bayan dawowar sa a gida tsohon shugaba Laurent Gbagbo zai ci moriyar illahirin haƙƙoƙin da doka ta ce a bai wa tsohon shugaban ƙasar.…
Read More