Labarai

A kan ƙarfin iko ne muke saɓani da Wike – Fubara

A kan ƙarfin iko ne muke saɓani da Wike – Fubara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara ya ce saɓaninsa da tsohon gwamnan jihar, bai wuce saboda ƙarfin ikon jan ragamar jihar ba. Fubara ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da tashar talabijin na Channels a ranar Litinin, a lokacin da yake bayyana rikicin da ya dabaibaye siyasar jihar, inda bayan zaɓen ƙananan hukumomi aka wayi gari da rigima. A game da alaƙarsa da Wike, Fubara ya ce, "gaskiya ba zan so in wannan maganar ba a nan, amma duk waɗanda suka san abin da ke faruwa, sun san cewa a kan ƙarfin ikon jan ragamar…
Read More
APC ta mayar da martani ga Amaechi, suna zargin shi da cin amanar jam’iyya

APC ta mayar da martani ga Amaechi, suna zargin shi da cin amanar jam’iyya

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta caccaki tsohon Ministan Sufuri a gwamnatin da ta gabata kuma tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, bisa zarginsa da tada zaune tsaye ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Amaechi a wata hira da yayi a baya-bayan nan ya caccaki matasan Nijeriya kan rashin yin zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa a ƙasar. Da yake mayar da martani ga jawabin a wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa Felix Morka ya fitar ranar Juma’a a Abuja, jam’iyyar mai mulki ta bayyana kalaman Amaechi a matsayin “rashin gaskiya da rashin kishin ƙasa.” A cewar…
Read More

APC reshen Bayelsa ta dakatar da Lokpobiri da wasu jiga-jigan jam’iyyar

Daga BELLO A. BABAJI Jam'iyyar APC reshen Jihar Bayelsa ta dakatar da ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri da ɗan takarar gwamnan jihar a 2019, David Lyon saboda ayyukan zagon-ƙasa. An kuma dakatar da wasu manyan jam'iyyar da suka haɗa da; Kwamishinan Lantarki, Kharim Kumoko; Kwamishinan filaye da safiyo, Peres Biewari; da tsohon shugaban jam'iyyar a jihar, Jothan Amos; da Godbless Diriwari, da kuma Shugaban matasan jam'iyyar reshen kudancin Ijaw, Sabi Morgan. Sauran sun haɗa da; shugaban jam'iyyar a ƙaramar hukumar Ekeremor wanda Mitin Eniekenemi Senator ya sanar da hakan. Eniekenemi Senator ya ce sun ɗauki matakin ne daga…
Read More
Ɗiyar Mele Kyari ta rasu

Ɗiyar Mele Kyari ta rasu

.Shugaban kamfanin NNPCL , malam Mele Kyari ya rasa ‘yarsa Fatima wadda ke da shekaru 25 a duniya a ranar Juma’a. Sai dai mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya jajanta wa Kyari da iyalansa, inda ya yi addu’ar Allah ya jiƙan Fatima da rahama. Shettima ya kuma yi addu’ar Allah ya baiwa ‘yan uwa hakurin jure wannan babban rashi. Mataimakin shugaban ƙasar ya bi sahun sauran masu jana'iza, wanda aka gudanar a masallacin Annur da ke Abuja.
Read More

Yana yiwuwa a kawo ƙarshen tashin hankali ga yara – Rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya

Wakiliyar Majalisar Ɗinkin Duniya ta musamman kan cin zarafin ƙananan yara, Dakta Najat Maalla M’jid ta bayyana cewa yawan cin zarafin ƙananan yara a duniya na ƙaruwa. Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya da aka fitar a ranar 10 ga watan Oktoba, ya jaddada cewa ta hanyar yin aiki tare jihohi za su iya kawar da wannan mummunar dabi'a. "Bayanan da aka nuna a cikin rahoton na da ban tsoro kuma mai yiwuwa ba a yi la'akari da su ba. “Yara sama da miliyoyi a duniya suna fama da tashe-tashen hankula na zahiri, jima'i, aikin yara, auren yara, kaciyar mata, cin…
Read More
Tsagin jam’iyyar PDP sun naɗa Yayari Ahmed a matsayin shugaban riƙon ƙwarya

Tsagin jam’iyyar PDP sun naɗa Yayari Ahmed a matsayin shugaban riƙon ƙwarya

Jam'iyyar PDP ta naɗa Ahmed Yayari wanda shine ma'ajin jam'iyyar a matsayin sabon shugaban ta na riƙon ƙwarya bayan dakatar da Umar Damagun da wani tsagin kwamitin gudnarwar jam'iyyar ya yi. Sanarwa ta fito a wata takarda wadda sakataren jam'iyyar Hon. Debo Ologunagba ya sanya wa hannu a ranar Juma’a a Abuja. Sanarwar ta bayyana Yayari Ahmed a matsayin sabon shugaban riƙon ƙwarya kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya bada damar yin hakan. Kwamitin ya roƙi mambobi da su haɗe kansu kuma su maida hankali ga taron kwamitin gudanarwa da ake sa ran za ayi 24 ga watan Oktoba…
Read More

Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar dakatar da zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Daga BELLO A. BABAJI Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta ƙi amincewa da buƙatar wani ɓangare na jami'yyar NNPP da ke neman a dakatar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka shirya yi a ranar 26 ga watan Oktoba, 2024. Waɗanda suka shigar da ƙarar sune NNPP da Injiniya Muhammad Babayo inda suka nemi kotun ta umarci Hukumar zaɓe ta jihar da Sufeton ƴan sanda da hukumar DSS su dakatar da yin zaɓen har sai an yi shari'a game da wani batu da aka jingine. Kuma sun buƙaci kotun ta umarci dukkan waɗanda aka zayyano a matsayin waɗanda…
Read More

Haƙiƙanin bayanai game da yaƙin Gaza – Ofishin jakadancin Palestine

Daga BELLO A. BABAJI Gidajen jaridu masu ɗaukar ɓangaranci daga yankin Yammacin duniya sun yi ta yaɗa labarai da ke tattare da ƙarairayi, waɗanda ke cike da zarge-zarge marasa tushe ko asali game yaƙin Gaza. Babbar abin tambayar a nan ita ce, mene ne haƙiƙanin abin da ya faru? Wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Ambasadan ofishin jakadancin ƙasar Palestine, Abdullah M. Abu Shawesh, ta yi bayani kamar haka; Dole sai Majalisar Ɗinkin Duniya ta naɗa kwamitin bincike tare da samar da rahoto na ƙarshe da yin adalci kan waɗanda aka tabbatar su na da hannu acikin laifukan…
Read More

Gwamna Abba ya bada tallafin N100m ga waɗanda gobarar kasuwar Kantin Kwari ta shafa

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a madadin gwamnatin jihar ya sanar da bada tallafin Naira miliyan 100 ga waɗanda iftila'in gobara ta rutsa da su a kasuwar Kantin Kwari da ke jihar. Gwamnan ya faɗi hakan ne a lokacin da ya jagoranci tawagar manyan ma'aikatan gwamnatinsa zuwa kasurwar a yau Juma'a don jajenta musu. Cikin wata takarda da Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Gwamna Abba ya ce gwamnatin jihar na jajenta wa waɗanda shagunansu suka ƙone ya yayin aukuwar lamarin. Ya ce, tallafin ba ya nufin biyansu asarar da suka yi na iftila'in,…
Read More

Dalilin da ya sa sojoji ba su ɗauki mataki kan Asari-Dokubo ba – Hedikwatar Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Alhamis ne Hedkwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce ta zaɓi ƙin ɗaukar mataki ne akan tsohon shugaban mayaƙan yankin Nija-Delta, Mujahid Asari-Dokubo don kar a zarge ta da saɓa wa ƙa'idar demokraɗiyya. Daraktan Labarai na Hedikwatar, Manjo-Janar Edward Buba ya bayyana hakan wa manema labarai a lokacin da ya ke tsokaci game da zargin cewa Asari-Dokubo ya yi barazanar kakkaɓo wani helkwaftan sojoji da ya gitta ta yankin gidansa. Saidai, kakakin rundunar ya bayyana hakan da Asari-Dokubo ya yi a matsayin abin dariya inda ya ƙalubalance shi da ya tunkari sojoji a filin yaƙi…
Read More