12
Oct
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Yayin da ake cigaba da shirye-shiryen gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi a jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani ya yi kurin cewa jam’iyyarsa ta APC ce za ta lashe kujerun shugabannin ƙananan hukumomi da na kansiloli kaf ɗinsu. Gwamna Sani ya bayyana haka ne a makon jiya yayin da yake miƙa wa 'yan takarar jam’iyyar na APC tuta. Taron ya samu halartar gaggan jam’iyyar APC, da magoya baya daga duka ƙananan hukumomin jihar. Yayin da yake jawabi gwamna Sani ya ce jam’iyyar APC ce jam’iyya ɗaya tilo a jihar Kaduna yanzu. Babu wata jam’iyya da…
