15
Sep
Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya roƙi al'ummar Jihar Edo su zaɓi ɗan takarar APC, Sanata Monday Okpebhol a zaɓen gwamna da za a yi a ranar Asabar don samun shugabanci mai inganci. Shettima, wanda ya halarci taron rufe yawon neman zaɓen ɗan takarar tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar a Benin babban birnin jihar, ya ce a halin da ake ciki, Edo ta na buƙatar jagora mai basira da iya gina al'umma wanda zai kai ga samun nasarori ga mutanensa. Ya kuma bayyana wa al'ummar jihar cewa, samun jiha mai cike da damanmaki shi ne burinsu…
