14
Sep
Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a ne Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya kai ziyara sansanin ƴan gudun hijira na Gwada da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja. Ya ce, Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin kai ziyarar don duba halin da mutanen da ambaliya da rashin tsaro suka yi sanadiyyar komawarsu wajen da kuma tallafa mu su. Ya bayyana alhinisa game da rayuka da dukiyoyin da aka rasa yayin aukuwar lamuran, ya na mai jajenta wa ƙananan hukumomi 14 na jihar da hakan suka shafe su. Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma tabbatar da cewa, gwamnatin Tinubu a…
