30
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya a ranar Alhamis ta ce za ta yi amfani da manufar ‘babu aiki, ba albashi’ kan yajin aikin likitoci a Nijeriya. Ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta tarayya ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mataimakin daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Ado Bako. Sanarwar ta ƙara da cewa ma’aikatar ta ji takaicin matakin da ƙungiyar likitocin mazauna Nijeriya ta ɗauka na shiga yajin aikin gargaɗi na tsawon kwanaki bakwai, inda ta yi watsi da duk wata tattaunawa da kuma ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi…
