Labarai

Cire tallafin mai: Har yanzu gwamnati ba ta fara ba mu tallafin N25,000 da ta yi alƙawari ba — ‘Yan fansho

Cire tallafin mai: Har yanzu gwamnati ba ta fara ba mu tallafin N25,000 da ta yi alƙawari ba — ‘Yan fansho

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mambobin ƙungiyar 'Yan Fansho ta ƙasa a ranar Talata sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta cika alƙawarin da ta yi na biyansu Naira 25,000 na wata-wata domin rage raɗaɗin janye tallafin man fetur. Tsoffin ma’aikatan sun kuma nemi Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya bada umarni ga hukumar kula da albashi ta ƙasa da ta fitar da sanarwar bada damar aiwatar da mafi ƙanƙantar kuɗin fansho kamar yadda aka amince da mafi ƙarancin albashi. A shekarar da ta gabata ne dai, gwamnatin ta yi alƙawarin biyan ma’aikata dubu 35 da 'yan…
Read More
Muna yin bakin ƙoƙarinmu kan matsalar tsaro – Gwamnatin Sakkwato

Muna yin bakin ƙoƙarinmu kan matsalar tsaro – Gwamnatin Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Bayan an shafe kwanaki ana sukar yadda gwamnatin jihar Sakkwato ke tafiyar da sha’anin tsaro, musamman bayan garkuwa da kuma kashe Sarkin Gobir na Gatawa, a yanzu hukumomin jihar sun bayyana cewa suna iyakar ƙoƙarinsu kan matsalar. A makon da ya gabata ne 'yan bindiga suka kashe Sarkin Gobir, Muhammad Isa Bawa, bayan yin garkuwa da shi na sama da mako uku, lamarin da ya janyo wa hukumomi kakkausar suka. Wasu dai a Nijeriya na zargin hukumomi da gaza yin abin da ya kamata wajen kawar da matsalar tsaro a faɗin ƙasar. 'yan fashin…
Read More
Sojoji ba za su saurari kiraye-kirayen kifar da gwamnatin Tinubu ba – Lagbaja

Sojoji ba za su saurari kiraye-kirayen kifar da gwamnatin Tinubu ba – Lagbaja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar-Gen Taoreed Lagbaja, ya bayyana cewa sojoji ba za su saurari kiraye-kirayen kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba. Lagbaja ya bayyana haka ne a ranar Talata a wajen bikin buɗe taron COAS Combined 2nd and 3rd ƙuarters a Uyo, jihar Akwa Ibom. A cewar Lagbaja, kiraye-kirayen shiga tsakani na soji ya fi fitowa ne daga matasan Nijeriya da ba su fuskanci zamanin mulkin soja na Nijeriya ba. Ya ce rundunar sojin Nijeriya ta gina wani sabon martaba a cikin shekaru 25 da suka gabata ta hanyar ba da damar…
Read More
Ya kamata matasa su ƙara himma wajen neman ilimi da sana’o’i – Barista Ahmed UPE

Ya kamata matasa su ƙara himma wajen neman ilimi da sana’o’i – Barista Ahmed UPE

Daga DAUDA USMAN a Legas Wani matashi mai suna Barista Lawal Ahmed UPE a Funtuwa ta jihar Katsina kuma jigo a tafiyar matasan jam'iyyar NNPP a jihar, ya shawarci matasan Funtuwa da na jihar Katsina da ma na ƙasar nan baki ɗaya da su ƙara ƙoƙari kuma su kasance masu neman ilimin boko da na Islamiyya tare da koyon sana'o'in dogaro da kai a Nijeriya baki ɗaya. Barista Lawan Ahmed UPE Funtuwa ya yi wannan tsokaci ne a Funtuwa a lokacin da yake karɓar baƙuncin waɗansu gungun matasan jam'iyyar NNPP na jihar Katsina da kewayenta da suka kawo masa gaisuwar…
Read More
Indonusiya da KASCOTEe sun yi bajekolin kamfanoni sama da 60 a Kano

Indonusiya da KASCOTEe sun yi bajekolin kamfanoni sama da 60 a Kano

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Ƙasar Indonusiya ƙarƙshin shugabancin Dr H. Usara jakadanta a Nijeriya da haɗin gwiwar majalisar 'yan kasuwa da masana'antu ta Jihar Kano da ake kira KASCOTE ƙarƙashin shugabanta Alhaji Hassan Tahir Yaro, ta yi gagarimin taron bajekolin kamfanoni sama da 60 na wajen ƙasar nan musamman kamfanonin ƙasar Indonusiya da wasu ƙasashen Afirka, da kamfanonin gida Nijeriya. A taron bajekolin irinsa na farko a tarihin Kano da aka fara ranar Talata aka kammala a ranar Asabar ɗin nan a titin Magajin Rumfa da ke Kano, a jawabinsa shugaban KASCOTE Hassan Tahir Yaro ya ce na da…
Read More
An buɗe ofishin dangantakar kasuwanci tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Benin a Kano

An buɗe ofishin dangantakar kasuwanci tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Benin a Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Hukumar hana  fasa kwauri ta ƙasa ta jaddada aniyarta na inganta gudanar da halaltacciyar kasuwanci ta hanyar tabbatar da tsaron kan iyaka. Kwanturola Janar na hukumar Bashir Adewale Adeniyi ne ya bayyana hakan a wajen bikin ƙaddamar da wani ofishin kasuwanci a Kano tsakanin Nijeriya da Jam'iyyar Benin. Kwanturola Janar na ƙasa da  Mataimakinsa Sambo  ɗangaladima ya wakilta ya ce an ƙaddamar da ofishin kasuwanci ne a matsayin wani babban tsari na inganta harkokin kasuwanci da haɓaka kasuwanci tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Benin. Ya ƙara da jaddada ƙudirin Hukumar hana fasa kwauri ta ƙasa na…
Read More
Dattijuwa mai shekaru 54 ta haifi jarirai 11 bayan samun ciki sama da shekaru uku

Dattijuwa mai shekaru 54 ta haifi jarirai 11 bayan samun ciki sama da shekaru uku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata ‘yar Nijeriya mai shekaru 54 mai suna Alake Latoyosi ta haifi jarirai 11 a birnin Cotonou na jamhuriyar Benin bayan ta ɗauki ciki sama da shekaru 3. A cewar mijin matar, Yahaya Nafiu, saitin farko na shida ya zo ne a ranar 7 ga Agusta, yayin da na biyu ya zo bayan kwanaki bakwai, a ranar 14 ga Agusta, 2024. Nafiu ya ce jariran maza takwas ne mata uku amma biyu daga cikin ‘yan matan sun rasu ne a lokacin haihuwa. Mijin mai shekaru 56 ya bayyana cewa cikin yaran ya wuce shekaru…
Read More
Ku ƙaurace wa wuraren ambaliya – Gwamnatin Kaduna

Ku ƙaurace wa wuraren ambaliya – Gwamnatin Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMAMD Biyo bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta lalata gidaje sama da 200 a ƙananan hukumomin Sabon Gari da Zariya a ranar Litinin, Gwamnatin Jihar Kaduna ta buƙaci mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su gaggauta ficewa. Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KASEMA) Dakta Usman Hayatu-Mazadu wanda ya yi wannan roƙo a lokacin da yake zantawa da manema labarai a daren ranar Talata, inda ya yi bayani dalla-dalla kan ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi na daƙile illar ambaliyar. Waɗannan ƙoƙarin sun haɗa da tsaftace magudanun ruwa…
Read More
Za mu fafata da ’yan bindiga cikin kwana 30 – Gwamnatin Katsina

Za mu fafata da ’yan bindiga cikin kwana 30 – Gwamnatin Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina  A ƙoƙarin da gwamnatin jihar Katsina ke yi na yaƙi da ta'addanci, gwamnatin jihar ta ƙaddamar da wani shirin fatatattakar 'yan bindiga dake garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa. Shirin haɗin gwiwa ne tsakanin jami'an tsaro, gwamnati da kuma masu ruwa da tsaki a harkar tsaro. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Nasir Muazu ne ya sanar da hakan ga manema labarai, bayan wani taron majalisar tsaro ta jiha. Gwamna Raɗɗa ne ya kira taron da nufin magance yawaitar hare-haren ‘yan bindiga waɗanda ke amfani da lokacin damina don aikin ta'addanci. Kwamishinan ya ce,…
Read More

Blueprint ta rasa ɗaya daga cikin manyan ma’aikatanta

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Alhamis 29 ga watan Agusta, 2024 jaridar Blueprint ta rasa ɗaya daga cikin manyan ma'aikatanta, Mista John Oba bayan wata gajeruwar rashin lafiya da yayi fama da ita. Kafin rasuwarsa, Mista Oba shine shugaban ɓangaren ruwaito labaran noma na jaridar. Wani daga cikin makusantansa ya ce da farko an kai shi babban asibitin da ke Wuse ne a Abuja inda ba a samu likitan da zai duba shi ba wanda daga nan ne aka kai shi asibitin Kings Care a 'Wuse Zone 4' inda yayin da aka isa, sai likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.…
Read More