30
Aug
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana damuwarsa kan yadda ambaliya ta lalata wasu garuruwa da amfanin gona a sassan ƙasar. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya fitar, Tinubu ya nuna damuwa ga iyalan da suka rasa makusantansu, manoma, garuruwan da suka lalace da kuma waɗanda suka rasa dukiyoyinsu. Wani bincike da hukumar bada agaji ta gaggawa, NEMA ta yi a kwanan nan ya nuna cewa, an rasa rayuka da dubunnan filayen noma da suka lalace da kuma dubunnan al'umma da suka rasa matsugunansu a faɗin Nijeriya. Tinubu ya sake nanata buƙatar…
