25
May
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa, EFCC, ta gurfanar da Hadi Sirika, tsohon ministan sufurin jiragen sama a gaban kotu bisa zargin almundahanar kwangila. EFCC ta gurfanar da Sirika ne tare da ɗan uwansa, Ahmad Abubakar Sirika kamfanin da Enginos Nigeria Limited, wani kamfani mallakin Abubakar, a gaban mai shari’a Suleman Belgore na babban kotun babban birnin tarayya Abuja da ke zaune a Garki, Abuja. An gurfanar da su a gaban kotu kan tuhume-tuhume 10 da aka gyara ranar 13 ga Mayu kuma aka shigar da su ranar 14 ga Mayu,…
