Labarai

An bai wa tsofaffin sarakunan Kano sa’o’i 48 su fice daga masarautu

An bai wa tsofaffin sarakunan Kano sa’o’i 48 su fice daga masarautu

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Gwamnatin jihar Kano ta bai wa tsofaffin sarakunan masarautun Kano; Rano da Gaya da Bichi da Ƙaraye wa’adin sa’o’i 48 su fice daga fada bayan rushe masarautun da gwamnatin ta yi a ranar Alhamis. Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da haka lokacin da ya yi jawabi jim kaɗan bayan sanya hannu kan dokar da ta rushe dokar da ta assasa masarautun a shekara ta 2019. A ranar Alhamis ne Gwamnan ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautar Kano, wadda ta rushe ƙarin masarautu huɗu da aka samar a 2019, wanda hakan ya…
Read More
Babu sarki a Kano a halin yanzu — Majalisa

Babu sarki a Kano a halin yanzu — Majalisa

Biyo bayan soke masarautun da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta ƙirƙiro a Kano a zaman da ta yi ranar Alhamis, Majalisar Dokokin Jihar ta ce a halin yanzu babu sarki a Kano. Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa, shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa manema labarai ƙarin haske dangane da matakin rushe masarautun da majalisar ta ɗauka. Ya ce a halin da ake ciki an aike da dokar masarautun da aka yi wa kwaskwarima ga Gwnan Kano, Abba Kabir, don ya rattaɓa hannu. Ya kara da cewa, dokar ta bai wa Gwamna…
Read More
Majalisar Dokokin Kano ta rushe sabbin masarautun da Ganduje ya ƙirƙiro

Majalisar Dokokin Kano ta rushe sabbin masarautun da Ganduje ya ƙirƙiro

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da rushe sabbin masarautu huɗu da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ƙirƙiro a jihar. Majalisar ta kuma rage matsayin sarakunan masarautun da abin ya shafa zuwa hakimai. Masarautun da lamarin ya shafa su ne; Bichi, Gaya, Karaye da kuma Rano. Majiyarmu ta ce an girke jami’an tsaron hukumar DSS a Fadar Sarkin Kano a safiyar Alhamis da ake soke sabbin masarautun.
Read More
Cikar Tinubu shekara guda kan mulki: Babu wani bukin a-zo-a-gani da za a shirya —Idris

Cikar Tinubu shekara guda kan mulki: Babu wani bukin a-zo-a-gani da za a shirya —Idris

Ministan Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa, ba za a shirya wani biki na a-zo-a-gani ba don cikar Shugaba Bola Tinubu shekara ɗaya a kan mulkin Nijeriya. Idris ya shaida wa manema labarai haka ne ranar Laraba a Abuja. A cewar Ministan, an ɗauki wannan mataki ne don cika manufar Tinubu ta yi wa ƙasa hidima yadda ya kamata da kuma yin amfani da dukiyar ƙasa don amfanin 'yan ƙasa. Ya ce, “bukin ba zai zama ƙasaitacce ba, illa iyaka za a bai wa ma'aikatu damar yin bayani kan ayyukansu. “Wannan ya yi daidai da manufar…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Gobara a sakatariyar gwamnatin Kaduna

Da Ɗumi-ɗumi: Gobara a sakatariyar gwamnatin Kaduna

Bayanan da muka samu yanzu-yanzu daga Jihar Kaduna sun ce, an samu aukuwar gobara a sakatariyar gwamnatin jihar, lamarin da ya yi sanadaiyar ƙonewar wasu ofisoshi. Wani ganau, Malam Ibrahim Mohammed, wanda ma'aika gwamnatin jihar ne, ya ce iftila'in ya auku ne da misalin ƙarfe 2:30 na rana wannan Larabar. Ya ce duk da dai ba a kai ga gano musababbin gobarar ba, amma ana zargin hakan ba ya rasa nasaba da wutar lantarki. Ya ƙara da cewa, ba a samu asarar rai ba, amma muhimman kayayyaki da dama sun ƙone ƙurmus. Ya zuwa haɗa wannan labari, babu wani ƙarin…
Read More
Ƙungiyoyin mata sun buƙaci a inganta samar da abinci mai gina jiki ga jarirai

Ƙungiyoyin mata sun buƙaci a inganta samar da abinci mai gina jiki ga jarirai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu ƙungiyoyin addini masu zaman kansu na mata sun yi kira da a inganta abinci mai gina jiki ga jarirai da ƙananan yara a ƙasar. Shugabannin Ƙungiyar Mata Musulmi ta Nijeriya; Sakatariyar Katolika ta Nijeriya; Ƙungiyar Matan Kirista ta Nijeriya; da kuma Cocin 'Redeemed Christian Church of God' sun yi wannan kiran ne a lokacin ziyarar da su ka kai na bada shawarwari ta hanyar Cibiyar Sadarwa da Tasirin zamantakewa, ga mata a wasu yankuna, tare da kira da a inganci abincin da mata ke ci domin su samu damar bai wa jarirai abinci mai gina…
Read More
Matashin da ya cinna wa masallata wuta a Kano ya amsa laifinsa

Matashin da ya cinna wa masallata wuta a Kano ya amsa laifinsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Matashin da ya banka wa masu sallah a Masallaci wuta a jihar Kano, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa a gaban kotu. Mutumin mai shekara 39 wanda ya gurfana a gaban wata kotun shari'ar Musulunci da ke birnin na Kano, inda aka tuhume shi da laifuka uku, ya ce ya amince da tuhume-tuhumen da aka karanta masa. A ranar Laraba 15 ga watan Mayu ne matashin ya cinna wuta a wani masallaci da ke ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano, daidai lokacin da ake ibada. Yanzu haka mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar…
Read More
Majalisar Dokokin Kano ta kama hanyar yi wa Dokar Masarauta kwaskwarima

Majalisar Dokokin Kano ta kama hanyar yi wa Dokar Masarauta kwaskwarima

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kama hanyar yi wa Dokar Masarautu kwaskwarima bayan shan kiraye-kiraye kan a dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammad Sanusi, wanda tsohuwar gwamnatin Umar Ganduje ta tsige. Majalisar ta yanke shawarar yi wa dokar kwaskwarima ne bayan da Shugaban Masu Rinjaye, Hussien Dala, mai wakiltar Mazaɓar Dala, ya miƙa ƙorafinsa yayin zaman majalisar a ranar Talata. An fara yi wa wannan doka kwaskwarima ne a 2019 bayan da ruwa ya yi tsami tsakanin gwamnan jihar na wancan loakci, Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano na 14, Sunusi. Sakamakon gayaran da aka yi wa dokar a…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe sama da mutum 40 a Filato

‘Yan bindiga sun kashe sama da mutum 40 a Filato

Bayanan da suka iso mana yanzu daga jihar Filato sun ce, 'yan bindiga sun kai ƙazamin hari ƙauyen Zurak da ke Gundumar Bashar District cikin ƙaramar hukumar Wase, Jihar Filato, inda suka kashe sama da mutum 40. A cewar mazauna yankin lamarin ya faru ne ranar Litinin da misalin karfe 5 na yamma yayin da jama'a ke gudanar da harkokinsu. Sun ƙara da cewa, ba su samau damar sanar da abin da ya auku d wuri ba ne sakamakon rashin kyawun sabis a yankin. Wani shugaban matasan yankin mai suna Sahpi’i Sambo, ya tabbatar da aukuwar harin ga jaridar Daily…
Read More