Labarai

Jerin wuraren da za a tantace masu neman aikin ɗan sanda

Jerin wuraren da za a tantace masu neman aikin ɗan sanda

Daga BASHIR ISAH Hukumar kula da shirin ɗaukar sabbin jami’an ’yan sanda ta fitar da jerin cibiyoyi guda 20 wanda a nan za a gudanar da shirin tantance masu neman aikin ɗan sanda a faɗin ƙasa. Hukumar Kula da Harkokin ’Yan Sanda (PSC) ce ta kafa wannan hukumar don taimaka mata wajen gudanar da shirin ɗaukar sabbin ƙananan jami’ai da ke gudana. Jaridar Daily Trust ta rawaito Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ‘Yan Sanda, Ikechukwu Ani, ya faɗa cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis cewa, yanzu ana kan matakin tantance lafiyar masu neman shiga aikin…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Ɗan daudu, Bobrisky ya faɗa a komar EFCC

Da Ɗumi-ɗumi: Ɗan daudu, Bobrisky ya faɗa a komar EFCC

Daga BASHIR ISAH Hukumar Yaƙi da Rashawa ta EFCC, ta tsare ɗan daudun nan, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky, bisa zargin wulaƙanta takardun kuɗi na Naira. Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, shi ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce an tsare Bobrisky ne ranar Laraba da misalin ƙarfe 3 na rana a rukunin gidaje na Pinnock Estate da ke Legas bisa zargin watsa takardun Naira a wajen taro wanda hakan cin mutuncin kuɗin ƙasa ne
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya rattaɓa hannu kan Dokar Bai wa Ɗalibai Rancen Karatu

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya rattaɓa hannu kan Dokar Bai wa Ɗalibai Rancen Karatu

Daga BASHIR ISAH A ranar Laraba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya rataɓɓa hannu kan Dokar Bai wa Ɗalibai Rancen Karatu ta 2024. Da wannan, sabuwar dokar za ta fara aiki ke nan, inda za ta bai wa ɗalibai a manyan makarantu zarafin samun rance daga gwamnati domin gudanar da harkokin karatunsu. Tinubu ya sanya wa dokar hannu ne bayan da Majalisar Tarayya ta nazarci rahoton Kwamitin Kula da Manyan Makarantu da kuma asusun TETFund.
Read More
Gwamnatin Zamfara ta kafa dokar taƙaita zirga-zirga a wasu sassan jihar

Gwamnatin Zamfara ta kafa dokar taƙaita zirga-zirga a wasu sassan jihar

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Zamfara ta kafa dokar taƙaita zirga-zirga a yankunan da take iyaka da jihohin Katsina da Sakkwato a matsayin ɓangare na yaƙi da matsalolin tsaron da suka addabi ƙasar. Dokar za ta fara aiki ne daga ƙarfe na 7:00 na dare zuwa 6:00 na safe. Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al'adu na Jihar, Manir Haidara, shi ne ya bayyana haka a ranar Talata. Haidara ya ce dokar na daga shawarwarin da Majalisar Tsaron jihar ta bayar a wajen taronta. A cewar Kwamishinan, “Daga yau, gwamnatin jihar ta ba da odar taƙaita zirga-zirga a yankin Yankara kan iyakar…
Read More
Yanzu-yanzu: Gwamnati ta ƙara kuɗin wutar lantarki

Yanzu-yanzu: Gwamnati ta ƙara kuɗin wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta ba da umarnin gaggawa kan ƙarin kuɗin wutar lantarki daga ranar Laraba, 3 ga watan Afrilun da ake ciki. Mataimakin Shugaban hukumar NERC, Musiliu Oseni ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Laraba a Abuja. Oseni ya ce ƙarin ya shafi kashi 15 na adadin masu amfani da wutar lantarki ne wanda kuma su ne ke shan kashi 40 na wutar da ake samarwa baki ɗaya. Ko a watan Janairun da ya gabata, NERC ta ce gwamnatin Nijeriya za ta biya Naira tiriliyan 1.6 don tallafa wa…
Read More
‘Yan bindiga sun sace wasu masallata a Gusau

‘Yan bindiga sun sace wasu masallata a Gusau

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau ’Yan ta’addan masu tayar da ƙayar baya sun mamaye yankin Samaru da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, inda suka yi garkuwa da ɗimbin masu gudanar da ibadar Sallar Tahajjud da tsakar daren ranar Talata. Mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan bindigar sun kewaye masallatan da misalin ƙarfe 1:30 na daren yau Talata, inda suka far wa masu ibada a cikin masallacin tare da yin garkuwa da dama daga cikinsu. "Kamar yadda nake magana a yanzu, har yanzu ba mu kai ga tantance adadin waɗanda aka yi…
Read More
An gano gawar DCP a gidansa a Oyo

An gano gawar DCP a gidansa a Oyo

Daga BASHIR ISAH An gano Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda (DCP), Gbolahan Olugbemi, kwance a mace a gidansa da ke Ogbomosho, Jihar Oyo. MANHAJA ta tattaro Olugbemi, wanda ke aiki da rundunar 'yan sanda ta Jihar Legas, ya tafi gida ne don yin hutun Easter. An ce mutuwar jami'in cike take da mamaki da ruɗani wanda hakan ya jefa jami'an sashen bincike na FCID na Legas cikin halin jimami. Majiyarmu ta rawaito cewa, Kakakin FCID, ASP Aminat Mayegun, ta ce za su gudanar da cikakken bincike domin gano dalilin mutuwar jami'in. Majiya ta kusa da FCID ta ce za a gayyato…
Read More
Gobara ta ƙone shaguna da dama a Kwara

Gobara ta ƙone shaguna da dama a Kwara

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga Jihar Kwara sun ce shaguna da dama sun ƙone tare da asarar dukiya mai yawa sakamakon ƙobarar da ta auku a Kasuwar Owode da ke garin Offa a jihar. An ce gobarar ta fara ne da asubahin Talata wanda hakan ya yi sanadiyar ƙonewar wasu shaguna a kasuwar. Cikin wani faifan bidiyo na gobara wanda aka yaɗa an jiyo murya cikin harshen Yarabanci na cewa: “Wutar ta yi ƙarfi sosai, ba lantarki ya haifar da gobarar ba, wataƙila sakamakon girki da ake yi kusa da wurin ne." Bayanai sun daga bisani, Jami'an Kwana-kwana na ji…
Read More
Da Ɗumi:ɗumi: An rantsar da Bassirou Faye a matsayin sabon Shugaban Ƙasar Senegal

Da Ɗumi:ɗumi: An rantsar da Bassirou Faye a matsayin sabon Shugaban Ƙasar Senegal

*Ya zama Shugaban Ƙasa mafi ƙarancin shekaru a Afirka Daga BASHIR ISAH An rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa don ci gaba da jan ragamar mulkin ƙasar. Da wannan Faye mai shekara 44, ya zama shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru a nahiyar Afirka. Bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe babban zaɓen ƙasar, Faye ya sha alwashin yin sauye-sauye da dama a ɓangarori daban-daban na ƙasar. An rantsar da Faye ne a ranar Talata a birnin Diamniadio da ke kusa da Dakar babban birnin ƙasar.
Read More
Ba mu ci bashin N14.26bn ba — Gwamnatin Zamfara

Ba mu ci bashin N14.26bn ba — Gwamnatin Zamfara

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Dauda Lawal ta bayyana cewa, ba ta ci bashin Naira biliyan 14.26 ba, amma cewa abin da ake gani yanzu ɓangare ne na bashin biliyan N20 da gwamnatin da ta gabata ta ranto. Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya faɗa a sanar da ya fitar cewa babu wani bashi da jihar ta ci, a gida ko ƙetate, tun bayan da Gwamna Dauda Lawal ya karɓi ragamar mulkin jihar. Ya ce, “Za mu so mu yi ƙarin haske kan rahoton Ofishin Kula da Bashi (DMO), Jihar Zamfara ba ta ci bashin biliyan…
Read More