Labarai

Binciken tsaro ya bankaɗo shirin neman gwara kan Sanatocin Arewa da na ’yan ƙasa

Binciken tsaro ya bankaɗo shirin neman gwara kan Sanatocin Arewa da na ’yan ƙasa

Daga BASHIR ISAH Wasu jami’an hukumomin tattara bayana asirri na kasa sun bankado shirin da wasu makirai ke yi na neman gwara kan sanatocin Arewa a Majalisar Tarayya  da talakawansu. Jami’an wadanda suka bukaci a sakaya sunansu su shaida wa jaridar PRNigeria cewa har wa yau, shirin na da nufin gwara kan hukumomin tsaron kasar nan don su rika ganin laifin juna game da matsalar tsaron kasa. Sun bayyana hakan ne a matsayin martani a kan wani rahoto wanda ya yi zargin hukumomin tsaron sun kafa idanunsu kan wani Sanatan Arewa saboda zarginsa da ake yi da daukar nauyin ta’addanci,…
Read More
Tinubu ya isa Abuja bayan kammala ziyara a Faransa

Tinubu ya isa Abuja bayan kammala ziyara a Faransa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Bola Tinubu ya isa birnin tarayya, Abuja, bayan kammala ziyara a kasar Faransa domin gudanar da harkokinsa. Tinubu ya sauka filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ne da misalin karfe 8:50 na dare inda ya samu tarba daga tawagar gwamnati karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume. Haka nan, tawagar takunshi manyan jami'ai irin su Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila; Ministan Abuja, Nyesom Wike da sauransu. Tun a ranar Laraba ta makon jiya Tinubu ya bar Nijeriya zuwa Faransa, kuma wannan ita ce ziyararsa ta biyu a kasar tun…
Read More
Ƙasurgumin ɗan fashin dajin da ya addabi Birnin Gwari ya shiga hannu a hanyarsa ta zuwa kafa sansani a Kano

Ƙasurgumin ɗan fashin dajin da ya addabi Birnin Gwari ya shiga hannu a hanyarsa ta zuwa kafa sansani a Kano

Daga BASHIR ISAH Jami’an tsaro a Kano sun cika hannu da gawurtaccen dan fashin dajin nan da ya addabi yankin Birnin Gwari, Isah Lawal. Dan bindigar ya fada a komar ‘yan sandan ne bayan da ya shirya zuwa kafa sansani a Kano inda aka same shi dauke da shanu 55 da tumaki guda shida, kamar yadda Kakakin ‘Yan sandan Kano, ASP Abdullahi Haruna ya bayyana a ranar Litinin. ‘Yan sanda sun ce wanda ake zargin a baya mazaunin kauyen Kaya ne da ke yankin Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna. Jami’an sun ce dan fashin dajin ya yi ikirarin cewa…
Read More
EFCC ta tsare ƙanin Hadi Sirika kan binciken badaƙalar N8bn

EFCC ta tsare ƙanin Hadi Sirika kan binciken badaƙalar N8bn

Daga BASHIR ISAH Jami’an Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC) ta tsare Abubakar Ahmad Sirika, kani ga tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Abubakar Sirika. News Point Nigeria ta rawaito cewar, jami’an sun cika hannu da dan’uwan tsohon ministan ne a ranar Lahadi bayan da binciken da EFCC ke gudanarwa a Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ya biyo ta kansa. Ana zargin Sirika da tafka almundahanar da ta kai N8,069,176,864 a lokacin da yake rike da mukamin Minista. Hukumar ta ce kudaden na wasu kwangila ne guda hudu wanda Sirika ya bai wa wani kamfani mai suna Engirios Nigeria Limited mallakar kanin…
Read More
An cafke matar da ta sayar da yara sama da 42

An cafke matar da ta sayar da yara sama da 42

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wata ’yar shekara 45 mai suna Alimot Haruna mai fataucin kananan yara, ta bayyana cewa ta sayar da yara sama da 42 a cikin shekaru biyar da suka gabata. A ranar Laraba ne wata tawagar ’yan sanda daga ofishin ’yan sanda na Ijora Badia na rundunar ’yan sandan Legas ta cafke wadda ake zargin. An tattaro cewa wadda ake zargin wanda cibiyarta ke a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ta kasance cikin jerin sunayen ’yan sandan da ake nema ruwa a jallo kan irin wannan laifin. Wadda ake zargin a cikin sanarwar da ta yi na…
Read More
Mai gadin makaranta ya kashe kansa saboda tsohuwar matarsa ta auri wani

Mai gadin makaranta ya kashe kansa saboda tsohuwar matarsa ta auri wani

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani mai gadi a kwalejin Prestige International College, Nurudeen Shehu, mai shekaru 37, ya kashe kansa sakamakon labarin kara auren tsohuwar matarsa a Kano. Kwamishinan 'yan sandan jihar, Usaini Gumel, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a cikin daya daga cikin azuzuwan kwalejin a ranar Lahadi. Gumel ya ce, “A ranar 28 ga watan Janairu da misalin karfe 10:30 na safe, Abdullahi Abdulsalam na Rijiyar Zaki ya ruwaito cewa an samu Shehu a rataye ba motsi a cikin aji. “’Yan sanda daga sashin Gwale, karkashin jagorancin DPO,…
Read More
Abin da ya faru a Minna aikin ɓata-gari ne ba zanga-zangar tsadar rayuwa ba – Gwamna Bago

Abin da ya faru a Minna aikin ɓata-gari ne ba zanga-zangar tsadar rayuwa ba – Gwamna Bago

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya ce dandazon jama'a da aka gani a kan hanya a wasu titunan garin Minna a ranar Litinin, ba zanga-zangar tsafar rayuwa ba ne face ayyukan wasu ɓata-gari ne masu neman daburta zaman lumanar al'umma. Ya ce wasu bata-gari ne suka shirya dandanzon don samun danar wawure kayan abincin da wata mota ke da su wadda ke kan hanyar shigowa gari daga hanyar Bida. Gwamnan ya kara da cewa, "Yanzun haka mun kama wasu daga cikin bata-garin kuma za mu ci gaba da daukar matakin ganin ba mu bari an kawo…
Read More
‘Yan sanda sun tabbatar da sace ‘yan rakiyar A’amarya 35 a Katsina

‘Yan sanda sun tabbatar da sace ‘yan rakiyar A’amarya 35 a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wata dabar 'yan bindiga ta sace mata 35 a lokacin da suke dawowa daga rakiyar amarya a karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina da misalin karfe 8: 30 na daren ranar Alhamis. Amma sai a wannan Litinin labarin ya yadu bayan da hukumomi suka ziyarci kauyen. 'Yan bindigar sun yi wa motar 'yan kai amaryar dirar mikiya inda suka harbi direman motar wanda yanzu haka yana kwance yana karbar magani. Kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Abubakar Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewar wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun…
Read More
Ƙananan asibitoci masu zaman kansu na buƙatar tallafi – Gabare Clinic

Ƙananan asibitoci masu zaman kansu na buƙatar tallafi – Gabare Clinic

Daga ABDULLAHI Sani Doguwa a Kano An buƙaci masu hali da ke cikin alumar musulmi a ko'ina da su rinka tallafa wa kananan asibitoci masu zaman kansu da gudunmawar da ta dace, musamman asibitochin da ke duba larurar iyaye mata masu dauke da juna biyu, ko dai sauran alumma da suke da larurori daban-daban, duba da halin da alumma ke ciki na matsin tsadar rayu. Mukaddashin babban daraktan lura da masu dauke da lafiyar iyali na asibitin Gabare Clinic & Maternity dake Sumaila, da ya bukaci a sakaye sunansa, shi ne ya yi wannan kira yayin ganawarsa da manema labarai.…
Read More
Tsadar rayuwa ta haifar da zanga-zanga a Neja

Tsadar rayuwa ta haifar da zanga-zanga a Neja

Daga BASHIR ISAH Al'ummar garin Minna, babban birnin Jihar Neja, sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin dadinsu dangane da tsadar rayuwar da ake ci gaba da fuskanta a Nijeriya. An ga masu zanga-zangar a ranar Litinin sun mamaye wasu manyan hanyoyin garin wanda hakan ya haifar da tsaikon zirga-zirgar abubuwan hawa. MANHAJA ta kalato cewar, mazauna yinkin Kpakungu da ke Minna sun yi cincirindo a kan hanya daidai randabawul da ke yankin inda suka hana masu abubuwa hawa shiga da fita. Bayanai sun ce jama'ar sun bukaci 'yan sandan da suka bayyana a wurin don kula da…
Read More