03
Feb
Daga BASHIR ISAH Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta bayyana adadin kudin da maniyyata za su biya domin aikin Hajjn 2024. Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Asabar ta bakin mai magana da yawunta, Fatima Sanda Usara, NAHCON ta ce game da Hajjin bana maniyyata daga Kudancin Nijeriya za su biya Miliyan N4,899,000, yayin da maniyyata daga Arewacin kasa za su biya Miliyan N4,699,000. Sanarwar ta kara da cewa, maniyyata daga Yola da Maiduguri Naira Miliyan 4,679,000 ne za su biya a matsayin kudin Hajjin 2024. Kafin wannan lokaci, Shugaban NAHCON na Kasa, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya yi…
