Labarai

Matsin Rayuwa: Ku ƙara haƙuri da gwamnatin Tinubu, sauƙi na tafe – kiran Idris ga ‘yan Nijeriya

Matsin Rayuwa: Ku ƙara haƙuri da gwamnatin Tinubu, sauƙi na tafe – kiran Idris ga ‘yan Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga 'yan Nijeriya da su kara hakuri da gwamnatin Shugaba Tinubu bisa sauye-sauyen da take yi don cigaban kasa. Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ne ya yi wannan kira, inda ya ce watannin da Tinubu ya yi a ofis ba su taka kara sun karya ba balle a rika kukan rashin gani a kasa. Tun bayan da ya kama mulkin kasa a watan Mayun da ya gabata, Tinubu ya dauki wasu matakai ciki har da cire tallafin mai lamarin da ya jefa kasa cikin halin tsadar rayuwa. Sai…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Babbar Kotu ta hana ci gaba da sauraren ƙarar da aka shigar kan mawaƙi Rarara bisa zargin sukar Buhari

Da Ɗumi-ɗumi: Babbar Kotu ta hana ci gaba da sauraren ƙarar da aka shigar kan mawaƙi Rarara bisa zargin sukar Buhari

Daga BASHIR ISAH Wata Babbar Kotun Jihar Nasarawa da ke zamanta a yankin Doma ta dakatar da Kotun Majastare ta 1 da ke Lafia daga ci gaba da sauraren ƙarar da wani matashi mai suna Sani Ahmad Zangina ya shigar kan fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Abdullahi Kahutu Rarara, bisa zarginsa da sukar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari. Lauyan da ke jagorantar tawagar lauyoyin Rarara, Barrister A. I Ma'aji, ya bayyana wa manema labarai cewar sun ɗaukaka ƙara a gaban Mai Shari'a Abdullahi H. Shamsu Shama na Babbar Kotu da ke Doma tun ranar Litinin ta ƙarshen watan jiya, bisa rashin…
Read More
Saudiyya ta yi wa Nijeriya ragin kudin aikin Hajjin 2024

Saudiyya ta yi wa Nijeriya ragin kudin aikin Hajjin 2024

Daga BASHIR ISAH Hukumar Alhazan ta Kasa (NAHCON) ta sanar da cewa Saudiyya ta yi wa Nijeriya ragin kudin aikin Hajjin bana don samun saukin wadanda za su tafi aikin Hajjin bana daga kasar. NAHCON ta ce shugabanta, Jalal Ahmad Arabi ne ya mika bukatar neman ragin domin walwalar mahajjatan Nijeriya. Bayanin haka na kunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun NACHON, Fatima Sanda Usara, ta fita a ranar Laraba, inda ta ce ragin ya shafin kudin tikitin jirgi, masauki, jigila da sauran hidimomin da ake yi wa alhazai yayin aikin Hajji a Saudiyya. Sanarwar ta ce biyo…
Read More
Rubutu makami ne mai dafi da za a iya sokar ahalin marubuci da shi – Faisal Hunkuyi

Rubutu makami ne mai dafi da za a iya sokar ahalin marubuci da shi – Faisal Hunkuyi

"Marubuci madubi ne mai ɗauke da majigin nazarto gaba da baya" Daga AISHA ASAS Shafin Adabi na wannan mako ya sakulo wa masu karatunmu daya daga cikin jajirtattun matasan da ke yi wa adabi hidima. Kokarin sa da nacewa wurin ganin ya kwankwade duk wani kalubale da ya yi tuntube da shi a hanyar sa ta zama marubuci abin a yaba masa ne. Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Faisal Haruna Hunkuyi; MANHAJA: Za mu so ka fara da bayyana kanka ga masu karatunmu. FAISAL HUNKUYI: Sunana Faisal Haruna Hunkuyi. An haife ni a cikin garin Hunkuyi da…
Read More
Ta yi yunƙurin sayar da ‘ya’yanta biyu kan N2m saboda tsadar rayuwa

Ta yi yunƙurin sayar da ‘ya’yanta biyu kan N2m saboda tsadar rayuwa

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Anambra ta cafke wata mata a jihar wadda ta yi yunkurin siyar da wasu ‘ya’yanta biyu maza daga cikin ‘ya’ya 11 da take da su. Chinyere Chukwu wadda ‘yar asalin yankin Karamar Hukumar Ihiala ce a jihar, ta fada a komar hukuma ne ta hannun Ma’aikatar Harkokin Mata da Walwala ta Jihar. Bayanai sun ce matar ta hada baki ne da daya daga cikin ‘ya’yanta mata mai shekara 17 a kan su siyar da biyu daga cikin ‘ya’yan  “saboda tsadar rayuwar da ake fama da ita a kasa.” Chukwu ta shaida wa hukuma cewa, ta…
Read More
MOPPAN ta naɗa Habibu Barde Shugaban Riƙo na Ƙasa

MOPPAN ta naɗa Habibu Barde Shugaban Riƙo na Ƙasa

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta nada Mataimakin Shugaba na Shuyyar Arewa ta Tsaki, Malam Habibu Barde, a matsayin shugaban riko na kasa na kungiya. Sanarwar nadin na kunshe ne cikin sanarwar manema labaran da Kwamitin Amintattu na kungiyar ya fitar a ranar Laraba mai dauke da sa hannun shugabansa, Makama Sani Mu'azu. Sanarwar ta kuma nuna cewa nadin Barde a matsayin Shugaban riko na kungiyar ya fara aiki ne nan take. A cewar danarwar, "Nadin ya biyo bayan ajiye mukaminsa da Dr. Ahmad Sarari ya yi ne a matsayin Shugaban Kungiyar." Keamitin ya nuna…
Read More
EFCC ta bankaɗo ƙungiyar addini tana samo kuɗin ɗaukar nauyin ta’addanci

EFCC ta bankaɗo ƙungiyar addini tana samo kuɗin ɗaukar nauyin ta’addanci

Daga BASHIR ISAH Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta bankado yadda wata kungiyar addini a Nijeriya ke tafka almudahana don daukar nauyin ta'addanci. Kazalika ya bayyana yadda suka sake gano wata kungiyar addini da ke ba da kariya ga wani mai karkatar da kudade bayan gano wasu kudade a asusun kungiyar da ake zargin na sata ne. Shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne a ranar Larabar a cibiyar Musa Yar’Adua da ke Abuja, yayin wata tattaunawa ta yini daya kan “Matasa, Addini da Yaki da Rashawa.” A cewar Olukoyede, EFCC ta yi…
Read More
Gwamna Fintiri ya yi nasara a Kotun Ƙoli

Gwamna Fintiri ya yi nasara a Kotun Ƙoli

Daga BASHIR ISAH Kotun Ƙoli mai zamanta a Abuja, ta tabbatar da Ahmadu Fintiri a matsayin zababben Gwamnan Jihar of Adamawa. Cikin hukuncin da ya karanto tayin zaman Kotun a ranar Laraba, John Okoro, ya yi watsi da karar da 'yar takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar, Aisha Dahiru, ta daukaka a kan Fintiri saboda rashin cancanta. Kotun ta ce halin da Kwamishinan Zaben jihar, Hudu Ari, ya nuna hali me na rashin kan gado laifi babba. Mai Shari'a Okoro ya kara da cewa, baturen zabe ne kadai doka rmta bai wa ikon sanar da sakamakon zabe domin kauce…
Read More
Majalisar Dokokin Jihar Ogun ta yi sabon shugaba

Majalisar Dokokin Jihar Ogun ta yi sabon shugaba

Daga BASHIR ISAH A ranar Talata aka rantsar da Hon. Oludaisi Elemide a matsayin sabon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ogun inda ya maye gurbin Olakunle Oluomo wanda ska tsige shi a matsayin kakin majalisar makon jiya. Yayin zaman majalisar karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar, Bolanle Ajayi wanda ya samu halarcin mambobi 22, Hon. Musefiu Lamidi ya karanto rahoton kwamitin da majalisar ta kafa don binke kan zarge-zargen da ake yi wa Oluomo. Rahoton Kwamitin ya ce rashin da'ar da tsohon Kakakin ya nuna wa Kwamitin a lokacin gudanar da bincikensa rashin martabaws ne ga Kwamitin da ma Majalisar baki daya.…
Read More
Majalisar Dattawa ta buƙaci zama da shugabannin tsaro kan tabarɓarewar tsaron ƙasa

Majalisar Dattawa ta buƙaci zama da shugabannin tsaro kan tabarɓarewar tsaron ƙasa

Daga BASHIR ISAH Majalisar Dattawa ta gayyaci shugabannin tsaro domin su zo a zauna don tattauna matsalar tsaron da ke kara kamari a kasa. Sai dai, Majlisar ba ta ayyana takamammiyar ranar da jami'an za su bayyana a gabanta ba. Majalisar ta gayyaci shugabannin tsaron ne bayan tattaunawar sirrin da mambobinta suka yi na sama da sa'o'i uku a ranar Talata, inda suka nuna damuwarsu kan yadda ake samun karuwar sace-sacen mutane da kisa da sauran manyan laifuka. Jagogaran Majlisar, Michael Bamidele Opeyemi, ya bayyana cewa baki daya sanatocin su 109 kowannensu ya gabatar da kudurin doka kan matsalar tsaro…
Read More