Labarai

Kotu ta ayyana Kasafin 2024 na Jihar Ribas haramtacce

Kotu ta ayyana Kasafin 2024 na Jihar Ribas haramtacce

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta  bayyana kasafin 2024 na Jihar Ribas a matsayin mara inganci kuma haramtacce. Kotun ta haramta kasafin ne a zaman shari’ar da ta yi a ranar Litinin karkashun jagorancin Mai Shari’a James Omotosho. A cewar Kotun, kasafin ya zama haramtacce ne saboda rashin ingancinsa da kuma saba tsari da aka yi kafin gabatar da shi a gaban Majalisar Dokokin Jihar. Kotun, wadda ta ayyana Martin Amaewhule a matsayin halastaccen Shugaban Majalisar, ta kama Gwamna Fubara da laifin yi wa Majalisar Dokoki na jihar katsalandan cikin harkokinta. Alkali Omotosho ya ce Gwamnan jihar ba shi da…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta sahale wa kamfanoni bakwai da su rarraba man Ɗangote

Gwamnatin Tarayya ta sahale wa kamfanoni bakwai da su rarraba man Ɗangote

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai manyan kamfanonin dillancin mai guda bakwai da muke da su a Nijeriya sun yi rajista tare da kamfanin tace man Dangote domin rarraba tataccen mai ta hanyar sara da sarar da shi. Wato dai man fetur din da matatar Dangoten wacce aka gina ta a kan Naira biliyan 20 ta samar. A ranar Lahadin da ta gabata ne dai su wadannan kamfannin dillancin a qarqashin shugabancin Kungiyar Manyan dillalan Man feturta Nijeriya (MOMAN) ita ce ta tabbatar da cewa,  bayan yin rajistar tasu, za su iya cigaba da rarraba man fetur din…
Read More
An damƙe ɗaya daga cikin masu garkuwa da suka addabi Abuja

An damƙe ɗaya daga cikin masu garkuwa da suka addabi Abuja

Rundunar ‘Yan Sandan Birnin Tarayya (FCT) ta tabbatar da cafke wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane, Chinaza Phillip, wanda ake zargin yana daya daga cikin batagarin da suka addabi yankin Abuja da sace-sacen mutane. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta ce sun kama wanda ake zargin ne a  ranar Alhamis a Jihar Kaduna. Ta kara da cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata aka mika wa rundunar Chinaza Phillip wanda a halin yanzu ake ci gaba da tsare shi. Cikin sanarwar da ta fitar, rundunar ta ce, “Rundunar ‘Yan Sandan FCT na sanar da cewa, jami’an ‘yansanda a jihar Kaduna…
Read More
‘Yan gida ɗaya da aka yi garkuwa da su a Abuja sun shaƙi iskar ‘yanci

‘Yan gida ɗaya da aka yi garkuwa da su a Abuja sun shaƙi iskar ‘yanci

‘Yan matan nan ‘yan gida daya da aka yi garkuwa da su tare da mahaifinsu a yankin Abuja, sun shaki iskar ‘yanci. A farkon watan Janairun da ake ciki ne ‘yan fashin dajin suka yi garkuwa da wadanda lamarin ya shafa, inda sakamakon jinkirin da aka yi wajen biyan kudin fansar da ‘yan bindigar suka nema, daya daga cikin yaran mai suna Nabeeha ta rasa ranta. A karshen mako ne aka ga isowar ‘yan matan gidansu da ke Abuja bayan da aka ceto su daga hannun ‘yan bindigar. Bayanai sun ce yaran sun koma gida ne bisa rakiyar jami’an tsaro…
Read More
Matsalar tsaro da tattalin arzikin Dala Tiriliyan 1

Matsalar tsaro da tattalin arzikin Dala Tiriliyan 1

Manufar Gwamnatin Tarayya na samar da Dala Tiriliyan 1 na tattalin arzikin kasa ba zai yiwu ba idan har aka cigaba da samun tabarbarewar matsalar rashin tsaro a kasar. Mafita ita ce jami’an tsaro su gaggauta daukar mataki tare da tabbatar da cewa an fatattaki ’yan bindiga da sauran miyagun da ke ta’addanci a kasar. Shugaba Bola Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga hafsoshin tsaro da shugabannin hukumomin leken asiri a wani taron tsaro da shugaban kasa ya gudanar kwanan nan a fadar shugaban kasa da ke Abuja. A cewar shugaban, yayin da ake samun…
Read More
Ba zan taɓa cin amanar Kwankwaso ba – Abba Gida-gida

Ba zan taɓa cin amanar Kwankwaso ba – Abba Gida-gida

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa ba zai taba cin amanar mai gidansa kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ba. Da ya ke jawabi ga magoya baya a Abuja, jim kadan bayan yanke hukuncin Kotun Koli da ta tabbatar masa da zabensa, Gwamna Yusuf ya nuna godiya ga Kwankwaso bisa kwazonsa na ganin cewa ba a zalunci al’ummar Kano ba. A cewar Gwamna Yusuf, “mu na godiya ga Allah da wannan gagarumar nasara da ya ba mu. Mu na kuma godiya ga jagoranmu, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa…
Read More
An cafke limami da wasu dauke da sassan jikin mutum a Legas

An cafke limami da wasu dauke da sassan jikin mutum a Legas

An cafke wani limami tare da wasu mutun hudu da ake zargin matsafa ne dauke da sassan jikin mutum a jihar Legas. An gano su ne dauke da kwarangwal na kan mutum da kuma wasu sassan jiki. Majiyarmu ta ce mazauna yankin Adamo a Ikorodu ne suka gano wadanda lamarin ya shafa kafin daga bisani aka mika su ga 'yansandan yankin. Majiyar ta kara da cewa, limamin da aka kama din ya bayyana wa 'yansanda cewa wani maigidansa yake yi wa aiki. A cewar mazauna yankin da lamarin ya faru, a ranar Alhamis da ta gabata ne 'yansanda sashen yaki…
Read More
Abba na buƙatar addu’ar sauke nauyin al’ummar Kano – Dr. Salihun-nur Adam

Abba na buƙatar addu’ar sauke nauyin al’ummar Kano – Dr. Salihun-nur Adam

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano An bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, yana buqatar addu'ar milyoyin al'ummar Kano don ya samu damar sauke nauyin shugabancin da ya rataya a wuyansa. A ranar Juma'ar makon jiya ne dai Kotun Ƙoli ta tabbatar wa Abba Kabir Yusuf da sahihancin nasararsa a zaben gwamnan Kano da aka yi a 2023. Wannan bayani ya fito ne daga bakin Dakta Salihun-nur Adam wanda aka fi sani da Salihanur Shugaban Cibiyar Bincike akan Ganyayyaki da sauyoyi da tsire-tsire domin maganin cututukan da ke damun dan Adam dake Kano. Haka kuma ya bayyana cewa,…
Read More
 Alhaji Ƙarami da ASUSS sun jagoranci ƙaddamar da littafin tarihin Fadar Bege da Hafiz Abdallah

 Alhaji Ƙarami da ASUSS sun jagoranci ƙaddamar da littafin tarihin Fadar Bege da Hafiz Abdallah

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Alhaji Ƙarami Isyaka Rabiu da ASUSS sun jagoranci kaddamar da littafin tarihin shahararrun sha’iri na Manzon Allah da sahabban sa da Ahalinsa wato Marigayi Abdulaziz Fadar Bege bayan rasuwar fadar bege shekaru 10 da suka wuce. Littafan biyu wanda fitaccen marubuci Malam Bilyaminu Abul-warakat Ayagi, wanda ya rubuta litattafai sama da 100 wanda kuma shi  ne ya rubuta litafin tarihin Marigayi Fadar Bege da kuma na sha’irin mawakin Manzon Allah wato Ambasada Dakta Hafizu Abdullah wanda Alhaji Karami Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu ya kaddamar da sayen litattafan hudu akan Naira miliyan biyu domin qarfafa gwiwa…
Read More
Wike ya ɗora alhakin yajin aikin malaman Abuja kan shugabannin ƙananan hukumomi

Wike ya ɗora alhakin yajin aikin malaman Abuja kan shugabannin ƙananan hukumomi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya zargi shugabannin kananan hukumomin shida da laifin yajin aikin da malaman makarantun firamare ke cigaba da yi a yankin. Wike, wanda ya yi wa ’yan jarida jawabi a ranar Talata a Abuja jim kadan kafin wani taron gaggawa da hukumomin tsaro, ya ce jami’an kananan hukumomin ba su cika aikin da aka dora musu ba. A ranar Lahadin da ta gabata ne Kungiyar Malamai ta babban birnin tarayya Abuja ta umurci malaman firamare da su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar 15 ga watan Janairu. Yajin aikin…
Read More