Labarai

Ɗan APC da ɗan PDP Ɗanjuma da Ɗanjummai ne – Sule Lamiɗo

Ɗan APC da ɗan PDP Ɗanjuma da Ɗanjummai ne – Sule Lamiɗo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a Jam'iyyar PDP ya ce zargin da tsohon shugaban rikon kwarya na jam'iyyar APC Chief Bisi Akande ya yi cewa idan PDP ta dawo mulki 'yan Nijeriya za su sake shiga qunci ba gaskiya ba ne. Alhaji Sule Lamido ya ce duk dan APCn da yake ganin PDP ce ta lalata Nijeriya to da shi a ciki, kasancewar shi ma asali dan PDP ne. Sule Lamido ya ce ya yi mamakin kalaman Bisi Akande kan cewa PDP musiba ce, annobar bala'i ce azaba ce, amma duk da hakan…
Read More
Daina biyan kuɗin fansa shi zai kawo ƙarshen garkuwa da mutane — Ministan Tsaro

Daina biyan kuɗin fansa shi zai kawo ƙarshen garkuwa da mutane — Ministan Tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan tsaron Nijeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya ce lokaci ya yi da za a daina biyan kudin kansa saboda haka ne kadai hanyar kawo karshen masu garkuwa da mutane. Ministan ya bayyana haka ne a taron majalisar zartaswa ta kasa da aka gudanar a ranar Laraba. Ya ce Shugaban Kasa ya bai wa dukkan hafsoshin tsaro goyon baya da ta kamata don ganin an kawo karshen garkuwa da mutane da ya yi kamari a kasar. Ministan tsaron ya ce dokar Nijeriya ta hana bayar da kudin fansa kuma bai kamata mutane su rika biyan…
Read More
CBN ya mayar da manyan sassansa zuwa jihar Legas

CBN ya mayar da manyan sassansa zuwa jihar Legas

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya shiraya don mayar da manyan sassansa zuwa jihar Legas. Wannan jawabi yana ƙunshe ne a cikin wata takardar yarjejeniyar cikin gida wacce aka ba wa majiyarmu damar samu. Wannan yunkuri a cewar wani jami’in CBN ɗin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa, an yi ne domin a rage cinkoso a babbar shalkwatar bankin da ke Abuja. Kodayake wasu daga cikin ma’aikatan na CBN ɗin sun yi tirjiya a kan komawa legas ɗin saboda suna ganin cewa wannan lamari an yi shi ne saboda qabilanci zalla ba don wani…
Read More
Ba zan yarda da cin hanci da rashawa a gwamnatina ba – gargaɗin Gwamnan Zamfara ga ma’aikatansa

Ba zan yarda da cin hanci da rashawa a gwamnatina ba – gargaɗin Gwamnan Zamfara ga ma’aikatansa

Daga MAHDI M. MUHHAMMAD Gwamna Dauda Lawal ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da duk wani nau'i na cin hanci da rashawa ko rashin tausayi daga mambobin majalisarsa ko ma'aikatan gwamnati a jihar Zamfara ba. A ranar Alhamis ne gwamnan ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa na musamman a zauren majalisar a gidan gwamnati da ke Gusau. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce majalisar ta kasance taron zartarwa na farko na gwamnatin Zamfara a shekarar 2024. Ya qara da cewa, Gwamna Dauda Lawal ya bukaci dukkan masu rike da manyan…
Read More
Tinubu ya gana da Majalisar Koli ta Shari’ah bisa nadama takarar Musulmi da Musulmi

Tinubu ya gana da Majalisar Koli ta Shari’ah bisa nadama takarar Musulmi da Musulmi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da ’Yan Majalisar Koli ta Shari’a a Nijeriya a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Ganawar da aka yi tsakanin shugaban kasar da majalisar na zuwa ne kimanin sa’o’i 48 bayan shugaban majalisar, Sheikh Abdur-Rasheed Hadiyyatullah, ya nuna nadamar goyon bayan takarar mabiya addinin faya da Tinubu da Shettima a bara. A ranar Talata, Sheikh Hadiyyatullah, a wata hira da manema labarai a Abuja, ya haifar da sabon cece-kuce kan tsayawa takarar jam’iyyar APC Musulmi da Musulmi a zaben 2023, wanda a cewarsa, ya gaza yadda ake tsammani. Ya…
Read More
Tinubu ya yi ganawar sirri da Ganduje da jiga-jigan APC na Kano

Tinubu ya yi ganawar sirri da Ganduje da jiga-jigan APC na Kano

Saga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi ganawar sirri da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje. Ganduje ya jagoranci wata tawaga da ta kunshi shugabannin jam’iyyar APC reshen Jihar Kano domin ganawa da Tinubu a fadar shugaban qasa ta Aso Rock Villa da ke Abuja, ranar Alhamis. Taron na ranar Alhamis ya zo ne mako guda bayan da Kotun Koli ta yanke hukuncin amincewa da Abba Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin halastaccen zababben gwamnan jihar da korar karar dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna. A watan Maris din da ya gabata ne dai mulki ya…
Read More
Gwamna Inuwa ya kai labari a Kotun Ƙoli

Gwamna Inuwa ya kai labari a Kotun Ƙoli

Daga BASHIR ISAH Kotun Ƙoli a ranar Juma'a ta tabbatar wa Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, nasarar da ya samu a zaben 2023. Kotun ta yanke hukuncin haka ne bayan da ta yi watsi da karar da dan takarar jam'iyyar PDP a zaben na ran 18 ga Maris, 2023, Mohammed Barde ya daukaka inda yake kalubalantar nasarar da Inuwa ya samu. Barde ya daukaka kara ne kan cewa zaben da ya bai wa inuwa nasara cike yake sa badakalar sayen kuri'u. Sai dai baki daya shari'o'in da aka yi kan zaben a kotuna matakai uku, sun tabbatar da Inuwa a…
Read More
Ibadan: Waɗanda suka mutu sun ƙaru zuwa biyar

Ibadan: Waɗanda suka mutu sun ƙaru zuwa biyar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Adadin wadanda suka mutu sakamakon fashewar wani abu da ya afku a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a ranar Talata, 16 ga watan Janairu, ya kai mutum biyar. A ranar Laraba da daddare, gwamnan jihar, Seyi Makinde, yayin da yake bayar da karin haske a gidan talabijin na Channels Television a wani shirin siyasa mai taken "Politics Today", ya ce an samu mutuwar mutane biyu a ranar Talata, inda ya qara da cewa wani wanda abin ya shafa ya mutu a asibiti ranar Laraba. Sai dai a wani sabon rahoto da aka fitar a…
Read More