Labarai

Tsaro: Gwamnan Zamfara ya haramta wa sarakunan gargajiya bada izinin haƙar ma’adina

Tsaro: Gwamnan Zamfara ya haramta wa sarakunan gargajiya bada izinin haƙar ma’adina

Daga BASHIR ISAH A matsayin mataki na ci gaba da yaki da matsalar tsaro a Jihar Zamfara, Gwamnan Jihar, Dauda Lawal, ya rattaba hannu kan dokar da ta haramta wa sarakunan gargajiya a fadin jihar bai wa masu hakar ma'adinai izinin gudanar da harkokinsu a jihar. Lawal ya ba da wannan umarnin ne yayin taron Majalisar Zartarwa na Jihar da ya gudana a Fadar Gwamnatin Jihar a ranar Alhamis. Mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar ran Alhamis cewa, an ba da wannan umarni ne domin dakile matsalar 'yan fashin dajin…
Read More
Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci ta ƙara jaddada goyon bayanta ga Shugaba Tinubu

Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci ta ƙara jaddada goyon bayanta ga Shugaba Tinubu

Majalisar Kolin ta ce ta sami kwarin gwiwar jaddada goyon bayan nata ga Shugaban Kasa Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ne biyo bayan hukuncin da Kotun Kolin ta Nijeriya ta yanke kan raba gardamar zabe inda kotun ta tabbatar da Shugaba Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben na shekarar 2023. Majalisar ta ce hukuncin ya kara tabbatar da cewa zaben da majalisar ta yi ba na tumun-dare ba ne don ya dace da zabin 'yan kasa. A cikin wata sanarwa da Majalisar ta fitar a wajen taronta na kasa na yini biyu da aka gudanar a…
Read More
An kama ɗalibin Jami’ar Bauchi ya mallaki bindiga ba bisa ƙa’ida ba

An kama ɗalibin Jami’ar Bauchi ya mallaki bindiga ba bisa ƙa’ida ba

Daga BASHIR ISAH Jami'an tsaro a jihar Bauchi sun kama wani dalibin Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa University (ATBU) Bauchi bisa zargin mallakar bindiga ba bisa ka'ida ba. Kakakin Rundunar 'Yansandan Bauchi, Ahmed Wakil, ya bayyana a ranar Laraba cewa, an tsare dalibin ne a ranar Asabar da ta gabata bayan da 'yan bijilanti suka kwarmata musu cewa dalibin ya mallaki karamar bindiga kirar gida har da alburushi. Ya ce tuni dalibin wanda dan aji hudu ne a ATBU ya amsa laifin da ake zarginsa. Ya kara da cewa, wanda ake zargi ya yi ikirarin asali bindigar ta wani ce wanda…
Read More
Yadda ‘yan ta’adda suka kai hari a sansanin sojoji a Katsina

Yadda ‘yan ta’adda suka kai hari a sansanin sojoji a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Barayin daji fiye da mutum 100 kan babura dauke da muggan makamai sun kai hari a sansanin jami'an tsaro da ya kunshi sojoji da 'yan sanda, a sansanin dake garin Nahuta a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina. Majiyar Manhaja ta bayyana cewar, sojojin sun mayar da martani ta hanyar bude wa 'yan bindigar wuta amma barayin sun fi su yawa sun kuma shammace su lamarin da ya tilasta jam'in tsaron janye. Bayan shafe kimanin sa'o'i biyu da rabi bangarorin biyu na dauki ba dadi, barayin sun samu nasarar kone Kayayyakin hansanin jami'an tsaron da…
Read More
Kano ta ware N8bn don gina makarantun firamare na musamman guda uku

Kano ta ware N8bn don gina makarantun firamare na musamman guda uku

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin jihar Kano ta ware Naira biliyan 8 domin gina manyan makarantun firamare guda uku a fadin jihar. A cewar Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf, makarantun za su kasance da cikakkun kayan aikin koyarwa, za kuma a samar da isasshen yanayi ga yaran da suka fito daga iyayen marasa galihu domin samun ingantaccen ilimi duka dai don samun ci gaba a nan gaba. Gwamnan ya ce za a kafa makarantun ne a kowace mazabar majalisar dattawa da kayayyakin koyo na zamani don samar da ingantaccen ilimi a matakin farko. Ya kuma ce an ware Naira…
Read More
Iftila’in Oyo: Dole a binciko masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba don fuskantar hukunci – Tinubu

Iftila’in Oyo: Dole a binciko masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba don fuskantar hukunci – Tinubu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ce dole ne a binciko tare da hukunta masu harkar haƙar ma'adinai ta haramtacciyar hanyar da suka yi sanadiyar aukuwar fashewa mai karfi a Ibadan, Jihar Oyo. MANHAJA ta ruwaito Tinubu ya bayyana haka ne cikin sanarwar da ya fitar ranar Laraba ta hannun kakakinsa, Ajuri Ngelale. Sanarwar ta ce “Abin damuwa ne ainun jin cewa aukuwar fashewar na da nasaba da ayyukan masu hakar ma'adina ba bisa ka'ida ba. "Dole a binciko masu hannun cikin wannan halin gangancin da ya haifar da wannan mummunan al'amari don su fuskanci hukunci." Shugaban Kasar…
Read More
Babbar mota ta markaɗe wata mata a yankin Abuja

Babbar mota ta markaɗe wata mata a yankin Abuja

Daga BASHIR ISAH Wata tipa makare da yashi ta markade wata mata a cikin motarta a hanyar zuwa filin jirgin sama a yankin Lugbe, Abuja. Binciken MANHAJA ya gano wannan mummunan al’amari ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata biyo bayan akasin burki da motar ta fuskanta. Hatarin ya haifar da tsaiko na wani lokaci a hanyar wanda hakan ya haifar da samun jerin gwanon motoci masu zaman jira a bude hanya. Wani faifan bidiyon hatsarin da aka yada ya nuna yadda yashin da tipar ta dauko ya zuba a kan karamar motar da aka markade wanda jama’a…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Sakkwato

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan zaɓen gwamnan Sakkwato

Kotun Koli da ke Abuja, ta kebe yanke hukunci kan karar da jam'iyyar PDP da dan takararta, Saidu Umar, suka daukaka na kalubalantar nasarar da Gwamna Ahmad Aliyu ya samu a matsayin zababben gwamnan jihar a zaben 2023. Kwamitin akalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun, ya dauki wannan mataki ne yayin zaman shsari'ar da ya yi a ranar Laraba. Kotun ta dage yanke hukunci kan shari'ar ne zuwa wani lokaci wanda ba ta ayyana ba. Kuma ta yi hakan ne bayan da ta karbi bayanai daga lauyoyin bangarorin da shari'ar ta shafa.
Read More

An samu aukuwar gobara a Kasuwar Panteka a Kaduna

Daga BASHIR ISAH Da safiyar wanna Laraba aks samu aukuwar gobara a fitacciyar kasuwar nan ta Panteka da ke Kaduna. Wani ganau mai suna Malam Isiyaku, ya ce gobara ta fara ne da misalin karfe na dare 12. Ya kara da cewa, ya zuwa lokacin da aka nemi jin ta bakinsa ba a kai ga gano dalilin aukuwar gobarar ba. MANHAJA ta tattaro cewa, gobarar ta kone shaguna masu yawa wanda hakan ya haifar da asarar dimbin dukiya. Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomi a jihar ba su ce uffan ban kan iftila'in gobarar. Ga wani bangare na bidiyon…
Read More