Labarai

Ministan Abuja ya kira taron gaggawa kan matsalar tsaro

Ministan Abuja ya kira taron gaggawa kan matsalar tsaro

Daga BASHIR ISAH Ministan Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya kira taron gaggawa a ranar Talata kan matsalar tsaron da ke addabar babban birnin kasa. Ministan ya bayyana haka ne sa'ilin da yake jawabi a wajen wani taro a Abuja, inda ya bai wa mazauna yankin tabbacin ba su kariya yadda ya kamata. Ya kara da cewa gwamnati na yin mai yiwuwa wajen karfafa wa hukumomin tsaro ta hanyar samar musu da dukkan abubuwan da suke bukata don dakile matsalar tsaro a fadin birnin. MANHAJA ta kalato cewa, wadan suka halarci taron gaggawar sun hada da shugabannin hukumomin tsaro na…
Read More
Jama’a sun shiga firgici sakamakon fashewa mai karfi da ta auku a Ibadan

Jama’a sun shiga firgici sakamakon fashewa mai karfi da ta auku a Ibadan

Daga BASHIR ISAH Al'umma mazauna Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun shiga firgici da tashin hankali biyo bayan fashewa mai karfi da ta auku da yammacin Talata a birnin. Mazauna yankunan Awolowo, Bodija, Akobo da sauransu sun ce, hatta gidaje da wasu motocin da ke kusa sai da suka amsa sakamakon karfin fashewar. A wani sako da ta wallaffa a shafinta na X, Gwamnatin Jihar Oyo ta ce ta samu rahoton fashewar da ta auku. “Ana kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu kasancewar hukumomin tsaro sun sunkuya bincike domin gano musababbin fashewar," in ji Gwamnatin Jihar. Jaridar…
Read More
An gano gawarwaki biyar a hatsarin jirgin ruwan da ya auku a Neja

An gano gawarwaki biyar a hatsarin jirgin ruwan da ya auku a Neja

Daga BASHIR ISAH Akalla gawarwaki biyar ne aka gano yayin da wasu dama sun bace sakamakon hatsarin jirgin ruwan da ya auku ranar Litinin a yankin Karamar Hukumar Borgu a Jihar Neja. Jami’in kula da iftila’i a yankin Borgu, Malam Musa Said, shi ne ya bayyana haka, inda ya ce a ci gaba da binciken da masu aikin ceto ke yi sun gano gawarwaki guda biyar, kuma ana ci gaba da neman ragowar mutanen da ba a gan su ba bayan aukuwar hatsarin. Haka shi ma Shugaban Hukumar ba da Agajin Gaggawa na Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar…
Read More
Kotun Ƙoli: Zamfarawa sun yi fitar farin dango don taya Gwamna Lawal murna

Kotun Ƙoli: Zamfarawa sun yi fitar farin dango don taya Gwamna Lawal murna

Daga BASHIR ISAH A ranar Litinin da ta gabata dubban Zamfarawa cike murna suka yi dandazo a Gusau, babban birnin jihar domin tarbar Gwamna Dauda Lawal in Gusau, bayan dawowa daga Kotun Ƙoli. A ranar Juma'ar da ta gabata Kotun Ƙoli mai zamanta a Abuja ta tabbatar  da Gwamna Lawal a matsayin wanda ya lashe zabe Gwamnan Zamfara, tare da yin watsi da karar da bangare hamayya ya daukaka na kalubalantar nasarar tasa. Cikin sanarwar manema labarai da ya fitar, Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ce masoyan gwamnan sun yi fitar farin dango don nuna farin cikinsu dangane da…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Kebbi

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Kebbi

Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan karar da aka dauka ta neman a sauke Dr Nasir Idris na jam'iyyar APC a matsayin Gwamnan Jihar Kebbi. Kotun ta dauki wannan matsaya yayin zaman ci gaba da sauraren shari'ar da ta yi ranar Talata karkashin jagorancin Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun, bayan ta karrbi bayanan lauyoyin duka bangarorin. Kotun ta ce za ta sanar da bangarorin da lamarin ya shafa baya ta tsayar da lokacin da za ta yanke hukunci kan shari'ar. Jam'iyyar PDP a Jihar Kebbi da dan takarar gwamnanta a zaben 2023, Manjo Janar Aminu Bande, su ne suka daukaka…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Nasarawa

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Nasarawa

Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari'ar zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa da ke gabanta. Kotu ta yi hakan ne a zaman ci gaba da sharilar da ta yi a wannan talatar. Ta ce za ta sanar da bangarorin da shari'ar ta shafa ranar da za raba gardama idan ta tsayar da rana nan gaba. Ana fafata shari'ar ne tsakanin Gwannan jihar, Injiniya Abdullahi Sule da kuma Jam'iyyar PDP a jihar tare da dan takararta na gwamna, David Ombugadu
Read More
Ɓata-gari sun kai hari asibiti sun yi awon gaba da gawa a Ekiti

Ɓata-gari sun kai hari asibiti sun yi awon gaba da gawa a Ekiti

Daga BASHIR ISAH Wasu bata-garin matasa a Jihar Ekiti sun kai hari Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jihar (EKSUTH) da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar inda suka sace wata gawa. MANHAJA ta kalato cewar wannan al’amari ya auku ne a ranar Litinin lamarin da ya haifar da tsaiko a ayyukan asibitin. Bayanai sun ce, gawar da aka sace din ta mahaifin daya daga cikin bata-garin ne. Sai dai, babbu cikakken bayani kan dalilin da ya sa matasan daukar wannan mataki. Faruwar wannan al’amari ya sanya kungiyar likitoci a jihar ta bai wa mambobinta umarnin fara yajin aikin sai-baba-ta-gani domin nuna rashin…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe ƙarin mutum 3 daga cikin 10 da suka sace a Abuja

‘Yan bindiga sun kashe ƙarin mutum 3 daga cikin 10 da suka sace a Abuja

*Sun ƙara kuɗin fansa zuwa N700m Daga BASHIR ISAH 'Yan bindigar da suka yi garkuwa da wasu mutum 10 a yankin Dutse, Abuja a ranar 7 ga Janairun da ake ciki, sun kashe karin mutum uku daga cikin mutane 10 da suka yi garkuwa da su. Majiyarmu ta ruwaito cewar, 'yan bindigar sun aikata hakan ne a matsayin gargadi ga 'yan wadanda ke hannunsu kan kudin fansar da suka nema a biya. A cewar majiyar, 'yan bindigar sun kara kudin fansar zuwa Naira miliyan 100 kan kowane mutum sabanin Naira miliyan N60 da suka nema da farko. Da wannan, 'yan…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya isa Owerri don rantsar da Gwamna Hope Uzodinma wa’adi na biyu

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya isa Owerri don rantsar da Gwamna Hope Uzodinma wa’adi na biyu

Daga BASHIR ISAH A halin da ake ciki, Shugaban Kasa Bola Tinubu ya isa Owerri, babban birnin Jihar Imo domin shaida bikin rantsar da Gwamna Hope Uzodinma a wa'adin mulkin jihar na biyu. MANHAJA ta kalato cewa, Tinubu ya bar Abuja zuwa Imo ne jim kadan bayan bikin Ranar Tunawa da Sojoji. Bikin rantsarwar na guna ne a babban filin wasannin motsa jiki na Dan Anyiam da ke Owerri. Yayin ziyarar, ana sa ran Shugaba Tinunu zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin jihar ta aiwatar.
Read More
Aminin Pantami ya ba da tallafin N50m don kuɓutar da ‘yan matan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Abuja

Aminin Pantami ya ba da tallafin N50m don kuɓutar da ‘yan matan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Abuja

Daga BASHIR ISAH Tsohon Minista kuma fitaccen malamin Islama, Farfesa Isa Pantami, ya sanar cewa an tara kudi Nairia miliyan 50 domin ceto da ‘yan matan zuri’ar Al-Kadriyar da ‘yan binbdiga suka yi garkuwa da su a yankin Abuja. Pantami ya ce wani amininsa ne ya ba da tallafin ragowar Naira miliyan 50 daga cikin miliyan 60 da ‘yan bindigar suka bukaci a biya, bayan da ya tattauna batun da shi. A cewar tsohon ministan, “Alhamdu lil Laah! A kashin kaina ba na goyon bayan biyan kudin fansa ga barayi. Amma tun da a bayyane yake mun rasa ‘yarmu Nabeeha…
Read More