Labarai

Barcelona ta sha kaye na uku a gasar LaLiga

Barcelona ta sha kaye na uku a gasar LaLiga

Daga MAHADI M. MUHAMMAD Barcelona ta sha kaye na uku a gasar LaLiga, bayan nasarar doke ta da ƙungiyar Rayo Vallecano ta yi da ƙwallaye 2-1. Alvaro Garcia da Fran Garcia suka jefa ƙwallayen biyu a ragar Barcelona, kafin daga bisani Robert Lewandowski ya rama guda ɗaya. Sai dai duk da rashin nasarar, Barcelona ta ci gaba da jagorancin LaLiga, abinda zai ba ta damar lashe kofin gasar na farko tun bayan kakar wasa ta 2018 da 2019. A halin yanzu maki 11 a tsakanin Barcelona da babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid, yayin da wasanni takwas suka rage wa kowannnensu…
Read More
Ruwa da iska mai ƙarfi sun lalata gidaje a Damaturu

Ruwa da iska mai ƙarfi sun lalata gidaje a Damaturu

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Wani ruwan sama haɗe da iska mai ƙarfin gaske sun lalata wasu gidaje a garin Damaturu, hedikwatarta Jihar Yobe. An shafe awa guda ana maka ruwan da iskan, tun gabanin Sallar La’asar a ranar Lahadi. Da daddare bayan Sallar Isha, aka sake maka wani ruwan kamar da bakin ƙwarya na tsawon lokaci. Akasarin gidajen da suka rushe suna unguwanni irin su Fawari na da Nainawa da gefen Rukunin Gidajen Ali Marami sai wani ɓangare na unguwar Pomfomari da makamantansu. Wani magidanci da wannan iftila’in ya rutsa da gidansa a unguwar Nainawa, Malam Umar ya tabbatar…
Read More
Mun samu labarin aukuwar gobara 258 a cikin watanni uku a Jihar Kano – Hukumar Kashe Gobara

Mun samu labarin aukuwar gobara 258 a cikin watanni uku a Jihar Kano – Hukumar Kashe Gobara

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce ta samu rahoton afkuwar gobara 258 a cikin watanni uku a sassa daban-daban na jihar. Da yake magana da NAN a ranar Talata, Hassan Muhammed, daraktan hukumar, ya ce an rubuta abubuwan da suka faru a kamfanoni, gidaje, shaguna, gidajen mai, kasuwanni, gonar kiwon kaji, motoci, da dai sauransu. “Yawancin faruwar gobarar ta faru ne sakamakon amfani da na’urorin lantarki da aka yi amfani da su, da cunkoson ababen lantarki, da cusa abubuwa da yawa a cikin mashin guda ɗaya da kuma amfani da igiyoyin lantarki na…
Read More
‘Yan bindiga sun sace mutane 29 a ƙauyen Abuja

‘Yan bindiga sun sace mutane 29 a ƙauyen Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu mutane 29 da suka haɗa da manya maza, matan aure da yara a ƙauyen Yewuti, mahaifar tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Kwali, Alhaji Zubairu Jibrin Yewuti. An samu labarin cewa wasu matan aure biyu, Zainab Umar da Aisha Zubairu, sun tsere daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da su a lokacin da aka kai su cikin daji. Daga cikin waɗanda aka sace akwai Idris Mohammed, Abdullahi Zubairu, Sani S. Magani, Peter Modu, Ibrahim Mamman, Yellow Abdulrasheed, Musa Suleiman, Simbiya Ishaku, Sumaiya Ibrahim, Muktari Yunusa…
Read More
Tinubu ya koma masaukin baƙi na tsaro da zama gabanin rantsar da shi

Tinubu ya koma masaukin baƙi na tsaro da zama gabanin rantsar da shi

Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ya koma masaukin baƙi na tsaro da ke yankin Maitama a Abuja, da zama. Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na Tinubu, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ta hanyar wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Tiwita a ranar Laraba. A cewar Onanuga, Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, za su ci gaba da zama a nan masaukin har zuwa lokacin da za a rantsar da su a matsayin Shugaban Ƙasa da Mataimaki a ranar 29 ga Mayu, 2023. A ranar Litinin Tinubu ya dawo Nijeriya bayan hutun wata…
Read More
Da ɗumi-ɗuminsa: Buhari ya maida kakin soja

Da ɗumi-ɗuminsa: Buhari ya maida kakin soja

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya maida kakin soja albarkacin bikin faretin nuna ƙawa na Sojojin Nijeriya na 2023. Buhari ya isa filin taron, Eagle Square - Abuja, sanye da kakin soja da misalin ƙarfe 10:18 na hantsi. Bikin gabatar da launuka, biki ne da ke nuna ranar tunawa ko abin da ya faru a tarihin wata runduna ta musamman. Daga cikin waɗanda suka mara wa Buharin baya har da Shugaban Fadar Ma'aikata na Fadar Shugaban Ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, inda shi ma aka gan shi sanye da kakin na soja. Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor, Babban Hafsan Sojoji, Lt.-Gen.…
Read More
Tsohon Ministan Ƙwadago, Musa Gwadabe ya rasu yana da shekara 87

Tsohon Ministan Ƙwadago, Musa Gwadabe ya rasu yana da shekara 87

Fitaccen ɗan siyasa kuma tsohon Ministan Ƙwadago, Alhaji Musa Gwadabe, ya kwanta dama. Majiya daga ahalin marigayin ta ce, tsohon Sakataren Gwamnatin Kanon ya rasu yana da shekara 87 bayan fama da rashin lafiya. Majaiyarmu ta ce za a yi jana'izar marigayin ne ranar Laraba da misalin ƙarfe biyu na rana a gidansa da ke hanyar Ado Madaka a Maiduguri road, Kano. Gwadabe ya rasu ya bar mata biyu, 'ya'ya 11 da jikoki da dama. Daga cikin 'ya'yan nasa akwai Alhaji Nazifi Musa Gwadabe da sauransu.
Read More
Jami’ar Bayero ta yi rashi

Jami’ar Bayero ta yi rashi

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Hukumar Jami’ar Bayero da ke Kano ta sanar da rasuwar magatakardarta, Malam Jamil Ahmad Salim, a safiyar ranar Laraba. Tun da farko an wallafa sanarwar ne a shafin Facebook na Jami’ar ta BUK, inda ake sanar da al’ummar Musulmi guri da lokacin da za a yi jana’izar marigayin. Sanarwar ta ƙara da cewa, za a yi jana’izar marigayin da misalin ƙarfe goma na safe a Babban Masallacin Juma’a da ke sabuwar jami’ar da ke kan titin zuwa Gwarzo a birnin Kano.
Read More
Kano ce ta uku a jihohin da aka fi kiran wayar salula da Internet– NBS

Kano ce ta uku a jihohin da aka fi kiran wayar salula da Internet– NBS

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya, wato NBS, ta bayyana Jihar Kano a matsayin ta uku a jerin jihohin da suka fi amfani da wayar salula da Internet a ƙasar. Sauran jihohin su ne Legas a matsayi ta ɗaya, sai Ogun a matsayin ta biyu. A wani rahoto da ta saba fitarwa duk bayan watanni uku, NBS ta yi bayani kan harkokin tarho, wanda ya ƙunshi bayanai na watannin ukun ƙarshe na shekarar 2022. Bayanan sun haɗa da na adadin masu kiran waya, da masu amfani da intanet, da kuma yawan masu amfani da kowane kamfanin sadarwar…
Read More
Yau Shugaba Buhari zai tafi Ghana

Yau Shugaba Buhari zai tafi Ghana

A wannan Talatar ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, zai ziyarci ƙasar Ghana don halartar taron ƙolin shugabannin ƙasashen yankin tekun Guinea da za a gudanar a Accra, babban birnin ƙasar. Hakan na ƙunshe ne ciki wata sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta wallafa a shafinta na Tiwita a ranar Litinin. Sanarwar ta ce, ta ce shugaban zai bar Nijeriya ranar Talata, 25 ga Afrilu domin halartar taron, wanda Shugaban Ƙasar Ghana, Nana Akuffo-Ado, zai jagoranta. Ana sa ran shugaban zai gabatar da jawabi a taron wanda zai tattauna dabarun ƙarfafa zaman lafiya da tsaro da yaƙi da masu…
Read More