Jami’ar Bayero ta yi rashi

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Hukumar Jami’ar Bayero da ke Kano ta sanar da rasuwar magatakardarta, Malam Jamil Ahmad Salim, a safiyar ranar Laraba.

Tun da farko an wallafa sanarwar ne a shafin Facebook na Jami’ar ta BUK, inda ake sanar da al’ummar Musulmi guri da lokacin da za a yi jana’izar marigayin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, za a yi jana’izar marigayin da misalin ƙarfe goma na safe a Babban Masallacin Juma’a da ke sabuwar jami’ar da ke kan titin zuwa Gwarzo a birnin Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *