Buhari: Ga wani darasi

Daga SHAFI’U DAUDA GIWA

Wannan bawan Allah shi ne wanda ya fi kowa farin jini a tarihin ƙasarmu Nijeriya.

Ɗaruruwan mutane sun rasa ransu saboda murnar zaɓen da ya ci a shekarar 2015. An yi lokacin da ko takarar kansila mutum ya tsaya sai ya haɗa hotonsa da na Buhari don ya ɗosani farin jini.

‘Yan siyasa bila’adadin sun ci zaɓe a sanadiyyar ɗaga hannunsu da Buhari ya yi, tun kafin ya ci nasa zaɓen a shekarun baya tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011 Allah kaɗai ya san adadin mutanen da shugaba Buhari ya ɗaga wa hannu suka kai labari

Waɗansu sun ce da an ƙwace masa zaɓen da ya ci a shekarar 2015 da Nijeriya ta rushe domin yaƙi ne zai ɓarke tsakanin manyan ƙabilu da addinai

Abin mamaki da fargaba shi ne, yau an wayi gari kafafen yaɗa labarai da sadarwa sun koma kan wasu mutanen waɗanda ake so a ji ɗuriyarsu fiye da Shugaba Buhari.

Duk manyan labaran da a ke bugawa a jaridu yanzu babu labaran Shugaba Buhari, farin jininsa da kwarjininsa da ƙarfin mulkinsa da Allah ya ara masa a hankali duk sun zaizaye, ban san wani ɗan takara da ya haɗa hotonsa da na Buhari ba har aka gama hada-hadar zaɓen wannan shekarar.

Lokaci kenan, duk matsayinka da ƙarfin mulkinka wata rana ba kai ba ne, kana kallo wasu za su zo su maye gurbinka, ka koma gida ka zauna daga kai sai iyalinka.

Kwanakin baya da na ji Shugaba Buhari ya kafa kwamitin miƙa mulki, ya fara haramar barin kujerarsa zai koma gida sai da gwiwata ta yi sanyi.

Ko ba komai rayuwarsa ta koya mana darasin ‘Babu abinda yake ɗorewa har abada’

Shafi’u Dauda Giwa, marubuci ne, kuma manazarci sannan mai sharhi a kan al’amurran rayuwa da siyasa. Ya rubuto daga Kaduna.