Goman Ƙarshe: Da gaske mata addu’ar neman miji suke yi a tahajjud? (II)

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A yau za mu cigaba daga inda muka tsaya a makon ga ya gabata.

Kamar misalin yadda Farfesa Fatima ta bayar ne, inda take cewa wasu iyaye masu kwaɗayin abin duniya suna taimakawa wajen daɗewar ’ya’yansu mata a gida, domin kuwa sun mayar da su tamkar wata hajar neman kuɗi, suna jiran sai wani babban mutum ko ɗan masu kudi ne zai fito su aura masa, saboda tunanin auren zai zama musu tsani na kai wa ga buƙatun su na rayuwa. Haka zalika su ma samarin yanzu idon su ya rufe da neman kuɗi domin su yi rayuwar kece raini, kuma su auri irin macen da suke buri. Ko kuma su samu damar auren ’yar babban gida wacce za ta buɗe musu ƙofar shiga duk wani mataki da suke da burin hawa a rayuwarsu. “Yanzu ba ana aure don soyayya ba ne, sai dai don cimma wani buri na rayuwa.”

“Maza sun mayar da mata abin ado da burgewa, ko kuma ma’aunin samun nasara a rayuwa,” a cewar Rahama Abdulmajid. “La’akari da haka ne ya sa tilas mata su yi taka tsantsan da duk namijin da ya zo musu da sunan soyayya ko aure, ko da kuwa hakan zai sa su daɗewa ba su yi auren ba. Don wani namijin da auren sa gara mace ta zauna a gidan su ba tare da aure ba, ya fi mata rufin asiri da kwanciyar hankali.”

Taɓarɓarewar tattalin arzikin duniya da yadda jama’a suka karkata ga neman kuɗi na daga cikin dalilan da ke kawo jinkiri a aure. Yayin da maza suka shagaltu da neman kuɗi, don samun damar kece raini da abin rufin asiri, su ma kuma matan yanzu hidimar neman tara abin duniya da neman aikin yi domin samun abin dogaro da kai shi ne a gaban su.

A ta bakin Farfesa Fatima Umar, “mata yanzu sun fi son auren mai kuɗi wanda za su huta a gidansa su da iyaye da ’yan uwansu, ba wai talaka da za a yi ta fama da neman na cin yau da na gobe ba.”

Tsarabe-tsarabe da al’adun da aka dora a cikin tsarin auratayya su ma sun taimaka wajen tsorata maza tunkarar aure ba tare da sun shirya ba. Malama Rahama na ganin haƙƙin malamai ne da masu ilimi a cikin al’umma su riqa wayar da kan iyaye, musamman mata, su yi watsi da wasu daga cikin al’adun da suke kawo cikas a sha’anin aure, kuma a riƙa nuna fifikon martaba da matsayin da auren ke da shi, a maimakon abin da za a kashe ko wanda za a samu ta dalilin auren.

Wani matashi mai suna Muhammad Khamees da bai daɗe da aure ba ya bayyana cewa, “a saboda matsalolin kuɗi har sai da na fara tunanin me ya sa ne tun farko ma na tsokano wannan magana. Saboda duk tunani na da dabaru na na tattalin kuɗi da shirin da na tsara, a dalilin wannan aure duk sai da suka rushe.”

Wata mai nazari kan zamantakewar maza da mata, Uwani Umar dake jihar Gombe ta dora alhakin samun irin wadannan matsaloli gabannin aure kan irin ƙarairayin da samari da ’yan mata suke gayawa junan su kafin batun auren ya taso, inda ta ce, “sau da dama za ka ga saurayi yana ruɗin budurwa da wasu irin alƙawura na bogi waɗanda su kan su ba su da tabbas a kansu, bisa tunanin shagulgulan da za a yi na buki ko kuma yanayin zaman auren da za a yi bayan buki. Ita ma kuma tana ruɗin kanta cewa, ga irin jin daɗin da take so ta ji, sakamakon ƙarairayin da saurayinta ya hure mata kunne da su.”

Fargabar irin ɗawainiyar dake cikin hidimar aure, yawan buƙatun da mata ke bijirowa da su waɗanda suka wuce ƙarfin tattalin arzikin mazan ya sa maza ke gudun nuna kansu a matsayin manema aure, sai dai masoya kawai da za a shaƙata ko a ɗebewa juna kewa kamar yadda suke faɗa. Yayin da suke tunanin aure a wajen su ba yanzu ba sai nan gaba, lokacin an samu ’yan canji a hannu.

A shekarun baya idan an fadi cewa, ’yan mata za su koma neman samari, aika musu da saqon soyayya ko zuwa gidan saurayi da sunan taɗi ko zance, sai a ƙaryata mutum ko kuma a yi tofin alla-tsine saboda tunanin ba yadda za a yi hakan ta faru, sai ga shi yanzu hakan na neman zama ruwan dare, ba wai wani abin ba a samun ba. Wannan ba yana nufin maza ba sa neman soyayyar matan ba ne, amma saboda ƙarancin mazan wajen zuwa wajen matan su bayyana musu abin da ke zuciyar su, ya sa matan suke cire kunya suna tunkarar mazan kai tsaye, musamman ga matan da suke ganin suna da buƙatar auren kuma babu tsayayyen saurayi.

“Ana samun damuwa wajen yadda maza suke gudun yi wa mace magana ko zuwa neman auren mace, don tsoron za ta iya raina masa arziki ko ya gagara ɗaukar awainiyarta,” in ji Hajiya Zulai Aminu wata uwa da take da ’ya’ya mata.

Ta ƙara da cewa, “’yan mata da dama da ke zaune a unguwannin manya na bayan gari ko GRA suna wuyar samun samari, in ba a wuraren buki ko makarantu ba.”

Wannan ya zo daidai da fahimtar Farfesa Fatima Umar da Hajiya Uwa Idris da suke ganin tsoron da maza suke da shi a kan mata yana daga cikin matsalolin da matan ke fuskanta. A ganin Hajiya Uwa, “Mata ne suka haifar da halin da suke ciki na rashin samun mazajen aure da wuri, saboda yadda suke nuna musu cewa sun yi karatu mai zurfi, suna da wayewa kuma sun fi maza hanyar samun kuɗi.”

“Kwaɗayin samun shaidar karatu mai zurfi da yin aikin samun albashi a ɓangaren ’yan mata na daga cikin dalilan dake kawo jinkirin aure a wajen wasu matan,” a cewar wani mai nazarin rayuwa Malam Sidi Ali Aliyu da ke Jos. “Kuma yana taimakawa wajen gurgunta auren da aka fara shi ba da ingantacciyar soyayya ko tarbiyya ta addini ba.”

A ɗaya ɓangaren idan an lura, za a fahimci cewa soyayya irin ta da wacce samari da ’yan mata ke yi wa juna lokacin ƙuruciya ta samartaka da ’yan matanci har zuwa lokacin aure da bayan haka, yanzu ta fara ɓacewa, ko ma dai a ce ta ɓace baki ɗaya. Zaurukan sada zumunta na wayoyin salula irin su Facebook, Whatsapp da Twitter sun maye gurbin soyayya da hirar taɗi da ake zuwa a shekarun baya. ’Yan mata na fakewa da waɗannan kafofi wajen neman mazajen da za su yi soyayya ko auren su fiye da yadda mazajen kan yi amfani da su don neman mata.

Maryam Ali Ali ita ma wannan matsala lalacewar matasa ta hanyar amfani da kafafen sadarwa na zamani na daga cikin abubuwan da suka fi jan hankalinta dangane da jinkirin aure a tsakanin matasan arewacin ƙasar nan, inda ta yi nuni da yadda samari suke shagala da neman ’yan matan ƙabilu waɗanda ba Musulmi ba, don samun damar biyan buƙatun su na sha’awa da shaiɗan ke angiza su a kai, sanadiyyar buƙatar da suke da ita na mace a zuciyarsu.

Sadiq Bature wani matashi ne da yake yawan amfani da zaurukan sada zumunta na waya, ya bayyana cewa, yana da ’yan mata da dama da yake hulɗa da su ta waya, waɗanda akasari su ne suka fara neman sa da abokantaka, har ta kai ga sun fara soyayya da wasu da ziyartar juna. Ya ce, “idan ina son hira da mace ba sai na je ina shan sanyi ko ina bin layi kafin na samu ganin ta ba, daga ɗakina da ’yar wayata a hannu zan nemi duk irin matar da nake so.”

Waɗannan canje-canje da ake kokawa da su ƙalubale ne na rayuwa da zamani yake tafe da su. Sai dai ba zai yiwu a kame baki ko a naxe hannu a zuba ido ba tare da tsawatarwa ba a duk yayin da wata varna ta bayyana ba. Wajibin iyaye ne, malamai da masu tarbiyya su riƙa faɗakarwa da sa ido game da irin kaiwa da komowar ’ya’yan su, samari da ’yan mata ke yi, don gudun kada kawar da kan ya jefa su da sauran al’umma cikin hallaka.

Mafita dai, a cewar Maryam Ali Ali ita ce a koma ga kwaɗaitar da mutane yin aure da wuri, musamman ga ’yan mata, tare da ƙarfafa musu gwiwar cigaba da karatun su ko da bayan sun yi auren ne. Sannan a rage al’adun da ake kallafawa masu buƙatar aure, da sauran bidi’o’in da aka ƙirƙiro da sunan murnan buki, waɗanda suma a karan kansu ba ƙaramin kashe kuɗi suke jawo wa ba.

Wannan shawara ta yi kama da ta Malama Fatima Sayyida da shugabar ƙungiyar zawarawa da marayu ta Jihar Kano Hajiya Altine Abdullahi da Hajiya Uwa Idris daga Jihar Kaduna duk suna ganin dacewar karfafa ilimin ’ya’ya mata, amma tare da goya musu baya su cigaba da neman ilimi daga gidajen auren su, a maimakon a bar su a gida ba aure sai sun kammala karatu ko sun samu aiki kafin su nemi mijin aure.

Samar da ingantaccen tsari don farfaɗo da kimar aure da martabarsa a idon matasa ta hanyar kafa wata cibiya mai kula da tattalin sha’anin aure da wayar da kan iyali, domin gyara fahimtar matasa da sauran jama’a game da abin da aure ya kunsa, yadda ya dace a kulla alaƙar aure, zamantakewar ma’aurata da kula da haƙƙoƙin juna. Wannan shi ne tunanin Farfesa Fatima Umar, Malama Rahama Abdulmajid da Hajiya Uwa Idris, wadanda ke ganin cigaban zamani da tasirin ilimin da mata suka samu ya haifar da yadda suke tunanin canza akalar yadda tsarin zamantakewar aure take a wannan zamani, ba kamar yadda a shekarun baya iyaye da kakanni suka yi ta haƙuri da juna ba.

Amma kuma ba su goyi bayan a ce mace ta fi ƙarfin zama ƙarƙashin namiji ba, matukar za a zauna cikin ƙauna da soyayya, fahimtar juna da mutunta haƙƙoƙin juna. Ba tare da wani ya yi amfani da addini ko al’ada wajen tauye haƙƙin abokin zamansa ba.

Shugabar Ƙungiyar Zawarawa da Marayu ta Jihar Kano Hajiya Altine Abdullahi ta ce wajibi ne gwamnati ta yi ruwa da tsaki a sha’anin aure, domin magance ɗimbin matsalolin da ake samu a dalilin riƙon sakainar kashin da ake yi wa aure, ta yadda mutane ke yin aure babu wani ƙwaƙƙwaran tsarin da zai riƙe auren da daraja.

Ta ce, gwamnati ce ya kamata a ce ta ɗauki kimanin kashi 70 cikin 100 na sha’anin aure, sai kuma a bar wa iyaye kashi 30, ta haka ne zai ƙarawa aure daraja kuma a kafa dokar da za ta kare haƙƙoƙin ma’aurata kafin, yayin, da bayan rabuwar aure. Sannan a tilastawa duk waɗanda za su yi aure sai sun je sun yi rijista da gwamnati, an ba su shaidar zama ma’aurata kuma su sa hannu a dokokin kula da haƙƙoƙin zamantakewar aure. Domin a samu damar ɗaukar matakan da suka dace na hukunta wanda ya saɓawa haƙƙoƙin aure da martabarsa.