Zuwa ga ‘yan mata da zawarawa: Hattara da samarin shaho!

Daga AMINA YUSUFU ALI

Masu karatu barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a filinku na zamantakewa a jaridarmu mai farin jini ta Manhaja.

Kamar yadda kuka gani a take, kira ne ga ‘yammata da zawarawa a kan su guje wa wasu nau’in samari da ake kira da samarin shaho. Na san mai karatu zai shiga kogin tunani a kan su waye samarin shaho kuma?

Samarin shaho ba wasu ne ba face samarin da za su zo wajen budurwa ba da niyyar aurenta ba sai don su rage lokaci, ko kuma don su ɓata mata rayuwa su gudu. Abinda ya sa za mu yi rubutu a kan samarin shaho shi ne, da yawa waɗannan samari sun fi shiga ran mata.

Musamman ƙananan ‘yammata. Kuma so ko abin hannun namiji yakan rufe wa mata idonsu kasa banbance tsakanin aya da tsakuwa. Domin samarin shaho abin gudu ne sosai. Idan za ki mutu saboda sonsu ba za su ji ko ɗar a kanki ba. Saboda sun saba kuma sun goge a harkar yaudara yadda idan ba lura kika yi da kyau ba, yanzun nan sai a sha ki basilla.

Sannan ga uwa uba ɓata lokaci. A banza zai ɓata miki lokaci ba tare da ya aure ki ba. Ga dai wasu hanyoyi da mata za su gano su waye samarin shaho kuma su nesanta kansu da su:

*Babbar alamar samarin shaho shi ne za ki gansu suna sayen wayoyi masu tsada, duk da yawancinsu ba wasu masu arziki ba ne. Amma zai wuya ya ga ya sayi waya mai tsada tare da sanya sutura mai tsada alhali ba mai kuɗi ba ne. Ga ɗaukar wanka a yi ta hoto ana sa wa a shafukan zumunta a koyaushe.

*Rashin tausayinta.

*Roƙon budurwa ko bazawara kuɗi maimakon shi ne mai ba ta.

*Rashin yi wa budurwa kyauta sosai. Yawanci saurayin da ya zo wajen budurwa da aure yakan yi mata kyaututtukan don iyayenta su san cewa yana ciki. Kodayake, ana samun wasu mayaudaran masu yaudarar mace da kuɗin su ɓata mata rayuwa.

In dai ya ce yana sonki da aure ba ya miki kyauta, ƙarya yake yi. Domin gani yake duk abin da ya kashe asara ne don ba aurenki zai yi ba. Sai dai idan kin biye masa kuna shaiɗana.

*Yawan zuwa da daɗewa a gidan su budurwa. Shi ma wannan yana daga alamomin mayaudaran saurayi. Kuma ba ya ba ta komai idan ya zo.

  • Rashin jin kunyar a ba shi abinci a gidan su budurwa ya cinye ba ya jin kunyarki bare iyayenki. burinsa a yi masa abinci ba ya kawo komai. Har ma wani lokaci ya dinga ba da umarni a yi masa girki kaza ba tare da sisinsa ba. Shi sam ba ya jin kunya saboda ya riga ya san ba aurenki zai yi ba ballantana ya ji tsoron jin kunya a gaba.

*Ba ya yawan kiranki sai dai ke ki kira shi. Kuma ba zai sa wa mace kati ba sai ma ya dinga ƙoƙarin dole ita za ta dinga kiransa.

*Neman son sai ya taɓa budurwa ko bazawarsa da son yi mata zancen batsa.

*Yakan ɗauki dogon lokaci yana neman mace kuma ya ƙi fitowa, sannan ya ƙi tafiya ya ba wa wani dama ya zo. Kar ki yaudaru ‘yaruwata. Duk saurayin da ya ja lokaci a soyayya ba aure ki zai yi ba.

Kuma idan kika biye masa sai dai ki ƙara jan lokaci amma ba zai aure ki ba. Watarana sai dai idan ya gaji da yaudarar ya ɓace ɓat, ko ki ji labarin aurensa ya zo ya ce miji auren dole ko na haɗi aka yi masa.

*Rashin son cigabanki. Kamar ya hana ta karatu ko sana’a tun kafin ya aure ta.

*Rashin son nuna ta ko da a waya ne ga iyayensa ko wani makusancinsa. Shi ma yana nuna ba da aure yake sonki ba.

*Rashin yadda ya je ya gaishe da iyayenta.

*Rashin cikakkiyar sana’a.

  • Yawan ba da uzuri da rashin cika Miki alƙawurra idan ya ɗauka.

Daga zarar kin karanci saurayinki kin ga ya faɗa ɗaya daga cikin waɗannan mutanen, to ki shafa wa kanki lafiya ki ƙara gaba. Kuma ki gode wa Allah da ya raba ki da jegon jaka.

Sannan akwai abinda waɗannan samarin shaho suke yi bayan sun latsa mace sun samu biyan buƙata ko kuma ya gaji da yaudararta ko kuma ya yi dabarar ya lalata rayuwar ta, amma ya kasa shawo kanta. Sai ya ƙirƙiro wasu hanyoyi don a ɓata ya samu hanyar guduwa.

*Yakan tsiri saurin fushi da ba ya yi a baya. Abu bai kai ya kawo ba sai ya rufe ki da faɗa. Ya ɗora miji laifin dukkan abin. Da haka ke ma za ki yi fushi shikenan gayyar ta watse.

*Yawan yi miki abinda ya san ba kya so kawai don ya harzuƙa ki ku yi tashin hankali.

  • Zai janye daga yawan kiranki ko zuwa gidanku yadda ya saba. Da zarar kin ga haka, kawai ki rabu da shi ki nemi zaɓin Allah.

*Daina damuwa da al’amuran ki sosai. Kodayake da can ɗin ma ba damuwa ya yi ba. Amma a da saboda yana neman karvuwa zai yi ƙoƙarin ganin ya yi haka ko da na ƙarya ne. Amma yanzu zai daina ɓoye-ɓoye ya bayyana asalin manufarsa a kanki.

*Kamar yadda a da yake miki zancen aure ko da ƙarya ne, yanzu zai daina ma wahalar da kansa wajen ƙaryar. Zai ƙyale ki, ki yi kiɗa da rawar ma gabaɗaya.

*Kodayake, da ma yana da wasu matan da yake kulawa bayan ke. Domin shi awajensa hakan wata hanya ce ta tafiyar da rayuwarsa. Amma yanzu zai daina shakkar ki zai dinga zancen ‘yammatansa a gabanki. Manufar hakan kuwa, ya san za ki ji kishi kuma za ki tunzura shi kuma sai ya samu hanyar guduwa.

*Zai daina cika Miki alƙawari. Saboda yanzu ya daina lallaɓa ki. Shi burinsa ma ya samu hanyar tunzura ki ya gudu ya barki.

*Idan ma yana miki kyauta komai ƙanƙantarta ta hana rantsuwa yanzu zai daina. Domin a ganinsa ba a kamfen bayan an gama zabe.

*Zai daina kishinki kamar yadda yake yi a baya. Idan kika samu kanku a wannan hali, ‘yaruwa kada ki sake ki ce za ki jure ko ki yi ƙoƙarin canza shi.

Domin ba dole ki samu nasara a kan mutumin da ya riga ya gama tsai da ransa cewa, zai rabu dake ba. Kawai ke ma ki daure ki rabu da shi tun ganin take-takensa na farko. Idan kika kau da kai kamar ba ki gani ba, zai iya ƙara sanya miki wasu matakan da suka fi waɗannan wuya da tsauri.

Duk yadda kika yi da wuya ki shawo kansa. Sai ki durfafi addu’a kuma ki danne zuciyarka ki rabu da shi ɗin. Allah Al- Musawwiri sai ki ga ya jawo muku wanda ya fi shi alkhairi. Kuma ko nan gaba ya dawo, ba nadama ta yi ba ko sonki yake yi ba. Wani abin ne ya ciwo shi na son kansa. Sannan ki daure ki ba wa sauran masu sonki dama su fito aurenku ki huta.

Mu haɗu a wani makon idan Allah kai rai.