Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya, wato NBS, ta bayyana Jihar Kano a matsayin ta uku a jerin jihohin da suka fi amfani da wayar salula da Internet a ƙasar.
Sauran jihohin su ne Legas a matsayi ta ɗaya, sai Ogun a matsayin ta biyu.
A wani rahoto da ta saba fitarwa duk bayan watanni uku, NBS ta yi bayani kan harkokin tarho, wanda ya ƙunshi bayanai na watannin ukun ƙarshe na shekarar 2022.
Bayanan sun haɗa da na adadin masu kiran waya, da masu amfani da intanet, da kuma yawan masu amfani da kowane kamfanin sadarwar da ke Nijeriya.
Ta cikin rahoton, a watannin ƙarshen 2022, jimillar mutanen da suka yi kiran wayar salula ta kai 222,571,568. Sai kuma jimillar waɗanda suka yi amfani da intanet da ta kai 154,847,901.
Jihohin da ke kan gaba da kuma na karshe a amfani da salula da data
Jihar Legas da ke kudu masu yammacin Nijeriya ke kan gaba a yawan masu amfani da salula, mai biye mata ita ce makwabciyarta jihar Ogun, sai kuma Kano da ke Arewa maso yammaci, a mataki na uku.
Ga jerin jihohi uku da ke kan gaba da kuma na matakin ƙarshe a watannin ƙarshen 2022:
Matakin jiha amfani da kiran salula Amfani da data
Ta ɗaya Legas 26,460,867 18,702,394
Ta biyu Ogun 12,994,352 9,206,614
Ta uku, Kano 12,373,201 8,470,131
Ta 35, Ekiti 2,001,846 1,474,970
Ta 36, Ebonyi 1,920,996 1,264,825
Ta 37, Bayelsa 1,571,692 1,101,002
Kazalika NBS ta ce a ɓangaren kamfanonin salula da ke Nijeriya kuwa, a ƙarshen 2022, kamfanin MTN ne ya fi yawan masu yin kiran salula, wad’ɗanda suka kai 89,016,678, da kuma masu amfani da data da suka kai 65,619,610.