Labarai

Sudan: Jihohin Jigawa, Kaduna, Borno sun kwashe ‘ya’yansu zuwa gida daga Masar

Sudan: Jihohin Jigawa, Kaduna, Borno sun kwashe ‘ya’yansu zuwa gida daga Masar

Daga BASHIR ISAH Da alama wasu daga jihohin Nijeriya sun ɗauki nauyin kwashe 'ya'yansu da suka maƙale a Sudan zuwa gida bayan da Gwamnatin Tarayya ta yi jigilarsu zuwa ƙasar Masar. Jaridar News Point Nigeria ta kalato cewar, jihohin da lamarin ya shafa sun haɗa da Borno da Jigawa da kuma Kaduna. Shugaban Ƙungiyar 'Yan Nijeriya Mazauna Sudan (Ɓangaren Dattawa), Dokta Hashim Na’Allah, ya tabbatar faruwar hakan. Ya ce, “Tabbas, gwamnatin jihohin Kaduna da Jigawa sun kwashe 'yan asalin jihohin yau.” Haka shi ma ɗalibi Abdullah Anyuabuga, ya ce “gwamnatin Kaduna ta kwashe 'yan asalin jihar a yau ta tafi…
Read More
Ranar Ma’aikata: Gwamnati ta yi amaye ta lashe kan bai wa NLC izinin amfani da ‘Eagle Square’

Ranar Ma’aikata: Gwamnati ta yi amaye ta lashe kan bai wa NLC izinin amfani da ‘Eagle Square’

Bayan kimanin sa'o'i 48 da janye izinin da ta bai wa Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) na damar amfani da dandalin 'Eagle Square' wajen gudanar da taron Ranar Ma'aikata na bana, Gwamnatin Tarayya ta maida wa NLC izin da ta janye don amfani da dandalin. Ministan Ƙwadago, Sanata Chris Ngige, shi ne ya sanar da maido da izinin a madadin Gwamnatin Tarayya cikin sanarwar da ya fitar mai ɗauke da sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a na ma'aikatarsa, Olajide Oshundun. Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga ɗaukacin waɗanda aka miƙa wa gayyata…
Read More
Mun gyara aikin soja a Nijeriya – Shugaba Buhari

Mun gyara aikin soja a Nijeriya – Shugaba Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, an cimma ƙwararan shirin inganta tsaro a Nijeriya, tare da inganta kayan aiki, horar da jami’ai da tsarin jin daɗin jama’a da ya shafi fiye da yara 50,000 na jaruman sojojin da suka mutu. Da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis, a wani bikin da ya samu halartar tsaffin shugabannin ƙasar biyu, shugaban ƙasa, Janar Yakubu Gowon da shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, shugaban ƙasar ya ce, ya kafa aikin ɗaukar sojoji 60,000 a aikin soja, kuma dubbai aka yaye daga makarantar horar da sojoji ta Nijeriya da sauran cibiyoyin…
Read More
Tinubu, Shugaban APC na Ƙasa, Adamu da wasu sun yi ganawar sirri

Tinubu, Shugaban APC na Ƙasa, Adamu da wasu sun yi ganawar sirri

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Sanata Bola Tinubu ya gana da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu a gidan tsaro da ke Abuja. A wajen taron da aka gudanar a sirrance akwai Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege; Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Iyiola Omisore da tsohon Sakataren Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugabancin Jam’iyyar APC, Hon James Faleke. A ƙarshen taron, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa ya ce taron wani aiki ne na yau da kullum. Ya ƙi bayyana batutuwan da aka tattauna…
Read More
Gwamnoni sun yi bankwana da Osinbajo a taron Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa na ƙarshe

Gwamnoni sun yi bankwana da Osinbajo a taron Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa na ƙarshe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mambobin Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa (NEC) a jiya ranar Alhamis sun gudanar da wani taro na ban mamaki kuma na ban-kwana da gwamnati mai barin gado a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Taron ya gudana ne a ƙarƙashin Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo wanda shi ne Shugaban Majalisar. Gwamnoni da wasu ‘yan majalisar zartaswa na tarayya sun tashi daga taron majalisar tattalin arziki na wata-wata da kalaman yabo ga Mataimakin Shugaban Ƙasa. Da yake jawabi a madadin gwamnonin jihohi 36 kuma a ƙarƙashin Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF), Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato…
Read More
Ranar Ma’aikata: Gwamnati ta janye izinin da ta bai wa NLC kan amfani da dandalin ‘Eagle Square’

Ranar Ma’aikata: Gwamnati ta janye izinin da ta bai wa NLC kan amfani da dandalin ‘Eagle Square’

Daga BASHIR ISAH Hukumar Birnin Tarayya (FCT), ta janye izinin da ta bai wa Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) don gudanar da bikin Ranar Ma'aikata na bana a dandalin Eagle Square da ke Abuja. Babban Sakataren ƙungiyar, Comrade Emmanuel Ugboaja, shi ne ya bayyana haka yayin zaman da ƙungiyar ta yi ranar Juma'a a Abuja. Ya ce janye izinin na ƙunshe ne cikin wasiƙar da Ministan Abuja, Muhammad Musa Bello, ya aike wa ƙungiyar. Wasiƙar ta ce an janye izinin ne don shirye-shiryen rantsar da sabuwar gwamnati wanda zai gudana a nan dandalin na Eagle Square ranar 29 ga…
Read More
Gwamnati ta sake ɗage shirin ƙidayar al’umma

Gwamnati ta sake ɗage shirin ƙidayar al’umma

Gwamnatin Tarayya ta sake ɗage shirin ƙidayar al'umma na 2023. Majiya mai tushe ta shaida wa jaridar News Point Nigeria a ranar Asabar cewar, an cimma matakin ɗage shirin ne bayan wata ganawa tsakanin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Shugaban Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), Nasir Isa Kwarra. A cewar majiyar, an ɗage shirin ne saboda ƙalubalan da Hukumar NPC ke fuskanta dangane da gudanar da shirin. Duk da dai majiyar ba ta bayyana matsalolin ba, amma dai a baya hukumar ta dakatar da shirin horar da ma'aikatanta na wucin-gadi saboda rashin kuɗi da sauransu. Majiyar ta ce ba za…
Read More
‘Yan sanda sun kashe gawurtattun ‘yan bindiga a Katsina

‘Yan sanda sun kashe gawurtattun ‘yan bindiga a Katsina

'Yan sanda a Jihar Katsina sun ga bayan gawurtattun 'yan bindiga, Shehu Tsauni da Duna a jihar. Haka nan, 'yan sanda sun ƙwato bindiga ƙirar AK 47 guda biyu daga hannun 'yan fashin dajin. Bayanai sun ce, 'yan sanda sun halaka ɓarayin ne bayan da suka yi yinƙurin yin garkuwa da wani fitaccen ɗan kasuwa a jihar. Majiyarmu ta ce lamarin ya auku ne a ranar Alhamis bayan da bayanan sirri suka riski sashen yaƙi da garkuwa da mutane na Rundunar 'Yan Sandan Jihar. Ta ƙara da cewa, bayan musayar wutar da aka yi tsakanin 'yan sanda da 'yan bindigar,…
Read More
Ta ƙona kanta bisa zargin saurayinta da cin amana a Jigawa

Ta ƙona kanta bisa zargin saurayinta da cin amana a Jigawa

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Wata mata ’yar shekara 35 mai suna Maryam Aminu ta conna wa kanta da kanta wuta bisa zargin saurayinta da cin amanarta a Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa. Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a jihar, Adamu Shehu, ne ya tabbatar da afkuwar lamarin ga manema labarai jiya Alhamis, 27 ga Afrilu, 2023. Ya ce, lamarin ya faru da misalin ƙarfe biyu na dare a unguwar Gindin Ɗinya da ke yankin Ƙaramar Hukumar Dutse. Ya ƙara da cewa, bisa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, matar ta kwarara wa…
Read More
Yau wa’adin da Hukumar Alhazai ta bai wa maniyyata su kammala biyan kuɗaɗensu ke cika

Yau wa’adin da Hukumar Alhazai ta bai wa maniyyata su kammala biyan kuɗaɗensu ke cika

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta bayar da wa'adin zuwa ranar Juma'a, 28 ga Afrilu, 2023, a matsayin ƙarshen wa'adin tura kuɗaɗen aikin hajjin shekarar 2023 daga maniyyata da kuma hukumomin kula da jin daɗin alhazai na jihohi. Shugaban Hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle-Hassan, ne ya bayar da wannan umarni a ranar Larabar da ta gabata yayin gudanar da wani gagarumin taron tsere-tsare da shuwagabannin hukumar jin daɗin alhazai ta gudanar a gidan Hajji da ya ke Abuja. A cewar wata sanarwa da mataimakiyar daraktar hulɗa da jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda-Usara ta fitar, ta ce,…
Read More