Ranar Ma’aikata: Gwamnati ta janye izinin da ta bai wa NLC kan amfani da dandalin ‘Eagle Square’

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Birnin Tarayya (FCT), ta janye izinin da ta bai wa Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) don gudanar da bikin Ranar Ma’aikata na bana a dandalin Eagle Square da ke Abuja.

Babban Sakataren ƙungiyar, Comrade Emmanuel Ugboaja, shi ne ya bayyana haka yayin zaman da ƙungiyar ta yi ranar Juma’a a Abuja.

Ya ce janye izinin na ƙunshe ne cikin wasiƙar da Ministan Abuja, Muhammad Musa Bello, ya aike wa ƙungiyar.

Wasiƙar ta ce an janye izinin ne don shirye-shiryen rantsar da sabuwar gwamnati wanda zai gudana a nan dandalin na Eagle Square ranar 29 ga Mayu.

Sai dai Ugboaja ya bayyana dalilin janye izinin da aka ba su a matsayin rashin jin daɗin taron nasu daga ɓangaren gwamnati da kuma rashin damuwa da makomar rayuwar ma’aikatan Nijeriya.

Ya ce duk da dai janye izinin ba zai yi wani tasiri a kan ma’aikata ba, amma gwamnati ta shirya sauraron bayanin ƙungiyar a Ranar Ma’aikata mai zuwa.

“Sun janye izinin kuma ba su son su yi mana bayani, Ministan FCT ya janye izinin da aka ba mu na yin amfani da Eagle Square don bikin Ranar Ma’aikata.

“Kuma a bayyane yake da yawun gwamnati yake magana, hakan na nufin gwamnati ba ta son yi wa ma’aikata bayani.

“Kenan ba su yaba ƙoƙarin ma’aikatan na shekarun da suka yi wajen yi wa ƙasa hidima, don haka ba za mu ji tsoron yaba wa kanmu,” in ji Sakataren ƙungiyar.