07
Apr
Daga RABI'U SANUSI a Kano Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya ƙaddamar da sabbin motocin sufuri mallakar gwamnatin jihar don inganta harkokin zirga-zirga a jihar da ma ƙasa baki ɗaya. Da yake ƙarin haske yayin duba sabbin motocin, Gwamna Masari ya yaba da ƙoƙarin da hukumar sufuri ta jihar take wajen samar da sabbin motocin ƙirar ‘Hummer’ duk ƙarshen wata. Haka kuma gwamnan ya yi fatan hukumar za ta cigaba da wannan namijin ƙoƙari wajen ganin an sauƙaƙa harkar sufuri a jihar Katsina. Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban hukumar sufuri na jihar Katsina Malam Haruna Musa…
