Labarai

APC ta rushe kwamitocin rumfunan zaɓe a Kebbi

APC ta rushe kwamitocin rumfunan zaɓe a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  A cikin shirye-shiryenta na tinkarar zaɓen gwamnoni mai zuwa, Jam'iyyar APC mai mulki a Kebbi ta rushe kwamitocin rumfunan zaɓe a jihar. Alhaji Isah Aslafi jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyyar ya bayyana wa jaridar Blueprint Manhaja da cewa wannan ya biyo bayan ganin abinda ya faru ne a zaɓen da ya gabata na Shugaban Ƙasa da 'yan majalisun tarayya wanda 'mun lura da yadda zaɓen ya bar mu da mamaki, saboda muna ganin muna da nasara amma sai akasin haka ta faru." Ya ƙara da cewa duk da yake dai sun yaba da ƙoƙarin…
Read More
Rundunar ‘yan sandan Katsina ta halaka ɓarayin daji biyu da karɓe makamansu

Rundunar ‘yan sandan Katsina ta halaka ɓarayin daji biyu da karɓe makamansu

Daga RABIU SANUSI a Kano Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina ta yi nasarar kashe wasu 'yan ta'addan daji guda biyu tare da samun bindiga ƙira AK-47 guda biyu haɗi da sauran wasu kaya daga maharan. Wannan na ɗauke ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Katsina SP Gambo Isah ya fitar wa manema labarai jiya Alhamis. Kamar yadda sanarwar ta bayyana cewa, a ranar 2 ga Maris ɗin wannan shekarar jami'an su  samu bayanai cewa 'yan ta'addan daji sun shiga ƙauyen Yasore dake ƙaramar hukumar Batsari tare da yin harbi kan mai uwa da wabi. Cikin…
Read More
Canjin kuɗi: APC ta buƙaci Emefiele da Malami su yi murabus saboda ɗora Buhari kan bauɗaɗɗiyar hanya

Canjin kuɗi: APC ta buƙaci Emefiele da Malami su yi murabus saboda ɗora Buhari kan bauɗaɗɗiyar hanya

Daga BASHIR ISAH Shugabancin Jam’iyyar APC a shiyyar Arewa maso Yamma, ya buƙaci Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele da Babban Lauyan Ƙasa, Abubakar Malami, da su ajiye aikinsu. APC ta buƙaci hakan ne saboda zargin su biyun da ɗora Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan bauɗaɗɗiyar hanya dangane da sabon tsarin nan taƙaita ta’ammali da tsabar kuɗi, wato “cashless policy”. A ranar Juma’a Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsoffin N200, N500 da N1000 zuwa Disamban 2023 biyo bayan ƙarar da wasu gwamnonin APC uku suka shigar kan Gwamnatin Tarayya. Gwamnonin da lamarin ya shafa…
Read More
Bode George ya yi fatali da nasarar Tinubu, ya ce zai yi ritaya daga siyasa

Bode George ya yi fatali da nasarar Tinubu, ya ce zai yi ritaya daga siyasa

Daga BASHIR ISAH Tsohon gwamnan soji na Jihar Ondo, Bode George, ya bayyana zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisu da ya gudana ranar Asabar da ta gabata a matsayin abin kunya. George ya ce Shugaban INEC ya gaza, bayan da ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin zai gudanar da zaɓe.mai tsabta ta amfani da na’ura, amma a ƙarshe lamari ya sauya. Kazalika, ya ce zai yi ritaya daga harkokin siyasa bayan kammala zaɓen gwamnoni ranar 11 ga Maris. Bode George, wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a shiyyar Kudu maso Yamma, ya bayyana nasarar da Ahmed Tinubu a…
Read More
Ku yi haƙuri game da wahalar da canjin kuɗi ya haifar, kiran Buhari ga ‘yan Nijeriya

Ku yi haƙuri game da wahalar da canjin kuɗi ya haifar, kiran Buhari ga ‘yan Nijeriya

Daga UMAR GARBA a Katsina Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ba wa al'ummar Jihar Katsina haƙuri dangane da mawuyacin halin da 'yan jihar da ma ƙasa baki ɗaya aka shiga sakamakon canjin kuɗi da Babban Bankin Ƙasa (CBN) ya yi. Buhari ya bayyana haka ne ran Laraba cikin wani jawabi da ya yi wa al'ummar jihar a gidansa da ke Daura. "Ina ƙara maku godiya da yarda da kuka yi da ni kuka zaɓe ni har sau biyu a matsayin shugaban ƙasa a jam'iyyar APC. "Ina baku haƙuri kan wahalar da aka sha ta canjin kuɗi an yi ne don…
Read More
Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta gayyaci zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Wakilai

Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta gayyaci zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Wakilai

Daga RABIU SANUSI a Kano Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ƙarƙashin Kwamishinan 'Yan Sanda, CP Muhammad Yakubu, ta gayyaci zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Tarayya Mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Dala, Hon Aliyu Sani Madakin Gini. Wannan bayanin na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar tare kuma da raba wa manema labarai a ranar Laraba. A cikin sanarwar kakakin rundunar 'yan sandan ya ce hukumar ta gayyaci Madakin Ginin ne bisa zargin sa da yin amfanin da bindiga yayin yaƙin neman zaɓensa da ya gudana kwanan baya. Sanarwar ta kara da cewa,…
Read More
NPC ta cafke mai yi mata sojan gona a Kano

NPC ta cafke mai yi mata sojan gona a Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) reshen Jihar Kano ta nesanta kanta da bayanan dake yawo na karɓar 5000 don tabbatar da sunan wanda suka cike aikin ƙidaya na wucin-gadi a jihar. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar a jihar Kano, Hajiya Jamila Abdulkadir, wadda aka raba wa manema labarai. Sanarwar ta ce, bisa bayanan da ta samu ta sa jami'an tsaro bincikar lamarin. Kalika, sanarwa ta ce waɗannan masu karɓar kuɗin da sunan za su tabbatar ma wanda ya cike gurbin aikin wucin-gadi na ƙidaya ba su da alaƙa da su,…
Read More
Kotu ta tsare Alhassan Doguwa a kurkuku

Kotu ta tsare Alhassan Doguwa a kurkuku

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Kotun Majastare a Kano ta tisa ƙeyar Shugaban Masu Rinjaya a Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, zuwa gidan yari kafin lokacin da za a ba da belinsa. Jaridar Solacebase ta rawaito cewa mai kare kansa, Alhassan Doguwa, na fuskantar tuhuma ne kan laifuka da dama da suka haɗa da kisan kai, haɗin baki, mallakar bindiga ba bisa ƙa'ida ba da tada fitina a tsakanin al'umma. Alƙalin kotun, Ibrahim Mansur Yola, shi ne ya ba da umarnin tsare Doguwa a kurkuku zuwa 7 ga Maris inda za a saurari neman belinsa.
Read More
Kai ne mutumin da ya fi dacewa da mulkin Nijeriya – Buhari ya taya Tinubu murnar lashe zaɓe

Kai ne mutumin da ya fi dacewa da mulkin Nijeriya – Buhari ya taya Tinubu murnar lashe zaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taya wanda ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa murna a 2023, ɗan takarar Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce shi ne mutumin da ya fi dacewa da wannan shugabanci. Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman, Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba, 1 ga Maris, 2023. Ya ce; “Ina taya mai girma Bola Ahmed Tinubu murnar nasarar da ya samu. Jama’a ne suka zaɓe shi, shi ne wanda ya fi dacewa da shugabancin. Yanzu zan…
Read More
Zan zama shugaban kowa – Tinubu ya gode wa ‘yan Nijeriya bayan ya doke Atiku da Peter Obi

Zan zama shugaban kowa – Tinubu ya gode wa ‘yan Nijeriya bayan ya doke Atiku da Peter Obi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gode wa ‘yan Nijeriya da suka ba shi jan ragamarsu, ya kuma ba su tabbacin cewa shi ne zai jagoranci kowa da kowa. Tsohon gwamnan na Legas ya yi wannan alƙawarin ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa na karrama shi biyo bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu. Tinubu, wanda shi ne ɗan takarar Jam’iyyar APC a zaɓen na ranar Asabar ya samu ƙuri’u 8,794,726 inda ya doke abokin hamayyarsa kuma ɗan…
Read More