Labarai

Bayan faɗuwar APC zaɓe a Katsina, Masari ya sallami wasu jiga-jigai a gwamnatinsa

Bayan faɗuwar APC zaɓe a Katsina, Masari ya sallami wasu jiga-jigai a gwamnatinsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya amince da dakatar da naɗin kwamishina da sakatarorin dindindin guda biyu da kuma shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta jihar nan take. A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin jihar, Muntari Lawal (SSG) ya fitar, ya ce jami’an da abin ya shafa sun haɗa da Alhaji Tasi’u Dahiru-Dandagoro, kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri. Sauran sun haɗa da Sakatariyar na dindindin, Manufofin ci gaba mai ɗorewa, Hajiya Fatima Ahmed, Sakatariyar dindindin ta Ma’aikatar Noma da Albarkatun Ƙasa, Alhaji Aminu Waziri. Hakazalika, Masari ya sake tabbatar wa Shugaban Hukumar Jin…
Read More
Mutum 3 sun mutu a harin da aka kai ofishin NNPP a Kano

Mutum 3 sun mutu a harin da aka kai ofishin NNPP a Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano Rundunar 'Yan Sandan jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutum biyu yayin da ake tsaka da tattara sakamakon zaɓe a ƙaramar hukumar Tudun Wada dake jihar kano. Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan Kano, CP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya fitar a ranar Lahadi zuwa safiyar Litinin. Sanarwar ta ce an sami bayanai cewa ana cikin tattara sakamakon zaɓen a Tudun Wada ne cikin ofishin hukumar zaɓe na ƙaramar hukumar wasu gungun 'yan dabar siyasa suka kai hari a ofishin kamfen na ɗan takarar majalisar tarayya tare da cinna masa…
Read More
Tinubu ya lashe zaɓen ƙananan hukumomi 6, Atiku ya samu 2 a Katsina

Tinubu ya lashe zaɓen ƙananan hukumomi 6, Atiku ya samu 2 a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya samu nasarar lashe zaɓen ƙananan hukumomi 6 daga cikin 8 da aka tattara kawo yanzu Babban jami'in tattara sakamakon zaɓe a jihar farfesa Mu'azu Abubakar Gusau ne ya sanar da hakan yau lahadi Ƙananan hukumomin da ɗan takarar jam'iyyar APC ɗin ya lashe sun haɗa da Matazu, Kaita, Musawa, Ingawa, Charachi da kuma Dutsi sai dai jam'iyyar PDP ce ta lashe zaɓen ƙaramar hukumar Batsari da kuma Kurfi A babban zaɓen da aka gudanar ranar Asabar. Tinubu ya samu ƙuri’a 82,332 a faɗin…
Read More
INEC ta ɗage tattara sakamakon zaɓen Shugaban Nijeriya zuwa Litinin

INEC ta ɗage tattara sakamakon zaɓen Shugaban Nijeriya zuwa Litinin

Daga SANI AHMAD GIWA Shugaban Hukumar Zaven Nijeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya ɗage zaman tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar zuwa ranar Litinin. Farfesa Mahmood ya bayyana hakan ne bayan gabatar da sakamakon jihar Ekiti a zauren tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da ke Abuja babban birnin ƙasar. Shugaban na INEC ya ce kasancewar jihar Ekitin ce kaɗai ta kai sakamakonta zuwa zauren tattara sakamakon zuwa yanzu, hukumar ta ɗage karvar sakamakon zuwa ranar Litinin da misalin ƙarfe 11:00 na safe.
Read More
Kwankwaso ya lashe zaɓe a ƙaramar hukumar Ganduje

Kwankwaso ya lashe zaɓe a ƙaramar hukumar Ganduje

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Dan takarar Shugaban Ƙasa na jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya lashe zaɓe a Ƙaramar Hukumar Dakin Tofa inda Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya fito. A sakamakon da jami'in INEC na Ƙaramar Hukumar, Adamu Jibril Alhassan ya sanar a hukumar zaɓe ta jihar Kano, ya ce NNPP ta samu ƙuri'a 16,773, yayin da NNPP ta samu 25,072. Kazalika, ya ce PDP ta samu ƙuri'a 2,477 sai kuma jam'iyyar LP da ta tsira da ƙuri'u 202.
Read More
PDP za ta yi na’am da sakamakon zaɓe – Tambuwal

PDP za ta yi na’am da sakamakon zaɓe – Tambuwal

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Babban mai yekuwar neman zaɓen Atiku Abubakar kuma Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya ce Jam'iyyar PDP za ta karɓi sakamakon zaɓe hannu bibbiyu duk yadda ya kasance. Tambuwal ya bayyana hakan ne a mahaifarsa, Tambuwal, jim kaɗa bayan kaɗa ƙuri'arsa. “Mun sani cewa duk yadda lamari ya samu ɗan Adam daga Ubangiji ne, haka shi ma shugabanci Ubangiji kan bayar da shi ga wanda ya so a kuma duk lokacin da Ya so". A cewarsa, "ganin yadda alumma suka fito zaɓe, wata manuniya ce da ke nuni da yadda jama'a suka bai wa sha'nin…
Read More
Atiku zai lashe zaɓen Shugaban Ƙasa, cewar Gwamna Bala

Atiku zai lashe zaɓen Shugaban Ƙasa, cewar Gwamna Bala

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ya bayyana cewar, yana da yaƙin ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar su ta PDP, Atiku Abubakar zai lashe kujerar shugabancin Najeriya. Inji gwamna, "A yanzu dai ba zance komai ba, amma muna jaddada tsammani ɗan takarar mu na shugaban ƙasa, Wazirin Adamawa zai ci zaɓen nan da ikon Allah, da kuma sauran 'yan takarkari na sanatoci da 'yan majalisar tarayya. Sanata Bala Mohammed wanda yayi wannan furuci a mazabar sa ta Bakin Dutse dake garin Yelwan Duguri ta jihar Bauchi, ya kuma nuna gamsuwar sa da yadda na'urar…
Read More
Atiku ya buƙaci jami’an tattara sakamakon zaɓe su dinga shigarwa tun daga rumfuna

Atiku ya buƙaci jami’an tattara sakamakon zaɓe su dinga shigarwa tun daga rumfuna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu da ya umurci jami’an tattara sakamakon zaɓen na ranar Asabar da su dinga shigar da sakamakon zaɓe tun daga rumfunan zaɓe. A cikin sanarwar da mai bai wa Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mista Paul Ibe ya sanya wa hannu, ya ce kiran ya zama wajibi "a binciki wasu gwamnonin da ke ƙoƙarin yin maguɗin zaɓe a matakin ƙananan hukumomi," inji shi
Read More
Zaɓen 2023: An kai wa ma’aikatan EFCC hari a Abuja da Imo

Zaɓen 2023: An kai wa ma’aikatan EFCC hari a Abuja da Imo

Daga AISHA ASAS Wasu tsageru sun kai wa wasu ma'aikatan hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, EFCC, waɗanda ke aikin saka ido a zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisu, hari a kusa da fadar hakimin Bwari da ke birnin tarayya. Lamarin ya biyo bayan kame da aka yi na wanda ake zargi da ƙwarewa wurin siyen ƙuri'un zaɓe a mazaɓar da ke Science Primary School, Bwari. Ma'aikatan na EFCC sun yi nasarar damƙe wanda ake zargi, mai kimanin shekaru 30, kuma a tare da shi akwai jerin sunayen waɗanda aka riga aka…
Read More