Labarai

HOTUNA: Sanata Adamu ya cika shekara 76

HOTUNA: Sanata Adamu ya cika shekara 76

Daga BASHIR ISAH Jiga-jigan 'yan siyasa daga ciki da wajen Jihar Nasarawa na ci gaba da miƙa saƙon taya murna na cika shekara 76 da haihuwa, ga Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu (Turakin Keffi). Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule bai bari an baro shi baya ba wajen taya jigon siyasar murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya bi shi har gidansa da ke Keffi ya miƙa masa katin taya murna.
Read More
Har yanzu Katsina ba ta yafe wa Ado Aliero ba – Masari

Har yanzu Katsina ba ta yafe wa Ado Aliero ba – Masari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya ce har yanzu gwamnatin Katsina ba ta yafe wa Ado Aliero ba, ɗan bindigar da take nema ruwa a jallo duk da naɗin sarautar da aka yi masa a Zamfara. Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ne ya shaida wa BBC cewar sun yi mamakin jin naɗin sarautar da aka yi masa, sai dai ya ce ko da a ce Ado Aliero ya daina ayyukan ta'adanci a Zamfara har yanzu a wajen su bai daina ba. Ya bayyana cewa tun bayan faruwar wannan lamari, ya yi ƙoƙarin tuntuɓar…
Read More
Tausayin maniyyata 700 ne ya sa ƙara’in zuwa Saudiyya bayan Arfa – Shugaban Hukumar Alhazan Kano

Tausayin maniyyata 700 ne ya sa ƙara’in zuwa Saudiyya bayan Arfa – Shugaban Hukumar Alhazan Kano

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano An bayyana cewa tausayi da alhinin maniyyatan Nijeriya 700 da ba su samu zuwa aikin Hajjin bana ba, shi ne ya sa shugabannin Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, kashi 90 cikin 100 na shugabannin ba su je aikin Hajjin bana ba, sakamakon matsalar rashin samun jirgi da Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON ta haddasa aiki a 2022 a cewarsa. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano Farfesa Imam Sale Pakistan kuma, shugaban JIBWIS na Ƙasa reshen jihar Kano a lokacin da yake zantawa da manema…
Read More
2023: INEC za ta gudanar da zave mafi tsafta a Nijeriya – Yakubu

2023: INEC za ta gudanar da zave mafi tsafta a Nijeriya – Yakubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, a ranar Talata, ta yi alƙawarin gudanar da zaɓuka mafi kyawu a Nijeriya a shekarar 2023. Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bada wannan tabbacin a lokacin da ya karvi baƙuncin tawagogin ' International Republican Institute, IRI, da na National Democratic Institute, NDI, a Abuja. Ya ce taron shi ne na farko da INEC ta shirya bayan zaɓen gwamnan jihar Osun da aka yi ranar Asabar, ya kuma bada tabbacin cewa za ta inganta nasarorin da ta samu a zaɓukan da ke tafe.…
Read More
Gwamna Sani Bello ya yaba wa sojoji bisa daƙile harin ‘yan ta’adda a Neja

Gwamna Sani Bello ya yaba wa sojoji bisa daƙile harin ‘yan ta’adda a Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya yaba wa sojoji da sauran jami’an tsaro bisa gaggawar daƙile harin 'yan ta'adda da suka yi yunqurin kai hari kan Sarkin Pawa, hedikwatar ƙaramar hukumar Munya a jihar ranar Litinin. Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, ‘yan ta’addan sun yi yunƙurin kai hari a garin da kuma wani sansanin soji da misalin ƙarfe 2:23 na safe, amma sojoji da sauran jami’an tsaro suka fatattake su. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mary Noel-Berje, ta fitar a Minna, gwamnan ya ce…
Read More
Guguwa ta lalata gidaje da gine-gine 1,300 a Jigawa

Guguwa ta lalata gidaje da gine-gine 1,300 a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Gwamnatin Jigawa ta ce gidaje 1,300 ne guguwar ta lalata a Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa. Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya bayar da rahoton cewa, lamarin da ya faru a ranar Talata da daddare, ya yi varna sosai. Mataimaki na musamman ga Gwamna Muhammad Badaru kan ci gaban al’umma da taimakon jama'a, Hamza Muhammad, ya shaida wa NAN a ranar Asabar cewa, sama da gidaje 1,300 ne ibtila'in guguwar ya afkawa, inda wasu suka rushe gaba ɗaya, wasu kuma suka lalace. Muhammad ya ce guguwar ta kuma lalata wasu sassan babban asibitin yankin…
Read More
Kotu a Kano ta umarci matashi ya biya diyyar Naira miliyan 52 bisa raunata wani

Kotu a Kano ta umarci matashi ya biya diyyar Naira miliyan 52 bisa raunata wani

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A Juma'ar da ta gabata ne dai wata Kotun Shari'ar Muslunci da ke zamanta a unguwar PRP a Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Abubakar Ayuba, ɗan kimanin shekaru 20 da haihuwa da laifin yi wa wani Salisu Usaini mummunan rauni a hannu, har ta kai ga hannun ya ruɓe a ka yanke shi a asibiti. Laifin, a cewar alƙalin kotun, Nura Yusuf Ahmad, ya saɓa wa sashi na 159 na kundin dokar laifuka (Penal Code) ta Jihar Kano. Shi ya sa alƙali Ahmad ya yanke wa mai laifin hukuncin ɗaurin…
Read More
Buhari bai ba wa Ministan Ilimi, Adamu Adamu wa’adin magance yajin aikin ASUU ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Buhari bai ba wa Ministan Ilimi, Adamu Adamu wa’adin magance yajin aikin ASUU ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH Fadar Shugaban Ƙasa ta ce, babu inda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bai wa Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu wa'adin makonni biyu a kan ya magance matsalar yajin aikin Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) da ta ƙi ce, ta ƙi cinyewa. Fadar ta bayyana hakan ne cikin sanarwar da ta fitar ta hannun mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Garba Shehu, a ranar Laraba. A Talatar da ta gabata wasu rahotanni suka ce, bayan da Shugaba Buhari ya saurari hukumomin da ke faɗi-tashin ganin an magance wannan yajin aikin, sai ya bai wa Minista Adamu Adamu wa'adin makonni…
Read More
‘Yan sanda sun damƙe ƙasurgumin mai safarar miyagun ƙwayoyi a Jigawa

‘Yan sanda sun damƙe ƙasurgumin mai safarar miyagun ƙwayoyi a Jigawa

Daga ABUBAKAR M TAHEER a Jigawa Jami'an 'Yan Sandan Jihar Jigawa sun sanar da damƙe ƙasurgumin mai safarar miyagun ƙwayoyi a ƙaramar Hukumar Auyo. A cikin wata sanarwar manema labarai da Jami'an hulɗa da jama'a na hukumar, SDP Shiisu Adam ya sa wa hannu ya bayyana cewa, sun yi nasarar damƙe matashin ne a Garin su na Auyo. Matashin mai Suna Auwal Muhammad Sani mai shekaru 22, ya bayyana cewa yana samun waɗannan muggan ƙwayoyi ne daga wani mai safarar ƙwayoyin mai suna Sule Kulle da ke ƙauyen Adaha. An samu a tattare da shi ƙullin wiwi guda 265, sai…
Read More
Tugun ‘yan baƙin ciki ba zai kashe mini gwiwa ba – Sadiya Umar Farouq

Tugun ‘yan baƙin ciki ba zai kashe mini gwiwa ba – Sadiya Umar Farouq

Daga WAKILINMU Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa duk wani tugu da 'yan baƙin ciki masu son ganin bayan kyawawan shirye-shiryen inganta rayuwa da gwamnatin Buhari ke yi domin cimma burin 'yanto 'yan Nijeriya marasa galihu miliyan 100 daga ƙuncin fatara zuwa shekara ta 2030 ba zai kashe mata ƙarfin gwiwa ba. Ministar ta bayyana haka ne a martanin da ta yi kan wani rahoto da wasu masu kiran kan su 'APC Initiative for Good Governance', wato Ƙungiyar Tabbatar da Nagartaccen Mulki na APC, su ka bayar inda su ka yi iƙirarin…
Read More