Labarai

Da ɗumi-ɗumi: Sanatan APC, Ali Ndume ya yi rashin Mahaifi

Da ɗumi-ɗumi: Sanatan APC, Ali Ndume ya yi rashin Mahaifi

Daga AMINA YUSUF ALI Mahaifin ɗaya daga cikin sanatocin Jam'iyyar APC mai wakiltar gundumar Kudancin Borno a Majalisar Dattawa ta Nijeriya, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya riga mu gidan gaskiya. Wannan sanarwar ta rashin mahaifin sanatan tana ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da Sanatan ya yi ranar Talata, 19 ga watan Yuli, 2022 a Abuja. Ɗan majalisar ya bayyana cewa, za a yi jana'izar mahaifin nasa ne Alhaji Ali Buba Ndume, a ranar Talata a garin Maiduguri babban birnin Jihar Borno. Wani sashen na sanarwar ya yi bayani kamar haka: "Muna masu nadamar sanar da rasuwar Alhaji Ali Buba…
Read More
Mata 1,000 za su samu bashi domin dogaro da kai a Sakkwato

Mata 1,000 za su samu bashi domin dogaro da kai a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato da haɗin gwiwar Bankin Sterling, za su bada bashin ga mata 1,000 masu qananun sana'o'i a Sakkwato da suka fito daga gundumomi, wasu  Masallatan Juma'a 50, da ƙungiyoyin addinin Musulunci 50, tare da sake kira ga jama'ar jihar nan da su duƙufa a cikin ƙanana da matsakaitan sana'o'i domin samun kuɗaɗen lalurar yau da kullun su da iyalansu. Shugaban zantarwar hukumar zakka da waƙafi ta Jihar Sakkwato Malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato ne ya yi wannan kiran yayin da yake buɗe taron wayar da kai a kan…
Read More
Nijeriya na neman diyya kan gurɓataccen abincin da aka ba alhazanta a Saudiyya

Nijeriya na neman diyya kan gurɓataccen abincin da aka ba alhazanta a Saudiyya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON) ta ce, za ta nemi hukumomin ƙasar Saudiyya su dawo mata da kuɗin abincin alhazanta saboda ta ba su gurɓataccen abincin. A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Laraba, ta ce, Shugabanta na ƙasa, Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayyana haka a Muna da ke Saudiyya, lokacin da ya ziyarci tantunan alhazai na jihohi. Ya ƙara da cewa, tuni suka rubuta wasiƙa zuwa ga hukumomin Saudiyya da suka kamata kan yanayin abincin da aka ba alhazan wanda suka yi ta ƙorafi a kan ingancinsa. Rashin abinci…
Read More
Kotun ECOWAS ta bayyana haramta Tiwita a Nijeriya a matsayin karya doka

Kotun ECOWAS ta bayyana haramta Tiwita a Nijeriya a matsayin karya doka

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Kotun Al’ummar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka ta bayyana dakatarwar da gwamnatin tarayya ta yi kan Tuwita a matsayin karya doka. Kotun ta kuma umurci gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da cewa kada ta sake yin hakan. Hakan ya biyo bayan ƙarar da Ƙungiyar Kare Haƙƙin Zamantakewa da Tattalin arziki (SERAP) da ’yan Nijeriya 176 da abin ya shafa suka yi, a cewar Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare. Ministan yaɗa labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya sanar da dakatar da shafin Tuwita a Nijeriya sakamakon goge saƙon da Buhari ya wallafa a shafinsa na…
Read More
Zan cigaba da siyasa ba gudu ba ja da baya – Malagi

Zan cigaba da siyasa ba gudu ba ja da baya – Malagi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, kuma wanda ya fito takarar gwamna a Jihar Neja a zaɓen fidda gwani, don tunkarar babban zaɓen 2023, Alhaji Mohammed Idris Malagi (Kakakin Nupe), ya bayyana muradinsa na cigaba da kasancewa tsundum a cikin siyasa ba tare da gudu ko ja da baya ba. Malagi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke karɓar baƙuncin tawagar shugabannin Ƙungiyar 'Yan Jaridu ta Ƙasa (NUJ) reshen Jihar Neja, a wata ziyarar godiya da suka kai masa a gidansa da ke Minna, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar Kwamared Abu Nmodu. A cewarsa,…
Read More
An fara gudanar da ƙididdigar gidaje a Kano

An fara gudanar da ƙididdigar gidaje a Kano

Daga BABANGIDA A. GORA a Kano Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa reshen Jihar Kano ta fara gudanar da ƙidayar gwaji, wato ƙidayar gidaje a wasu ƙananan hukumomi daga shiyyoyi ukku dake Jihar Kano. Idan dai ana biye da mu za a iya tunawa cewa a makon da ya gabata ne hukumar qidaya ta ƙasa ta bada umarnin fara gudanar da wannan aikin na ƙidaya a faɗin ƙasar da aka ɗauki tsawon lokaci ba a gudanar ba. Kamar yadda hukumar ta bada umarnin shelantawa kwanan baya cewa kowace jiha za a gudanar da wannan aikin ƙidaya ta tun daga matakin gidaje ya…
Read More
Yadda Nijeriya ta ciyo bashin Naira tiriliyan 225 cikin shekara 20

Yadda Nijeriya ta ciyo bashin Naira tiriliyan 225 cikin shekara 20

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Nijeriya ta ci bashibn Naira tiriliyan 225.93 a cikin shekaru 20 da suka gabata, wanda ya kusa ninka Naira tiriliyan 114.46 da qasar ta samu na kuɗaɗen shiga a tsawon lokacin. Alƙaluman da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar sun nuna Gwamnatin Tarayya da jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774 ne suka ciyo basukan daga shekarar 2001 zuwa 2022. Masana sun bayyana yawan basukan a mastayin babban abin damuwa, ganin da yadda tattalin arzikin Nijeriya ya fi dogaro a kan ɗanyen mai. Ƙididdigar yawan basukan Naira 225.9 a tsawon shekara 20 da CBN ta fitar a…
Read More
Gwamnatin Ganduje ta haramta hawa adaidaita sahu bayan ƙarfe 10 na dare

Gwamnatin Ganduje ta haramta hawa adaidaita sahu bayan ƙarfe 10 na dare

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta haramta yin amfani da baburan masu ƙafa uku da aka fi sani da adaidata sahu bayan ƙarfe 10:00 na dare. Hakan na cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar a ranar Litinin. Sanarwar ta ce, gwamnatin ta ɗauki matakin ne domin magance matsalar tsaro da jihar ke fama da ita. Muhammad Garba, ta cikin sanarwar ya kuma bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis ɗin makon nan. Kazalika, sanarwar ta buƙaci masu tuƙa baburan na…
Read More
Kwalejin Nazarin Kiwon Lafiya ta Keffi ta soma jarrabawar neman gurbin karatu

Kwalejin Nazarin Kiwon Lafiya ta Keffi ta soma jarrabawar neman gurbin karatu

Daga BASHIR ISAH A ranar Alhamis, 14 ga Yulin 2022, Kwalejin Nazarin Kimiyya da Fasahar Kiwon Lafiya ta Jihar Nasarawa da ke Keffi, ta kaddamar da jarrabawar neman gurbin karatu na shekarar 2022/2023 domin bai wa masu sha'awar shiga kwalejin damar da suke buƙata. Dalibai maza da mata daga ciki da wajen Jihar Nasarawa ne suka haɗu a harabar kwalejin da ke babbar hanyar Keffi zuwa Abuja don rubuta jarrabawar. Jarrabawar wadda za a shafe kwana tara ana gudanar da ita, an tsara gudanar da ita ne ta hanyar amfani da kwamfuta kai tsaye, kamar yadda kodinetan shirin, Mista Emmanuel…
Read More
Za a sallamo Osinbajo daga asibiti bayan an yi masa tiyata cikin nasara

Za a sallamo Osinbajo daga asibiti bayan an yi masa tiyata cikin nasara

Daga AMINA YUSUF ALI An yi wa mataimaakin Shugaban ƙasar Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo tiyata cikin nasara. Kuma ana sa ran za a sallame shi nan da kwanaki kaɗan bayan ya ƙara jin ƙwarin jikinsa. A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne dai aka yi wa Osinbajo tiyata a cinyarsa wanda tawagar ƙwararrun likitoci suka gudanar a wani asibiti dake yankin Ikejan Jahar Legas. Mai taimaka wa Mataimakin Shugaban ƙasar a fanni yaɗa labarai, Laolu Akande, shi ya ba da wannan bayani a jawabin manema wanda aka wallafa a ranar Asabar. A cikin jawabin, Akande ya bayyana cewa, wasu…
Read More