Labarai

Mu da gwamnati muke amfana da matsalar tsaro – Ƙasurgumin ɗan fashin daji

Mu da gwamnati muke amfana da matsalar tsaro – Ƙasurgumin ɗan fashin daji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai satar mutane a Jihar Zamfara ya ce matsalar rashin tsaro na ƙara ta'azzara ne a Arewacin ƙasar saboda an mayar da lamarin na neman kuɗi. Abu Sani wanda shi ne ya jagoranci sace 'yan matan sakandaren gwamnati ta garin Jengeɓe a bara, ya faɗi hakan ne a wani shiri na musamman na binciken ƙwaƙwaf da BBC ta gudanar kan ayyukan 'yan bindigar. "An mayar da abin neman kuɗi a wannan ɓangare, kowa kuɗi yake nema, shi ya sa harkoki suke lalacewa, tun daga manyan har zuwa ga ƙananan," inji…
Read More
Hanifa: Kotu ta yanke wa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa ta hanyar rataya

Hanifa: Kotu ta yanke wa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa ta hanyar rataya

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Kano karkashin jagorancin Alkali Usman Na’abba, ta yan ke wa wanda ya kitsa sacewa da kashe Hanifa Abubakar 'yar shekara biyar a Kano, Abdulmalik Tanko, hukuncin kisa ta hanyar rataya. A ranar Alhamis kotun ta yanke wannan hukunci, inda ta ce dole Tanko ya bakunci lahira bayan kama shi da laifin kisa. Tanko shi ne mai makarantar Nobel Kids Academy inda nan marigayiya Hanifa ke tafiya kafin cimma ajalinta. Idan dai za a iya tunawa, a ranar 4 ga Disamban 2021 aka yi garkuwa da Hanifa a kan hanyarta ta komawa gida daga Islamiyya, inda…
Read More
Ya auri jikarsa kuma ya ƙi rabuwa da ita

Ya auri jikarsa kuma ya ƙi rabuwa da ita

Wani magidanci mai suna Alhaji Musa Tsafe mai shekaru 47, ya dage kan ƙin sakin jikarsa wadda ya aura shekaru 20 da suka gabata. Mutumin wanda ke zaune a Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara tare da iyalinsa, ya ce, ba zai sawwaƙe wa jikar tasa ba duk da an ankarar da shi a kan haramcin igiyar auren da aka ƙulla a tsakaninsa da ita. Bayanai sun ce, matar mai suna Wasila Isah Tsafe mai kimanin shekaru 35, wadda jika ce ga babban yayan Alhaji Musa, ta haifa masa ’ya’ya takwas a tsawon shekaru 20 na aurensu. Sai dai wannan…
Read More
Likitoci sun gano kuɗaɗe da ƙusoshi a cikin wani mutum

Likitoci sun gano kuɗaɗe da ƙusoshi a cikin wani mutum

Likitoci sun shiga mamaki bayan sun gano ɗaruruwan tsabar kuɗi da ƙusoshi da batura da guntattakin gilasai bayan da wani mutum mai suna Burhan Demir daga garin Ipekyolu na ƙasar Turkiyya ya kai ƙaninsa asibiti saboda kukan ciwon ciki. A lokacin da likitocin suka yi gwajin hoton cikin mutumin ta amfani da 'Endoscopic' tare da ɗaukar hoton cikin da na’urar d-ray sun yi mamaki bayan gano abubuwa 233 a cikin mara lafiyar mai shekara 35. Abubuwan sun haɗa da tsabar ƙarafan kuɗin ƙasar Lira guda ɗaya da batura da mayen ƙarfe da ƙusoshi da gilasai da duwatsu. Daga baya likitocin…
Read More
Barazanar hari: Gwamnati ta rufe Kwalejin Kwali a Abuja

Barazanar hari: Gwamnati ta rufe Kwalejin Kwali a Abuja

Daga BASHIR ISAH Biyo bayan barazanar mahara a yankin babban birnin tarayya, Abuja, ya sa Gwamnatin Tarayya ɗaukar matakin rufe Kwalejin Tarayya (FGC) da ke Kwali a ranar Litinin don kauce wa jefa rayuwar ɗalibai da malamai cikin haɗari. Gwamnati ta bada sanarwar rufe makarantar ne bayan da ta samu rahoton jami'an tsaro sun daƙile wani shirin kai harin da aka yi zargin 'yan bindiga sun yi a yankin Bwari. Wannan na zuwa ne kwanaki 21 bayan mummunan harin da 'yan bindigar da ake kyautata zaton ISWAP ne suka kai gidan yarin Kuje a Abuja. Lamarin da ya yi sanadiyar…
Read More
Rundunar ‘yan sandan Kano ta bajekolin mutane 198 masu laifi daban-daban

Rundunar ‘yan sandan Kano ta bajekolin mutane 198 masu laifi daban-daban

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta yi nasarar yin awon gaba da masu laifuffuka daban-daban a faɗin jihar cikin watanni uku don samar da zaman lafiya da kare rayukan al'umma da dukiyoyinsu. Tabbatar da hakan na zuwa ne sa'ilin da rundunar take gabatar wa da manema labarai masu laifuffukan a hedikwatarta da ke Bampai a ranar Alhamis da ta gabata ƙarƙashin jagorancin Maigirma Kwamishinan 'Yan Sanda da ake wa laƙabi da 'Nagari Na Kowa', CP Sama'ila Shu'aibu Dikko. A jawabinsa lokacin da yake gabatar da masu laifuffukan, kwamishinan ya yaba wa jami'an rundunar da…
Read More
‘Yan sanda sun damƙe wakilin Leadership a Zamfara

‘Yan sanda sun damƙe wakilin Leadership a Zamfara

Daga WAKILINMU A ranar Asabar da ta gabata Rundunar 'Yan Sandan Jihar Zamfara ta damƙe tare da tsare wakilin Jaridar Leadership na jihar, Malam Umaru Maradun a kan dalilin da ba a bayyana ba. Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mista Ayuba Elkanah, ya tabbatar da faruwar hakan ga Shugaban Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Nijeriya, Reshen Jihar Zamfara, Ibrahim Maizare, yayin zantawar da suka yi kan batun ta waya. Elkanah ya ce zai dubi lamarin kafin ɗaukar mataki na gaba. 'Yan sanda sun kama Maradun ne a gidansa da ke yankin Ƙaramar Hukumar Maradun wanda nan ne mahaifar Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle.…
Read More
Yajin aiki: NUEE ta shirya mara wa ASUU baya

Yajin aiki: NUEE ta shirya mara wa ASUU baya

Dag BASHIR ISAH Ƙungiyar Ma'aikatan Lantarki ta Ƙasa (NUEE) ta umarci mambobinta da su shirya su shiga babbar zanga-zangar ƙungiyar ƙwadago NLC da ASUU suka shirya gudanarwa a ranar 26 ga Yuli, 2022. NUEE ta ba da wannan umarni ne ta cikin wasiƙar goyon bayan da ta aika wa NLC da ASUU mai ɗauke da kwanan wata 22 ga Yuli da kuma sa hannun sakataren ƙungiyar na ƙasa, Joe Ajaero. A cikin wasiƙar tata, ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin nuna goyon bayanta ga ASUU wajen taya ta yaƙin neman cimma bauƙatunta a wajen Gwamnatin Tarayya don a…
Read More
2023: Zaɓen Shettima a matsayin mataimakin Tinubu daidai ne – NPCF

2023: Zaɓen Shettima a matsayin mataimakin Tinubu daidai ne – NPCF

Daga BASHIR ISAH An bayyana cewa farar dabara ce zaɓen da Bola Tinubu ya yi wa Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a babban zaɓen 2023. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da shugaban ƙungiyar kansiloli na ƙasa (NPCF), Honarabul Muslihu Yusuf Ali, mai wakiltar gundumar Gurungawa, Kumbotso, Jihar Kano ya fitar a ranar Asabar. Ali ya ce, nasarar da Tinubu ya samu na zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa na APC na 2023, abu ne da babu makawa. Ya ce dukkanin 'yan takarar sauran jam'iyyu babu wanda zai iya karawa da Tinubu saboda ya…
Read More
Ganduje ya bai wa ɗan Kano tallafin karatu miliyan N3

Ganduje ya bai wa ɗan Kano tallafin karatu miliyan N3

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Kano, Umaru Abdullahi Ganduje, ya bada tallafin karatu na kuɗi Naira miliyan N3 ga wani matashin jihar, Suyudi Sani, saboda bajintar da ya nuna a jarrabawar neman shiga jami'a da hukumar JAMB ta saba shiryawa inda ya zama ɗalibin da ya fi kowa samun maki bayan da ya samu maki 303. Gwamnatin Kano ta miƙa wa matashin cekin kuɗin ne ta hannun Kwamishinar Manyan Makarantun Jihar, Dakta Mariya Mahmud Bunkure, kuma tuni ya samu gurbin karatu a Jami'ar Bayero da ke Kano (BUK), inji Kwamishinar. Mariya ta ƙara da cewa, Suyudi ya nuna bajinta a…
Read More