Labarai

Saƙon Sabuwar Shekarar Hijira: Adamu ya buƙaci ‘yan Nijeriya su mallaki katin zaɓe

Saƙon Sabuwar Shekarar Hijira: Adamu ya buƙaci ‘yan Nijeriya su mallaki katin zaɓe

Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi kira ga 'yan Nijeriya, musamman waɗanda suka kai shekarun zaɓe da su tabbatar da sun yi rijistar katin zaɓe don su yi amfani da shi a zaɓe mai zuwa da sauransu. Sanata Adamu ya yi wannan kira ne a wani saƙon manema labarai da ya fitar ta hannu mai taimaka masa kan sha'anin sabbin kafofin yaɗa labarai, Muhammad Nata'ala Keffi, a ranar Asabar don taya al'ummar Musulmi shiga sabuwar shekarar Musulunci, 1444. Adamu ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga Muslimin Nijeriya da su yi…
Read More
Za a gabatar da Neymar gaban kotu kan zargin zamba da cin hanci

Za a gabatar da Neymar gaban kotu kan zargin zamba da cin hanci

Daga Mahdi M. Muhammad Shekaru tara kenan da Neymar ya kammala komawa Barcelona daga ƙungiyar Santos ta Brazil. An yi la'akari da shi a matsayin matashin ɗan wasan ƙwallon ƙafa mafi kyau a duniya a lokacin, sanya hannunsa ya gamu da farin ciki da yawa kuma Selecao bai yi ƙasa a gwiwa ba. Ana zargin ɗan awallon tawagar Brazil, wanda yanzu ke taka leda a Paris St Germain da aikata zamba da cin hanci. An daɗe ana ci gaba da shari’ar kuma a watan Oktoba ne za a fara sauraren ƙarar a kotun Barcelona. El Pais ya yi ƙarin haske…
Read More

HOTO: Ganduje ya kai ziyarar duba aiki

Yayin da Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, tare da Mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da tawagarsu suka kai ziyarar duba aikin titi mai tsawon kilomita hamsin wanda ya tashi daga Ƙaramar Hukumar Kumbotso ya wuce ta ƙananan hukumomi biyar har zuwa Ƙaraye
Read More
Gwamnatin Kano ta gano ma’ajiyar gurɓataccen taki da ake sayar wa manoma

Gwamnatin Kano ta gano ma’ajiyar gurɓataccen taki da ake sayar wa manoma

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ta bankaɗo wata ma’ajiya da aka ajiye gurɓataccen taki a Gunduwawa da ke Ƙaramar Hukumar Gabasawa. Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin mai Saye, CPC, Baffa Babba Ɗan’agundi ne ya bayyana hakan ta bakin mai magana da yawun hukumar, Musbahu Yakasai a ranar Laraba a Kano. “Mun samu bayanan sirri cewa akwai wani mamallakin ma’ajiyar taki yana haɗa takin da yashi, sannan ya siyarwa manoma. “Hakan ya sa muka ɗauki matakin rufe ma’ajiyar, domin kare al-ummar Jihar Kano daga amfani da taki maras kyau,” inji shi. Yakasai ya kuma ƙara da cewa a…
Read More
Harin jirgin ƙasa: Gwamnatin Buhari ta ci amanar talakawan Nijeriya – PDP

Harin jirgin ƙasa: Gwamnatin Buhari ta ci amanar talakawan Nijeriya – PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari mai mulki ta ci amanar 'yan Nijeriya a tsawon mulkinta a ƙasar nan. Kakakin jam’iyyar Debo Ologunagba ya bayyana cewa, ”irin mulkin kama-karyar da APC take yi a ƙasar nan da kuma nuna halin ko-in-kula da take yi kan kiyaye rayukan mutanen ƙasar ya nuna gazawar gwamnatin. ”Ku duba yadda 'yan bindiga suke cin karensu ba babbaka a ƙasar nan. Duk wanda ya ga yadda 'yan bindiga ke jibgar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba sannan kuma gwamnati ta zuba musu ido,…
Read More
Kashi biyu cikin ɗari ne na ‘yan gudun hijira miliyan 3.2 aka yi rajistarsu, cewar gwamnati

Kashi biyu cikin ɗari ne na ‘yan gudun hijira miliyan 3.2 aka yi rajistarsu, cewar gwamnati

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Dubu tamanin da huɗu, da ɗari takwas da uku kacal, misalin kashi biyu cikin ɗari na miliyan uku da dubu ɗari biyu na ‘yan gudun hijira dake jibge a sassa daban-daban na ƙasar nan aka yi wa rajista ko hukuma ta san da zamansu, a cewar gwamnatin tarayya. Jihar Borno ita ce akan gaba da take da tarin ‘yan gudun hijira da suka kai kimani miliyan ɗaya da dubu ɗari shida, yayin da jihar Ekiti ke biye da ita da ‘yan gudin hijira dubu biyar da ɗari uku da saba’in da bakwai. Waɗannan bayanai sun…
Read More
Badaƙalar Biliyan N109: Kotu ta bada belin Akanta-Janar, Ahmed Idris

Badaƙalar Biliyan N109: Kotu ta bada belin Akanta-Janar, Ahmed Idris

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Abuja mai zamanta a yankin Maitama, ta bada belin dakataccen Akanta-Janar na Ƙasa, Ahmed Idris. Idan za a iya tunawa, a ranar Juma'a kotu ta bada umarnin a garƙame Akanta-Janar ɗin tare da sauran waɗanda suke kare kansu a gidan yarin Kuje kafin sauraren buƙatar belin da suka shigar. A ranar 16 ga Mayun 2022 jami'an Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC) suka damƙe Idris bisa alaƙarsa da wawushe biliyan N80. Bayan 'yan kwanaki da kama shi ne sai Ministar Kuɗi da Tsare-tsaren Ƙasa, Zainab Ahmed, ta dakatar…
Read More
An garƙame tsohon Akanta-Janar na Nijeriya, Ahmed Idris kan badaƙalar Naira biliyan 109

An garƙame tsohon Akanta-Janar na Nijeriya, Ahmed Idris kan badaƙalar Naira biliyan 109

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi An bayar da umarni a garƙame tsohon Akanta-Janar na Nijeriya, Ahmed Idris da wasu mutane biyu a gidan gyaran hali na Kuje dake Abuja, akan ha’inci ko zamba cikin aminci na zunzurutun kuɗaɗe na Naira biliyan 109. Babbar Kotu dake ƙarƙashin jagorancin Alƙali J.O. Adeyemi-Ajayi ita ce ta bayar da umarnin garƙame waɗannan mutane guda uku a ranar Juma’a da ta gabata lokacin da aka gurfanar da su bisa zargin yin zamba da halasta kuɗaɗen haram da ake tuhumar tsohon ma’ajin tarayyar ta Nijeriya. Alƙalin ya bayar da umarnin a garƙame su a kurkuku har…
Read More
Ba zan taɓa sassautawa wajen murƙushe ‘yan ta’adda ba – Buhari

Ba zan taɓa sassautawa wajen murƙushe ‘yan ta’adda ba – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ƙara nanata aniyar gwamnatinsa na kawo ƙarshen matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta, yana mai cewa ko kaɗan bai zai raga wa 'yan bindiga da 'yan ta'addan da ke kai hare-hare a faɗin ƙasar. A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Lahadi, ya ce manyan hafsoshin tsaron ƙasar na iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an kawo ƙarshen matsalar 'yan bindiga a ƙasar. Ya kuma jajenta wa tsohon shugaban Jam'iyyar PDP, Adamu Muazu, saboda kashe ɗan uwansa da 'yan…
Read More
Farfesa Isah Ali Pantami Al-huda-hudan ilimi ne – Farfesa Rasheed

Farfesa Isah Ali Pantami Al-huda-hudan ilimi ne – Farfesa Rasheed

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe An bayyana Ministan Sadarwan Zamani da Tattalin Arziki na Nijeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin Al-huda-hudan ilimi a wannan zamanin. Babban sakatare a hukumar kula da jami’o’in Nijeriya (NUC), Farfesa Abubakar Rasheed, ya bayyana hakan ne a wajen wani taro na Mataimakan Shugabannin jami’o’in Gwamnati na Nijeriya (VC Retreat) da aka gudanar, inda ya jinjina wa Farfesa Pantami a kan irin baiwarsa ta ilimi da yake da ita. Ya ƙara da cewa, Isa Ali gangaran ne a ɓangaren ilimin addini da na zamani wanda haziƙancinsa ya sa aka bayyana shi da Al-huda-huda,…
Read More