Harin jirgin ƙasa: Gwamnatin Buhari ta ci amanar talakawan Nijeriya – PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari mai mulki ta ci amanar ‘yan Nijeriya a tsawon mulkinta a ƙasar nan.

Kakakin jam’iyyar Debo Ologunagba ya bayyana cewa, ”irin mulkin kama-karyar da APC take yi a ƙasar nan da kuma nuna halin ko-in-kula da take yi kan kiyaye rayukan mutanen ƙasar ya nuna gazawar gwamnatin.

”Ku duba yadda ‘yan bindiga suke cin karensu ba babbaka a ƙasar nan. Duk wanda ya ga yadda ‘yan bindiga ke jibgar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba sannan kuma gwamnati ta zuba musu ido, ina talaka zai saka kansa?.

”Ƙarƙashin wannan mulki na APC, kisa ya zama kusan jiki ga mutane. Gaba ɗaya jam’iyyar ta ruguza tsarin zaman lafiya a ƙasar wanda talakawa suka saba da ita. Abu kamar wasa, ƙiriƙiri abu ya zama ruwan dare ta ko’ina kisa kawai ake yi sannan babu wani abu da gwamnati ke iya yi.

”Daga 2020 zuwa yanzu ‘yan bindiga sun kashe mutum sama da 18,000. Kuma wai a ce akwai gwamnati a ƙasar nan. Komai ya daburce, talaka ya afka cikin ruɗani, babu inda zai saka kansa amma kuma kullum sai kurin gwamnati ta kusa gamawa da su, amma jiya iyau.”

A ranar Litinin ‘yan bindiga sun saki ƙarin wasu fasinjoji 3 daga cikin fasinjojin da ‘yan bindiga suka sace a layin jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna.