Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Jihar Kano ta bankaɗo wata ma’ajiya da aka ajiye gurɓataccen taki a Gunduwawa da ke Ƙaramar Hukumar Gabasawa.
Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin mai Saye, CPC, Baffa Babba Ɗan’agundi ne ya bayyana hakan ta bakin mai magana da yawun hukumar, Musbahu Yakasai a ranar Laraba a Kano.
“Mun samu bayanan sirri cewa akwai wani mamallakin ma’ajiyar taki yana haɗa takin da yashi, sannan ya siyarwa manoma.
“Hakan ya sa muka ɗauki matakin rufe ma’ajiyar, domin kare al-ummar Jihar Kano daga amfani da taki maras kyau,” inji shi.
Yakasai ya kuma ƙara da cewa a baya ma hukumar tasu ta kama wata mota a cike da garin semovita mara kyau a kasuwar Singa, inda ya ƙara da cewa hukumar ta ƙara kama wata ma’ajiyar takin mara kyau a Ƙaramar Hukumar Garko.
Ya kuma nemi al’umma da su cigaba da bai wa hukumar bayanan irin waɗannan gurare domin kare lafiya da ma rayukan al’umma.