02
Nov
Daga BASHIR ISAH Kimanin ɗaliban makarantar sakandare su sama da talatin ne suka tsinci kansu cikin wani mummunan yanayi bayan da wata mota ƙirar Siena ta saki hanya ta afaka musu a bakin titi a dai lokacin da suke ƙoƙarin komawa gida bayan tashi daga makaranta. Wannan ibtila'in ya faru ne a jiya Litinin a Tudun Wada da ke yankin Uke cikin ƙaramar hukumar Karu, jihar Nasarawa da misalin ƙarfe biyu na rana. Bayanan shaidu sun ce, lamarin ya auku ne sakamakon ƙwacewar da motar da lamarin ya shafa ta yi wa direbanta, inda nan take ta afka wa ɗaliban…
