Labarai

Da Ɗumi-ɗuminsa: An ceto ma’aikatan Jami’ar Abuja

Da Ɗumi-ɗuminsa: An ceto ma’aikatan Jami’ar Abuja

Daga BASHIR ISAH Rundunar 'yan sandan birnin tarayya Abuja, ta tabbatar da cewa rundunar tsaron haɗin gwiwa sun ceto dukkan ma'aikatan Jami'ar Abuja da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Litinin da ta gabata. Mai magana da yawun 'yan sandan yankin, Josephine Adeh, ita ce ta bada wannan tabbaci cikin sanarwar da ta fitar a yau Juma'a. Haka nan, Adeh ta ce tuni an sadar da waɗanda lamarin ya shafa da iyalansu.
Read More
‘Yan bindiga sun sace tsohon babban Manajan NPA a Kano

‘Yan bindiga sun sace tsohon babban Manajan NPA a Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano Wasu gungun 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun sace tsohon Janar manajan hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya NPA Bashir M. Abdullahi. Rahotanni sun ce, ɓata garin sun sace shi ne a wata gonarsa da ke garin Sitti da ke yankin ƙaramar hukumar Sumaila da yammacin ranar Laraba da ta gabata, To sai dai kuma rahotanni sun ruwaito cewa, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, ba ta samu rahoton sace shi ba, Wasu mazauna garin da lamarin ya faru ne dai suka shaida wa manema labarai faruwar…
Read More
Ruftawar bene: Mutane 10 sun rasa rayukansu a Legas

Ruftawar bene: Mutane 10 sun rasa rayukansu a Legas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Aƙalla mutane 10 ne aka ruwaito sun mutu a ranar Litinin bayan da wani gini mai hawa 21 ya ruguje a hanyar Gerard a unguwar Ikoyi da ke Jihar Legas. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, mutane da dama sun maƙale a cikin baraguzan ginin, ciki har da Manajan Darakta na Fourscore Heights Limited, Femi Osibona, wanda shi ne mai maginin, da wasu abokan aikinsa da injiniyoyi. Ɗaya daga cikin ma’aikatan da suka tsallake rijiya da baya, Gabriel Bassey, ya shaida wa manema labarai cewa, har yanzu kimanin mutane 50 ne ke maƙale a cikin ɓaraguzan…
Read More
Kotun Ƙoli ta yi magana kan mamaye gidan Mai Shari’a Odili

Kotun Ƙoli ta yi magana kan mamaye gidan Mai Shari’a Odili

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja A ranar Talata ne kotun ƙolin ƙasar nan ta bayyana mamaye gidan mai shari’a Mary Odili da cewa ba a hukunta shi ba. A martaninta na farko kan wannan mummunar lamarin, kotun ƙolin, a wata sanarwa da kakakinta, Akande Festus, ya fitar, ta ce harin rashin wayewa ne, kuma abin kunya ne na farautar wani jami’in shari’a da ba shi da laifi. Kotun ta yi gargaɗin cewa bai kamata wani mutum ko ma’aikatun gwamnati su yi wa ɓangaren shari’a mummunar fahimta a matsayin yaron da ake yi wa bulala a cikin hannun gwamnati uku…
Read More
An cafke mamallakin benen da ya ruguje a Legas saboda saɓa ƙa’ida

An cafke mamallakin benen da ya ruguje a Legas saboda saɓa ƙa’ida

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Manajan Hukumar Kula da Tsarin Gine-gine a Jihar Legas (LASBCA), Gbolahan Oki ya ce mamallakin benen nan wanda ya ruguje mai hawa 21 da ake ginawa a Ikoyi, an ba shi izinin gina hawa 15 ne kawai. Oki ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ta wayar salula cewa hukuma ta cafke mai gidan, kuma zai fuskanci shari'a saboda rayukan mutane da suka salwanta a dalilin iftila'in. "Ya samu izinin gina bene mai hawa 15, amma sai ya ƙara yadda yake so. Yanzu haka ina a wajen, hatta kayan aikin da…
Read More
Mun kama waɗanda suka kai samame gidan Mai Shari’a Mary Odili – Sufeto Janar

Mun kama waɗanda suka kai samame gidan Mai Shari’a Mary Odili – Sufeto Janar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An kama mutanen da suka kai samame gidan Mai Shari'a Mary Odili ta Kotun Ƙoli da ke Abuja, kamar yadda Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Usman Alkali Baba ya bayyana. Alkali ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da Mataimakin Sufeton 'Yan Sandan shiyya ta biyu a wajen taron sanin makamar aiki da aka shirya wa jami'an tsaro a Legas da kuma Ogun, wanda ya gudana a Victoria Island cikin birnin Legas. Bayan irin kiraye-kirayen da jama'a ke ta yi akan wannan badaqala, ranar Litinin Babban Sufeto Janar na 'Yan sandan Nijeriya ya…
Read More
‘Yan jarida 62 aka kashe a 2020 – UNESCO

‘Yan jarida 62 aka kashe a 2020 – UNESCO

Daga AISHA ASAS Aƙalla 'yan jarida 62 ne suka rasa rayukansu ta sanadiyyar aikin nasu. Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO ta tabbatar da hakan. Hukumar ta ce a tsakanin shekara ta 2006 zuwa 2020, sama da mutum 1,200 na ƙwararrun 'yan jarida sun rasa rayukansu ta sanadiyyar neman labarai. Sai dai abin takaici kaso tara cikin goma na waɗanda wannan iftila'in ya faɗa wa ba a hukunta makasan su ba. A shekara ta 2021, alƙaluma sun tabbatar da yawaitar kisan gillar da ake yi wa 'yan jarida ba tare da haƙƙinsu ba, hakan yasa aka…
Read More
Wahalar rayuwa ta sa wata mata jefa ‘ya’yanta cikin rijiya

Wahalar rayuwa ta sa wata mata jefa ‘ya’yanta cikin rijiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata mata a da ke zaune a yankin Ibuaje, Osogbo, Babban Birnin Jihar Osun ta tsunduma 'ya'yanta mata guda biyu cikin rijiya. Mazauna yankin da matar take sun ce dama matar ta sha yin ƙorafi akan yadda take ɗanɗana wahalhalun rayuwa da kuma ɗawainiya da waɗannan 'ya'ya. Wani mazaunin unguwar da yake bayyana yadda abun ya faru, ya ce "Matar ta fara jefa babbar yarinyar ne mai kimanin shekara bakwai da haihuwa cikin rijiyar, sai kuma daga bisani ta jefa ƙaramar 'yar kimanin shekara biyar, da misalin ƙarfe biyu na rana." Ko a lokacin…
Read More