Labarai

Sojoji sun kama wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne a wani masallacin Kano

Sojoji sun kama wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne a wani masallacin Kano

Daga UMAR M. GOMBE Sojojin Nijeriya sun kai samame a wani masallaci da ake zargin na 'yan Boko Haram ne da ke Hotoro a Kano, inda suka cafke wasu mutum 10. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna an yi kamen ne da yammacin Asabar da ta gabata. Haka nan cewa sojojin sun aiwatar da aikinsu ne cikin ƙwarewa ba tare da ɗaga hankali kowa ba da ke yankin. Rahotanni sun suna wasu da suka yiwo gudun hijira daga Barno zuwa Kano a dalilin rikicin Boko Haram ne suka kafa masallacin. Ya zuwa haɗa wannan labari, da aka nemi jin…
Read More
Ƙungiyar Arewa ta yi takaicin milyoyin Naira da aka biya wajen kuɓutar da ɗaliban Kaduna

Ƙungiyar Arewa ta yi takaicin milyoyin Naira da aka biya wajen kuɓutar da ɗaliban Kaduna

Daga AISHA ASAS Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta bayyana damuwarta dangane da yadda akan biya kuɗaɗen fansa wajen kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su a hannun 'yan bindiga. Ƙungiyar ta bayyana damuwarta ne a wani bayanin da Sakatarenta na Hulɗa da Jama'a na Ƙasa, Emmanuel Yawe, ya fitar Asabar da ta gabata a Kaduna. ACF ta yi amfani da wannan dama wajen jinjina wa duka waɗanda suka sadaukar da ransu wajen tattaunawa da 'yan fashin dajin domin kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su, musamman ma ɗaliban Jami'ar Greenfield, Kaduna. Ta ce “Mun gode wa Allah…
Read More
Majalisar Dattawa za ta gana da hafsoshin tsaro kan sha’anin tsaron ƙasa

Majalisar Dattawa za ta gana da hafsoshin tsaro kan sha’anin tsaron ƙasa

Daga AISHA ASAS A ranar Alhamis ake sa ran Majalisar Dattawa ta karɓi baƙuncin manyan hafsoshin tsaron ƙasa da sauran hukumomin tsaro inda za a tattauna kan batun da ya shafi matsalolin tsaron ƙasa. Manhaja ta fahimci cewa buƙatar gayyatar jami'an ta taso ne duba da yadda sha'anin tsaron ƙasa ke ƙara daburcewa. Tun farko, Majalisar ta so ganawa da Shugaban Rundunar Sojoji da Babban Sufeton 'Yan Sanda da kuma Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri (NIA), a Talatar da ta gabata amma sai hakan bai yiwu ba sakamakon taron majalisar tsaro ta ƙasa ta gudanar. A bisa wannan dalili ne…
Read More
Malamai sun tsunduma yajin aiki a Neja

Malamai sun tsunduma yajin aiki a Neja

Daga UMAR M. GOMBE Malaman makarantun gwamnati a jihar Neja sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a wannan Laraba. Cikin wata takardar sanarwa wadda Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa (NUT) reshen jihar ta fitar cikin daren da ya gabata, NUT ta ce malaman firamare da na sakandare na gwamnati a jihar, sun soma yajin aikin ne saboda gazawa da gwamnatin jihar ta yi wajen biya wa malamai buƙatunsu kamar yadda aka yi yarjejeniya a baya. NUT ta ce kafin kai wa ga ɗaukar wannan mataki sai da ta tattauna da Shugaban Ma'aikata na jihar da manyan sakatarori a ranar…
Read More
An sako ɗaya daga cikin ɗaliban jami’ar da aka yi garkuwa da su a Kaduna

An sako ɗaya daga cikin ɗaliban jami’ar da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Daga AISHA ASAS 'Yan bindiga sun sako ɗaya daga cikin ɗaliban jami'ar Greenfield da suka yi garkuwa da su kwanan nan a Kaduna. Kodayake dai babu wani bayani a hukumance da ya tabbatar da hakan, amma mahaifiyar ɗalibin da ya kuɓutan, Lauritta Attahiru ta tabbatar wa manema labarai kan cewa ɗanta ya dawo gida. Sai dai Lauritta ba ta yi cikakken bayani ba dangane da yadda aka yi ɗan nata ya dawo gida ba, sai da aka biya fansa ko kuwa a'a. Wata majiya ta faɗa cewa a ranar Asabar da ta gabata aka sako ɗalibin bayan kuma mahaifiyarsa ta…
Read More
Za a soma cin tarar N100,000 kan masu kada bishiyoyi ba da izinin gwamnati ba a Abuja

Za a soma cin tarar N100,000 kan masu kada bishiyoyi ba da izinin gwamnati ba a Abuja

Daga FATUHU MUSTAPHA Hukumar Abuja ta ce haramun me ga mazauna birnin su kada bishiyoyin cikin gidajensu da na wuraren da jama'a ke haɗuwa suna shakatawa ba tare da izinin gwamnati ba. Hukumar ta yi gargaɗin duk wanda ta kama da laifin take wannan doka, tarar N100,000 lakadan ta hau kansa. Darakta a Hukumar, Hajiya Riskatu Abdulazeez ce ta bayyana hakan a Abuja a ƙarshen mako. A cewarta, da zarar bishiyoyin da aka daddasa a gidaje suka girma, shi kenan sun zama mallakar gwmamnati wanda dole sai da izinin gwamnatin kafin a sare ko a kada su. Ta ce ɗaukar…
Read More
‘Yan bindiga sun hallaka kwamishina a Kogi

‘Yan bindiga sun hallaka kwamishina a Kogi

Daga AISHA ASAS 'Yan bindiga a jihar Kogi, sun kashe Kwamishinan Fansho na jihar, Solomon Adebayo, a kan babbar hanyar Kabba zuwa Ilori da ke jihar. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna lamarin ya auku ne cikin daren Asabar da ta gabata sa'ilin da Marigayin ke kan hanyarsa ta zuwa yankin Kabba daga Ilori. Majiyar Manhaja ta ce 'yan bindigar sun buɗe wa motar kwamishinan wuta ne wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa nan take, tare da raunata direbansa. Tuni dai rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin. Da yake magana a kan batun, mai magana da…
Read More
Buhari ya taya Mohammed Idris murnar cika shekara 55 da haihuwa

Buhari ya taya Mohammed Idris murnar cika shekara 55 da haihuwa

Daga BASHIR ISAH A yau ne fitaccen nan a harkar yaɗa labarai, wato Alhaji Mohammed Idris, ya cika shekara 55 da haihuwa. Tuni dai dangi, 'yan'uwa da abokan arziki suka shiga zazzaga wa jigon fatan alheri dangane da zagayowar wannan rana mai muhimmanci a rayuwar Kakakin Nupe. Shi ma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bai bari an baro shi baya ba, domin kuwa ya aike da saƙonsa na taya murna ga Babban Sakataren Ƙungiyar Masu Jaridu na Nijeriya (NPAN), Alhaji Mohammed Idris, bisa cikarsa shekara 55 da haihuwa. A cewar Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa, Garba Shehu, "Shugaba Buhari ya…
Read More
Ma’aikata a kama sana’a, cewar Gwamna Matawalle

Ma’aikata a kama sana’a, cewar Gwamna Matawalle

Daga AISHA ASAS Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi kira ga ma'aikatan gwamnatin jihar cewa baya ga albashi da suke karɓa duk wata, akwai buƙatar su duba su haɗa da sana'a domin samun ƙarin kuɗaden shiga saboda a cewarsa, gwamnati ba ta da halin biyan  sabon mafi ƙarancin albashi. Gwamnan ya ce a halin da ake ciki, gwamnati na fama da biyan basussukan da ta gada daga gwamnatin da ta gabace ta na biyan albashi da gudanar da harkokin gwamnati. Matawalle ya bayyana hakan ne a Juma'ar da ta gabata sa'ilin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Ƙungiyar Ƙwadago (NLC)…
Read More