07
Aug
Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Bichi daga Jihar Kano, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar, ya ƙaddamar da buɗe tashar wutar lantarki da ake kira Farno-farno a ƙaramar hukumar. A sanarwar da Jami'ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, ta ce ya bayyana shekaru huɗu da suka wuce suke ta fafutukar yadda za a samar da tsayayyiyar wutarlantarkin a garuruwan mazaɓun yamma a garin Bichin, duba da ƙaruwar yawan jama'ar mazaɓun a halin yanzu, da hakan ya janyo matsalar rashin samun wuta yadda yakamata a yankunan. Mazaɓun da suka haɗa da; Ɗanzabuwa, Ƙyalli, Ƙauƙau da kuma…
