07
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya yaba wa Hukumar Ba Da Lamunin Karatu ga ɗalibai ta Nijeriya (NELFUND), ya ce hukumar tana faɗaɗa damar samun ilimi mai zurfi. Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi Shugaban hukumar ta NELFUND, Mista Jim Oɓia, tare da Manajan Darakta/Babban Jami’in Gudanarwa na NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr, a Abuja ranar Talata. A yayin ganawar, Tinubu ya yaba wa NELFUND bisa gagarumin cigaban da ta samu wajen faɗaɗa damar samun ilimi mai zurfi ta hanyar nasarar aiwatar da Shirin Ba da Lamunin Karatu ga ɗalibai. Haka kuma, Shugaban…
