Babban Labari

Na goyi bayan sayar da NNPC, inji El-Rufai

Na goyi bayan sayar da NNPC, inji El-Rufai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce, Gwamnatin Nijeriya ta gaza a ɓangaren mai da iskar gas, don haka ya kamata ta janye kanta daga fannin. El-Rufai ya ce, babu amfani gwamnati ta ci gaba da harkar mai, tunda duk abin da yi a ɓangaren, ciki har da cefanar da NNPC, haƙa ba ta cimma ruwa ba. “Harafin L da aka ƙara a sunan NNPC babu abin da ya sauya; har yanzu kuɗaɗenmu suke ci, suna cewa, an samu riba, amma ba mu ga ko sisi ba. “NNPC babbar matsala ce a Nijeriya, wadda dole mu…
Read More
Sallamar Kanu aka yi ba wanke shi ba – Malami

Sallamar Kanu aka yi ba wanke shi ba – Malami

Ofishin Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari'a, ya ce sake Nnamdi Kanu da aka yi ba wanke shi aka yi ba an sallame shi ne kawai. Ofishin ya yi wannan ƙarin hasken ne don kawar da sahakku a tsakanin 'yan ƙasa kan hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ɗauka dangane da shari'ar Nnamdi Kanu. Hadimin Ministan Shari'a, Dakta Umar Jibrilu Gwandu ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ran Alhamis. Ya ce, jama'a su sani sallama kawai kotun ta yi wa Kanu amma ba wanke shi ba, domin kuwa shari'a ba ta ƙare ba. Kazalika, ofishin ya ce…
Read More
Kotu ta saki shugaban ’yan ta’adda, Nnamdi Kanu

Kotu ta saki shugaban ’yan ta’adda, Nnamdi Kanu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kotun ɗaukaka Ƙara ta Tarayyar Nijeriya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin sakin shugaban ƙungiyar nan ta a ’yan ta’adda, wato IPOB, Nnamdi Kanu, ƙungiyar da a baya wata kotu ta tava ayyana a matsayin ta ’yan ta’adda. A ranar Alhamis Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta wanke Nnamdi Kanu daga laifin da Gwamantin Nijeriya ke zargin sa aikatawa na tayar da zauna tsaye da ta’addanci da kuma jagorantar haramtacciyar ƙungiya. Lauyansa, Ifeanyi Ejiofor, ya sanar ta shafinsa na Facebook cewa, “Mun yi nasara, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta wanke ta kuma saki Nnamdi Kani.” A…
Read More
Ambaliyar Lokoja ta zama barazana ga Abuja

Ambaliyar Lokoja ta zama barazana ga Abuja

*Gwamnati ta ɗora alhakin ƙarancin mai a Babban Birnin Tarayya kan ambaliyar*Ta gargaɗi matafiya masu bin hanyar Abuja zuwa Lokoja Daga SANI AHMAD GIWA da MAHDI M. MUHAMMAD Wata gagarumar ambaliyar ruwa da aka yi kuma ake hasashen cigaba da yi a ’yan kwanakin nan a garin Lokoja da ke kan hanyar zuwa Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, daga yankin kudancin ƙasar, ta yi sanadiyyar haifar da gagarumar barazana ga mazauna Babban Birnin Ƙasar ta fuskar walwalar rayuwarsu, domin ba ɓarkar kawai da ambaliyar ta yi a Lokoja ce kaɗai ta shafi al’ummar ƙasar ba, har ma da matafiya da…
Read More
2023: Rundunar ’Yan Sanda ta ja kunnen dogarin matar Atiku bisa riƙe mata jaka

2023: Rundunar ’Yan Sanda ta ja kunnen dogarin matar Atiku bisa riƙe mata jaka

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta ja kunnen wata ’yar sanda da har yanzu ba a bayyana sunanta ba, saboda riƙe jakar Titi, matar ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP a Babban Zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ’yar sandar da ta kasance dogari ga matar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar. Matar Atiku Titi, a ranar Laraba, 5 ga Oktoba, 2022, ta gabatar da wani shiri da ya mayar da hankali kan mata a Abuja kuma mijin nata ya raba hotuna daga taron, wanda ya nuna ta a tsaye da ’yar sanda tana riƙe da jaka a bayanta. Kafofin…
Read More
2023: Abacha ya yi ɓatan dabo a jerin ’yan takarar gwamnan Kano

2023: Abacha ya yi ɓatan dabo a jerin ’yan takarar gwamnan Kano

Daga AMINA YUSUF ALI Sunan Muhammad Abacha ya yi vatan dabo a cikin jerin sunayen 'yan takarar Gwamnan Kano a 2023 da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC) ta saki a ranar Talatar da ta gabata.  Haka zalika, sunan ɗan takarar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin jami'yyar LP, Bashir Ishaq Bashir shi ma ya yi layar zana a dai jadawalin na INEC. Amma sai aka maye gurbin sunansa da sunan wani Abdullahi Mohammed Raji. Shi kuma Assadiq Wali, sunansa shi ne ya fito a matsayin ɗan takarar na PDP a jihar Kano. Wannan ya sanya 'yan jam'iyya cikin…
Read More
2023: Bakin alƙalami ya bushe kan batun sauya ’yan takara, inji INEC

2023: Bakin alƙalami ya bushe kan batun sauya ’yan takara, inji INEC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta ce, ba za ta amince da janyewa ko sauya sheƙa ba bayan fitar da jerin sunayen ’yan takarar da za su tsaya takara a zaven 2023. Sai dai hukumar ta ce, za a iya yin maye gurbin ne kawai idan mutum ya mutu kamar yadda sashi na 34(1) na dokar zaɓe ya tanada ko kuma bisa umarnin kotun da ta dace. Gargaɗin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zace Barista Festus Okoye…
Read More
2023: An rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

2023: An rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

…Yayin da aka ɗage takunkumin yaƙin neman zaɓe…Na rungumi ƙaddara kan takarar sanata, cewar Ahmad Lawan Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kamar yadda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da tsare-tsarenta ga masu neman kujerun siyasa daban-daban a babban zaɓen shejarar 2023 mai ƙaratowa, inda ta fitar da ranar Larabar nan da ta gabata 28 ga Satumba, 2023 a matsayin ranar da kowane ɗan takara zai nuna farin jininsa ga al'umma, ma'ana an yarje wa kowane ɗan takara ya fita yaƙin neman zaɓe a jam'iyyu 18 da Hukumar INEC ɗin ta yi wa rajista. Sai…
Read More
Ziyarar musamman: Yadda masha’a ta ragu a garin Tafa

Ziyarar musamman: Yadda masha’a ta ragu a garin Tafa

*Yanzu gidan karuwai kashi 30 ne a garin*Mu biyar muka fara kafa garin, inji Goran Tafa*Ashe ’yan asalin Kano suka kafa garin*Gwamna El-Rufai ya yi watsi da mu, cewar mazaunan Tafa Daga MOHAMMED ALI a Tafa Garin Tafa yana cikin Ƙaramar Hukumar Kagarko da ke Jihar Kaduna ne, inda ya ke da nisan kilomita 161 daga Garin Kaduna akan hanyar zuwa Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, wanda kuma kilomita 41 ne tsakaninsa da Abuja ɗin. Tafa ya yi shuhura da fice, musamman saboda kasancewarsa wani wajen yada zango ga direbobi masu lodin manyan motoci ƙurar Tirela. Sai dai kuma a…
Read More