Babban Labari

Rodger Federer ya yi ritaya daga wasan Tennis

Rodger Federer ya yi ritaya daga wasan Tennis

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Fitaccen ɗan wasan tennis ɗan ƙasar Switzerland, Roger Federer ya sanar da yin ritaya daga fagen wasan Tennis bayan da ya lashe kofuna sama da 103, da manyan wasanni 20 a cikin shekaru ashirin da huɗu na ganiyarsa a wasan ƙwallon Tennis. Federer ya fitar da sanarwa a shafinsa na Tiwuta, "wasan cin kofin Laver da za a yi a mako mai zuwa a Landan zai zama taron ATP na ƙarshe". Ɗan wasan mai shekaru 41, wanda ya lashe kofunan Grand Slam 20 bai taka leda ba tun bayan da ya yi rashin nasara a wasan…
Read More
A shirye muke mu janye yajin aiki – ASUU

A shirye muke mu janye yajin aiki – ASUU

…Amma idan an cimma matsaya, inji shugabanta*Ya ce, shigar da ƙungiyar ƙara ba mafita ba ce*Za mu cigaba da shiga tsakani don kawo ƙarshe, cewar wata ƙungiya Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sama da watanni bakwai kenan Ƙungiyar Malaman Jami'o'i a Nijeriya (ASUU) na cigaba da yajin aiki akan wasu buƙatu da suke neman gwamnati ta cika. Duk da zaman tattaunawa da ƙungiyar ta riƙa yi da Gwamnatin Tarayya akai-akai don sasantawa, amma ba a cimma wata matsaya ba, lamarin da ya haifar da kowanne vangare na zargin juna da nuna son zuciya, inda a gefe guda kuma ɗalibai…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Kotu ta soke zaɓen fidda gwanin PDP na Gwamnan Zamfara

Da ɗumi-ɗumi: Kotu ta soke zaɓen fidda gwanin PDP na Gwamnan Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, ta soke zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP na takarar gwamna a zaɓen 2023 mai zuwa. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Aminu Baffa ya yanke hukuncin ne ranar Juma'a yayin da kotu ta yanke hukunci kan ƙarar. “Bisa hukuncin da kotun ta yanke mai shafi 109 kotun ta gamsu da ƙarar da Injiniya Ibrahim Shehu Gusau ya shigar a gabanta a kan PDP, Adamu Maina Waziri, Kanar Bala Mande, Dauda Lawal Dare da INEC kan rashin bin ƙa’ida a zaɓen gwamnan PDP da aka kammala…
Read More
2023: Baya ta haihu a rikicin PDP

2023: Baya ta haihu a rikicin PDP

*Wike ya cigaba da yi wa Atiku turjiya…Duk da murabus ɗin Jibril daga shugabancin Kwamitin Amintattun jam’iyya*Ina nan kan bakana sai Ayu ma ya tafi – Wike*Jam'iyyar ta naɗa Adolphus Wabara sabon Shugaban Kwamitin Amintattu*Ruɗani ya taso bayan Gwamna Makinde ya maye gurbin Tambuwal a shugabancin Ƙungiyar Gwamnonin PDP*Har yanzu Tambuwal ne shugaban ƙungiyar, cewar jam’iyyar*An naɗa Tambuwal jagorancin yaƙin neman zaɓen Atiku Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alhamis da ta gabata Shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibril ya yi murabus daga muƙaminsa. Sanata Walid Jibril ya sauka daga kujerar tasa ce a ranar Alhamis, a daidai lokacin…
Read More
Ranar Hausa Ta Duniya: Shin ko kwalliya ta biya kuɗin sabulu?

Ranar Hausa Ta Duniya: Shin ko kwalliya ta biya kuɗin sabulu?

*Yadda aka gudanar da bikin a Kaduna Daga SANI AHMAD GIWA a Kaduna Kasancewar bunƙasar harshen Hausa, wanda an yi ƙiyasin yana da masu amfani da shi kimanin mutane miliyan 50 a duniya, hakan ya sa ba tare da wani jeka-ka-dawo ba, Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ware duk ranar 26 ga Agusta a matsayin Ranar Hausa Ta Duniya. Wannan dalili ne ya sa Taskar Nasaba tare da haɗin gwiwar Amale Hausa24, Ƙungiyar Matasan 'Yan Jarida ta Jihar Kaduna da kuma sauran kafafen yaɗa labarai suka shirya wannan gagarumin taro a Kaduna, garin gwamna. Wani sashe na mahalarta taro…
Read More
Jami’ar Maryam Abacha ta karrama Atiku, ta sanya wa wata tsangaya sunansa

Jami’ar Maryam Abacha ta karrama Atiku, ta sanya wa wata tsangaya sunansa

Daga AMINU AMANAWA A yayin wani taro mai cike da tarihi, Jam'iar Maryam Abacha American University ta Najeriya ta karrama ɗan takarar shugabancin Najeriya na Jam'iyyar PDP a zaɓen baɗi, Atiku Abubakar, inda ta sanya wa wata tsangaya sunansa. Ginin tsangayar mai suna Atiku Abubakar, yana ɗauke da kwalejin nazarin kimiyyar zamantakewa da sha'anin Mulki, Atikun ne da kansa ya ƙaddamar da shi. A taron ƙaddamarwar da ya sami halartar manyan mutane a Kano, wanda ya kafa jam'ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya jinjina wa Wazirin Adamawa, inda ya bayyana shi da wata maɓuɓɓugar ilimi da ƙarfafa gwiwa ga matasan…
Read More
Halin ha’ula’i da makarantar Turaki da ke cikin birnin Sakkwato ke ciki

Halin ha’ula’i da makarantar Turaki da ke cikin birnin Sakkwato ke ciki

…Mun bada umarnin kawo ƙarshen matsalar cikin gaggawa, cewar Shugaban SUBEB Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Makarantar ta Turaki dai na ɗaya daga cikin makarantun firamari a Sakkwato dake da daɗaɗɗen tarihi kasantuwar bayanai sun nunar da cewa an kafata ne tun a lokacin mulkin gwamnan soji na wancan lokacin Gado Nasko kimanin shekaru 40 da suka gabata. Duk da daɗaɗɗen tarihin da makarantar firamarin ke da halin rashin magudanun ruwa dake damun makarantar ke fuskanta na cigaba da zama wani babban ƙalubale ga muhallin karatu ga ɗaliban makarantar dake karatu a ciki. Manhaja ta samu damar kai ziyara a…
Read More
Kotu ta hana Buhari da NBC rufe kafafen yaɗa labarai 53

Kotu ta hana Buhari da NBC rufe kafafen yaɗa labarai 53

Daga BASHIR ISAH A ranar Litinin wata Babbar Kotu mai zamanta a Legas, ta hana Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC) ƙwace lasisi da rufe wasu kafafen yaɗa labarai 53 a faɗin ƙasa saboda rashin sabunta lasisinsu. Wata sanarwar haɗin gwiwa mai ɗauke da sa hannun Sakatare-Janar na Ƙungiyar Editoci ta Nijeriya (NGE) Iyobosa Uwugiaren da Mataimakin Darakta na SERAP, Kola Oluwadare, ta nuna Alƙalin kotun, Akintayo Aluko ya ba da umarnin hana rufe kafafen ne bayan da ya saurari ƙorafin NGE da SERAP suka shigar kotun. A makon da ya…
Read More
Taron Blueprint ya yi armashi

Taron Blueprint ya yi armashi

*Janar Dambazau ya nemi a tsaurara matakan yaƙi da  ta'addanci Daga AMINA YUSUF ALI Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Nijeriya, Laftana Janar Abdulrahman Bello Dambazau (mai ritaya), ya yi kira da a yi garambawul a sashen tsaron ƙasar nan domin magance ƙalubalen tsaro da suke fuskantar ƙasar nan.  Dambazau ya qara da cewa, dole ne a yi nazari na gaggawa a kan salon yaƙi da ta'addancin da muke da shi a Nijeriya, musamman ma saboda yawaitar samun ɓata-gari masu shigowa daga wajen Nijeriya, abinda a cewar sa ya jefa rayuwar 'yan Nijeriya a cikin tasku. Tsohon ministan ya yi…
Read More
Abubuwan da za su taimaka wajen inganta zaɓen 2023 – Dambazau

Abubuwan da za su taimaka wajen inganta zaɓen 2023 – Dambazau

Daga BASHIR ISAH An bayyana cewa, tsarin karɓa-karɓa zai taka rawa gaya wajen inganta zaɓuɓɓukan 2023. Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Laftanar-Janar Abdulrahman Dambazau ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen Taron Lacca na 2021 da kamfanin Blueprint ya shirya ranar Talata Abuja. Kazalika, Dambazau ya ce sake fasalin ƙasa gami da sha'anin addini na daga cikin abubuwan da idan aka riƙe su za su yi tasiri mai ma'ana ga babban zaɓen na 2023. Ya ƙara da cewa, tun bayan samun 'yancin kai, Nijeriyar ta gudanar da manyan zaɓuɓɓuka guda shida, wanda idan Allah Ya so…
Read More