02
Apr
*Zaluncin 'yan kasuwa ne ya durƙusar da marubutan mu - Fatima DAGA AISHA ASAS Fatima Garba Ɗanborno ba za a kira ta ɓoyayya ba musamman a wajen ma'abota karance-karancen littafan Hausa, domin ta yi fice wajen fitar da littattafai masu tarin faɗakarwa gami da ilimintarwa da kuma nuni cikin nishaɗi. Shi ya sa a wannan makon Jaridar Manhaja ta zagaya don zaƙulo wa masu karatu ita don jin wace ce ita? Me ya kai ta ga fara rubutu da shiga harkokin marubuta tsundum? Tare kuma da jin irin nasarori da faɗi-tashin da ta yi kafin ta zama cikakkiyar marubuciya? Duk…
