16
Aug
Daga BASHIR ISAH Ya zuwa ranar 22 ga Agusta ake sa ran rufe shiga gasar rubutun ƙagaggen labari ta mata mai taken 'Hikayata' ta 2021 wadda sashen Hausa na BBC ya saba shiryawa duk shekara. Sanarwar da BBC ta fitar ta nuna an ƙirƙiro gasar ƙagaggen gajeren labarin ce a 2016 don ƙarfafa wa mata wajen bayarwa da kuma yaɗa labarun da suka shafe su. Sanarwar ta ce akan bai wa mata damar aiko da ayyukansu na ƙagaggun labarai da suka rubutu cikin harshen Hausa masu yawan kalmomi tsakanin 1000 zuwa 1500. Bayan kammala tattara ayyukan da aka shigar a…
