23
Apr
Waka saƙa ta ake yi kamar tabarmar kaba, shi kuma zube gina shi ake kamar yadda ake gida - Khalid Daga AISHA ASAS Shahararre kuma sanannen marubuci da ake alfahari da shi a duniyar Adabin Hausa Khalid Imam, ya samu damar amsa gayyatar jaridar Manhaja inda masu karatu za su ji cikaken tarihi tare da nasarorin da ya samu a duniyar rubutu. An dai ce waƙa a bakin mai ita za ta fi zaƙi, ku biyo mu don jin wane ne Khalid Imam: Masu karatu za su so jin tarihin ka.Suna na Khalid lmam. An haife ni a shekarar 1973…
