Adabi

Abinda ya sa muka kafa Kwalejin Marubutan Hausa – Kabiru Yusuf Fagge

Abinda ya sa muka kafa Kwalejin Marubutan Hausa – Kabiru Yusuf Fagge

"Rubutu a kafafen sadarwa na zamani cigaba ne" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Duniyar marubutan adabi ba za ta taɓa mantawa da sunan Malam Kabiru Yusuf Fagge ba, wanda aka fi sani da ANKA, da irin gudunmawar da ya bayar kuma har yanzu yake kan bayarwa a harkar rubutun adabi, kama daga rubutun zube, wasan kwaikwayo har zuwa rubutun littattafan ýan makaranta, don bunƙasa ilimin yara manyan gobe. Marubuci, mawallafi, malamin makaranta, kuma ɗan kasuwa. Wakilin Manhaja Abba Abubakar Yakubu ya yi kaciɓis da shi a Kano, bayan yayen ɗalibai zangon farko na Kwalejin Marubutan Hausa da aka gudanar, bayan kammala…
Read More
Sharhin littafin ‘Duhun Damina’ na Maryamerh Abdul

Sharhin littafin ‘Duhun Damina’ na Maryamerh Abdul

Daga BAMAI ALHAJI DABUWA Sunan Marubuciya: Maryamerh AbdulShekarar Bugu: Babu.ISBN: 978-978-982-968-4.Mai Sharhi: Bamai Dabuwa.Lambar Waya: 07037852514. Gabatarwa/Abubuwan Burgewa:Littafin 'Duhun Damina' littafi ne da a ka yi amfani da wani irin salo mai kama da tafiyar kura. Shi ne littafin da ya kawo zunzurutun kuɗi sama da miliyan guda a ranar da a ka ƙaddamar da shi. Littafin ya taɓo wata matsala da kusan kowa ke tsoron taɓawa saboda gudun tambayar kai ta ya aka yi ka sani? Wasu kuma hankalinsu bai kai wajen ba, musamman iyaye, amma kuma rayuwar 'ya'yansu ce dumu-dumu a ciki. Littafi ne da kowanne uba/uwa ya…
Read More
Na rubuta littafin abinda ya faru da ni bayan fitowarsa – Zuwaira Kolo

Na rubuta littafin abinda ya faru da ni bayan fitowarsa – Zuwaira Kolo

"Har yau akwai waɗanda ba sa iya karatun littafi a waya" Daga AISHA ASAS Ɗaya daga cikin marubutan da suka jima su na ciyar da adabin Kano gaba ce Blueprint Manhaja ta ɗauko mu ku a wannan mako. Zuwaira Dauda Kolo marubuciya ce da ta jima ta na ƙawata zukatan makaranta da daɗaɗan littafai, masu fadakarwa gami da nishaɗantarwa kai har ma da ilimintarwa. A tattaunawarta da Wakiliyar Blueprint Manhaja, Aisha ASAS, mai karatu zai ji irin tata gwagwarmayar a duniyar rubutu. Ga yadda tattaunawar ta kasance: MANHAJA: Mu fara da jin taƙaitaccen tarihinki.ZUWAIRA KOLO: Da farko sunana Zuwaira Dauda…
Read More
Yadda Ƙungiyar Marubutan Katsina ta gabatar da taron bita

Yadda Ƙungiyar Marubutan Katsina ta gabatar da taron bita

Daga USMAN ANGO a Katsina Ƙungiyar Marubutan Jihar Katsina da ta ke a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammad Bello Sambo ta sake gabatar da taron zaman karatu (reading sesson) karo na biyu. Taron dai ya zo da sabon salo na ba wa marubuta da mawaƙa dama su gabatar da ayyukansu gaban 'yan uwansu marubuta, yayin da za a yi mu su gyara da kuma jinjina. Taron, wanda a ka gabatar a ranar Asabar, ya samu halartar wasu daga cikin jiga-jigan ƙungiyar, kamar su; Muhammad Bello Sambo (Shugaba)Fatima S. Muhammad ( Ma'aji), Usman Ango (PRO), Abubakar Ƴar'aAdua (Baba Abu), A'isha Mobile, Lu'ubatu…
Read More
Har yau ban cimma nasarar da na ke fatan samu a rubutu ba – Auntyn KD

Har yau ban cimma nasarar da na ke fatan samu a rubutu ba – Auntyn KD

"ƙungiyoyin marubuta na taka rawa kan dawo da martabar rubutu" Ɗaya daga cikin iyaye kuma gatan littafan adabin Kano, Sadiya Muhammad Abdullahi, wadda aka fi sani da Auntyn Kd, ta kasance jajirtacciyar marubuciya da ke kishin rubutun Hausa, hakan ta sa ta zare damtse wurin ganin ba a bar harkar ta su ta rubutu a baya ba, ta hanyar kafa ƙungiyoyi, zuwa taruka da kuma shiga hanyar fafutukar neman mafita ga marubuta. Shafin adabi na wannan sati, ya lalubo wa masu karatu ita, don haka idan kun shirya, ku biyo mu, don jin yadda tattaunawar ta kasance: Daga AISHA ASAS…
Read More
Soyayya ce sanadiyyar fara rubutuna- MD Asnanic

Soyayya ce sanadiyyar fara rubutuna- MD Asnanic

"Marubuci mutum ne mai keɓaɓɓiyar ƙwaƙwalwa" Daga AISHA ASA Sanannen abu ne, Arewacin Nijeriya kewaye ta ke da albarkatun ƙasa da ko su kaɗai mu ka doga da su, za su iya cin ƙarfin buƙatunmu. Duk da wannan ni'ima da aka ba mu, Allah ya mana daɗɗi da baiwar ƙirƙira, musamman a tsakanin matasanmu. Muhammad Iliyass, wanda aka fi sani da MD Asnanic, matashi ne da ƙwaƙwalwarsa ke zagaya tsakanin ɓangarorin rubutu, kai har ma da na rera waƙa. A taƙaice, matashi ne mai ƙwaƙwalwar mutane da yawa. A wannan makon, shafin adabi na jaridarku mai farin jini, Manhaja, ta…
Read More
Ban ɗauki rubutu a matsayin sana’a ba – Muhammad Bala Garba

Ban ɗauki rubutu a matsayin sana’a ba – Muhammad Bala Garba

"Yawaitar marubutan yanar gizo ne ya kashe kasuwar littatafai" Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Filin Adabi a wannan mako ya yi babban ka mu, inda ya samu damar hira da haziƙin marubuci da ya ƙware a harkar rubutu ta fannoni daban-daban, masu bibiyarmu yau mun karɓi baƙuncin Muhammad Bala Garba Maiduguri. A hirarsa da Wakilin Blueprint Manhaja, Ibrahinm Hamisu, za ku ji yadda ya faro rubutu tun daga makarantar sakandire. Ku biyo mu, don jin yadda tattaunawar ta kasance: MANHAJA: Za mu so ka gabatar da tarihinka ga masu karatunmu?MUHAMMED BALA: Bismillahir Rahamanir Rahim. Dukkan godiya ta tabbata ga Sarki…
Read More
Sharhin littafin ‘Da Ma Sun Faɗa Mini’

Sharhin littafin ‘Da Ma Sun Faɗa Mini’

Daga BAMAI DABUWA KKM Sunan Littafi: Da Ma Sun Faɗa Mini.Marubuci: Jibrin Adamu Jibrin Rano.ISBN: Babu.Shekarar Bugu: 2020.Yawan Shafi: 200.Mai Sharhi: Bamai Dabuwa Kkm. Gabatarwa/Tsokaci.Babu buƙatar fayyacewa ko bayyana haɗuwa da ƙwarewar wannan littafin ko na marubucin. Don haka ne ma za mu faɗa a taƙaice, wanda na tabbatar ya wadatar: 'Da Ma Sun Faɗa Min', shi ne labarin da ya lashe kambu a gasar Gusau Institute ta shekarar 2020. 'Da Ma Sun Faɗa Min', labarin wasu ma'aurata ne guda biyu (Zainab da Aliyu). Wanda wani marubuci (Jibril) ya samar a dalilin zaman majalisa daga abokinsa Bashir ɗan Kimiyya. Cukurkuɗaɗɗen…
Read More
Jami’ar Bayero ta ƙaddamar da ƙamus ɗin Hausa zuwa Ingilishi a Kano

Jami’ar Bayero ta ƙaddamar da ƙamus ɗin Hausa zuwa Ingilishi a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  A ranar Asabar da ta gata an ƙaddamar da sabon qamus ɗin harshen Hausa zuwa Ingilishi da ya gudana a Jami’ar Bayero ta Kano. Littafin dai yana ɗauke da shafi 627, wanda Bature kuma masani a ɓangaren harsuna da ke Jihar Indiana ta Amurka, Paul Newman da mai ɗakinsa, Roxana Ma Newman suka wallafa, kuma maɗaba’ar Jami'ar Bayero ta buga shi. Newman dai ya tava zama a  Kano ne tun a  shekarar 1972, inda ya  zama Darakta na farko a Cibiyar Koyar da Harsunan Nijeriya a BUK, lokacin tana Kwalejin Abdullahi Bayero. Da ya ke…
Read More
Rashin ƙa’idojin rubutu na jirkita saƙon marubuci – Ibrahim Nayaya

Rashin ƙa’idojin rubutu na jirkita saƙon marubuci – Ibrahim Nayaya

“Akwai tasirin ƙa'idojin rubutu a litattafan Hausa” Daga AISHA ASAS Ɗaya daga cikin dalilan da masana su ka ce ya ciyar da rubutun Hausa ko a ce rubutun 'Adabin Kasuwar Kano' baya shine, kurakuren da su ka yawaita a cikin littattafan. A na ɗora alhakin wannan kan su marubutan litattafan, saboda kasancewar su ne masu wuƙa da nama a lamarin. Duk da haka, su kansu masanan na da na su kaso a wannan matsala, duba da cewa, da yawa daga cikin marubutan ba masu sani ne a kan Hausa ba. Ko da yake idan aka yi duba da ƙarancin sani kan…
Read More